Wasu 'yan Najeriya sun soma yin caca a kan ranar da shugaban kasar Muhammadu Buhari, wanda ya shafe kusan wata uku yana jinya a birnin London, zai koma kasar.
Muhammad Buhari.
Wani shafin intanet da ke yin caca, NaijaBet.com, na tambayar mutanen da ke da sha'awar cacar su canki ranar da shugaban kasar, wanda ya fice daga Najeriya ranar bakwai ga watan Mayu, zai koma gida.
A watan Yunin shekarar 2016 ne shugaban, mai shekara 74 a duniya, ya soma tafiya London domin yin jinyar abin da, a wancan lokacin, jami'an gwamnati suka bayyana da ciwon kunne.
A farkon wannan shekarar ma Shugaba Buhari ya koma London inda aka duba lafiyarsa.
A lokacin da ya koma kasar a watan Maris, ya ce an yi masa karin jini, ko da yake bai fadi larurar da yake fama da ita ba.
Sai dai shugaban na Najeriya ya ce bai taba yin jinya irinta ba a rayuwarsa.
A watan jiya ne mukaddashin shugaban kasar Yemi Osinabjo ya ziyarci Shugaba Buhari a London, kuma ya ce shugaban yana samun sauki.
Ga abin da Osinbajo ya ce sun tattauna da mai gidan nasa:
"Da farko kamar yadda kuka sani, na je ne in duba lafiyarsa domin in san yadda yake ji.
Kuma daman ina magana da shi ta waya, sai na ga ya dace in je in gan shi kuma in ga irin halin da yake ciki tare da ba shi labarin abubuwan da ke aukuwa a gida.
Saboda haka, mun tattauna da kyau kan abubuwa da dama kuma yana cike da annashuwa. Yana samun sauki sosai."
'Yan jarida sun tambaye shi:
Yaya jikin shugaban kasar?
E, kamar yadda na ce yana cikin annashuwa, yana samun sauki sosai. Kuma mun yi tattaunawa ta tsawon lokaci. Mun shafe fiye da sa'a daya muna tattaunawa, kuma yana nan kamar yadda aka san shi da raharsa. Yana samun sauki sosai.
Yaushe zai dawo?
Ina ganin a nan gaba kadan. Nan ba da jimawa ba. Ina ganin ya kamata mu tsammanci dawowarsa. Kamar yadda na fada yana samun sauki sosai.
Kun tattauna kan batun sakataren gwamnatin tarayyar da shugaban hukumar leken asiri?
Batutuwa da dama ne. Ba zan iya bayayya batutuwan da muka tattauna ba dalla-dalla.
Rashin lafiyar Buhari tun farkon shekarar 2017.
Wasu gwamnoni, ciki har da na jam'iyyar PDP mai hamayya da kuma shugaban jam'iyyar APC mai mulki sun gana da Shugaba Buhari a London, inda suka ce nan ba da dadewa zai koma kasar.
Rashin lafiyar shugaban na Najeriya na jawo ce-ce-ku-ce a kasar duk da yake ya mika mulki a hannun mataimakinsa kafin ya fice daga kasar, kuma har yanzu ba a tabbatar da lokacin da shugaban zai dawo ba.
Source: bbc hausa.

19 ga watan Jan - Ya tafi Birtaniya domin "hutun jinya".
5 ga watan Fabrairu - ya nemi majalisar dokoki ta kara masa tsawon hutun jinya.
10 ga watan Maris - Ya koma gida, amman bai fara aiki nan-da-nan ba.
26 ga watan Afrilu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba kuma "yana aiki daga gida".
28 ga watan Afrilu - Bai halarci Sallar Juma'a ba.
3 ga watan Mayu - Bai halarci zaman majalisar ministoci ba a karo na uku.
5 ga watan Mayu - Ya halarci sallar Juma'a a karon farko cikin mako biyu.
7 ga watan Mayu - Ya koma Birtaniya domin jinya.
25 ga watan Yuni - Ya aikowa 'yan Najeriya sakon murya. SAURARI MURYAR
11 ga watan Yuli - Osinbajo ya gana da shi a London.
22 ga watan Yuli - Wasu gwamnonin APC da shugaban jam'iyyar sun gana da shi.
24 ga watan Yuli - Karin gwamnoni, ciki har da na PDP - sun ziyarci Buhari
Wasu gwamnoni, ciki har da na jam'iyyar PDP mai hamayya da kuma shugaban jam'iyyar APC mai mulki sun gana da Shugaba Buhari a London, inda suka ce nan ba da dadewa zai koma kasar.
Rashin lafiyar shugaban na Najeriya na jawo ce-ce-ku-ce a kasar duk da yake ya mika mulki a hannun mataimakinsa kafin ya fice daga kasar, kuma har yanzu ba a tabbatar da lokacin da shugaban zai dawo ba.
Source: bbc hausa.
No comments:
Write Comments