Saturday

Wanene Qassem Suleimani - Dr, Sani Umar Rijiyar Lemu
Wanene Qassem Suleimani - Dr, Sani Umar Rijiyar Lemu : Download mp3
DARASI
MAUDU'I Siyasar Kasashen Larabawa, z@luncin Kasar Iran da Amurka da ta@ddancin Janar Qassem SuleimaniGABATARWA Ash-sheikh Dr Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu
Malamin yayi cikakken bayani da fashin baki akan siyasar duniya musamman gabas ta tsakiya, da tasirin Kasar Iran, da irin zalunci da ta@ddanci da barnan da shugaban sojojin Iran Janar Qassem Suleimani yayi a doron kasa kafin hallakarsa
Malamin yayi cikakken bayani akan alakar sirri dake tsakanin Amurka da Iran da irin yadda suke taimakon juna
-Ina wanda ke son sanin dalilin da yasa Amurka ta kashe Qassim S#leimani, da kuma shin za'a iya yin yaki tsakanin kasar Amurka da Iran?
-In wanda ke son sanin irin ta@ddancin da Kasar Iran take yi a Kasashen Musulmai da yadda kasashen turawa suke yiwa yaransu da suka raina?
-Ina wanda ke son sanin waye shugaban sojojin juyin juya hali na Kasar Iran Janar Qassim Suleimani da irin mugun ta@ddancin da yayi a doron duniya kafin ya hallaka?
DOWNLOAD NOW
@Arewasound
Sunday

INEC : YADDA ZA KA DUBA SUNAN KA DA MAZABAR KA A ONLINE .
YADDA ZA KA DUBA SUNAN KA DA MAZABAR KA A ONLINE .
Yau saura kwanaki 2 kacal wa'adin da hukumar zaben Najeriya INEC ta bayar na kowane mai son yin za6e a 2019 ya garzaya maza6ar da yayi rajista domin tabbatar da sunan sa. Tare kuma da kai korafin sa a cibiyar mazabar sa (ward center) idan bai ga sunan sa ba, ko kuma akwai matsala a sunan na sa.
GA DAMA TA SAMU !
Idan ba ka da iko na zuwa mazabar ka domin duba sunan ka, to za ka iya amfani da wayar ka domin duba sunan ka.Ga yadda abin ya ke :
HANYA TA FARKO
1 - bude manhajar ka ta Opera ko UC Browser sai ka yi bincike ta Google a wannan adireshin :Voters.inecnigeria.org
Akwai bayanan katin zaben ka da za a nemi ka cike a wannan shafi :
i- sunan jihar ka,
ii- sunan mahaifin ka,
iii- sunan ka,
iv- kwanan watan haihuwar ka (date of birth).
MISALI :
i- KANO
ii- MUHAMMAD
iii- IBRAHIM
iv- 01-10-2000.
KO KUMA :
(i) sunan jihar ka,
(ii) sunan ka (First name),
(iii) lambobi biyar NA KARSHEN VIN ( Voter's Identification Number ) da ke a cikin katin zaben ka, (kana kuma iya sa su gabaki daya).
Sannan ka aika.
MISALI :
i - KANO
ii - IBRAHIM
iii- 01234.
HANYA TA BIYU
2 - ka aika da sunan # Jihar ka, da # Sunan ka, da kuma lambobi 5 na kashe a VIN naka dake a cikin katin zaben ka zuwa ga WANNAN LAMBA :20120, ko kuma: 08171646879.
MISALI :
KANO
IBRAHIM
01234
zuwa ga 20120, ko 08171646879.
Allah Ya bada sa'a.
A TUNA CEWA KATIN ZABEN KA SHI NE MAKAMIN KA WAJEN FATATTAKAR DUK SHUGABAN BA YA KYAUTATA MAKA, TARE DA ZABEN WANDA KAKE SO YA SHUGABANCE KA.
Allah Ya yi mana zabi mafi alheri. Ameen.
Wednesday

Tofa!! Dangote ya bayyanawa matasa hanyar da za su zama kamar shi
Wani wanda ya halarci taron ya yiwa Dangote wasu tambayoyi, inda ya ke tambayar shi wane fanni zai fi mayar da hankali inda ace shi matashi ne dan shekara 21 a duniya, sannan kuma yana da sha'awar fara kasuwanci?
Attajirin ya ce zai fi mayar da hankalin shi akan harkokin sadarwa na zamani da kuma fannin noma.
"Wadannan su ne bangarori biyu da za su fi kowanne bangare kawo riba," in ji Dangote.
Sannan kuma mai kudin ya shawarci matasa akan irin dabi'un da suke da su bayan sun fara kasuwanci, musamman ma matasa na yankin Afirka.
Ya ce, "Matasa su na kashe ribar da ba ta zo hannunsu ba idan suna kasuwanci."
"Daga mutum ya fara kasuwanci kuma ya fuskanci kasuwancin yana samun cigaba, maimakon ya yi ta kara jari, sai kaga mutum ya kashe ribar kasuwar a tunanin shi na cewa ribar za ta cigaba da zuwa," in ji attajirin.
KU KARANTA: Yadda aka kama wasu mutane 3 yayin da suke yunkurin tono gawa daga kabari.
Dangote ya ce, "Idan mutum ya sayi manyan abubuwa na kyale-kyale da more rayuwa, za su dauke masa hankali daga harkokinsa na kasuwanci."
Mai kudin ya bada misali da kansa, in da ya ke cewa, "a yanzu haka bani da wani gida da nake zuwa domin na shakata, wanda ya ke mallakina a fadin duniyar nan."
"Amma kuma akwai da yawa daga cikin masu yi mini aiki da suke da gidajen shakatawa a birnin Landan." in ji Dangote.
Alhaji Aliko dangote dai shine mutum na daya da ya fi kowa kudi a nahiyar Afirka, Dangote cikakken Bahaushe ne, wanda ya fito daga jihar Kano da ke yankin arewacin Najeriya. Tun lokacin da ya zama na daya a nahiyar ta Afirka har yanzu ba a samu wani wanda ya ko kama kafarshi ba a nahiyar.
To sai dai kuma ba kasafai aka fiya samun masu kudi suna fitowa fili suna ba wa mutane shawarwari ba musamman masu kudi na nahiyar Afirka.
SOURCE LEGIT. NG
Monday

Hukumar Raba Hasken Lantarki za ta fara tilasta sayen mita kan naira 36,991.50
“MAP za su caji naira 36,991.50 ga wanda zai daura layin wuta daya tilo a gidan sa. Shi kuma wanda zai daura layi biyu, to zai sayi mita mai layi uku a kan kudi naira 67,055.85.
Arabi ya ce mitar ta yi tsada ne saboda an hada “farashin ta har da ladar aikin kaiwa har gida, daurawa, ladar zuwa a gyara maka idan ta lalace, ko kuma a canja maka wata idan ba za ta iya gyaruwa ba.”
Tuesday

Asalin tsafi : kissar Haruta Da Maruta.
QISSAR HARUTA DA MARUTA
.Asalin tsafi.
.Shin Mala'iku Ne Su Ka Koyar da Tsafi?
Daga Cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah, Masu Yin Ruq'yah Da Harhada Magungunan Musulunci. Lambar waya 08162600700.
Allah Madaukakin Sarki Ya ambaci sunayen Haruta da Maruta sau daya a cikin Alqur'ani mai girma, acikin Suratul Baqarah.
Ruwayoyi da dama sun zo akan Qissar wadannan sunaye na Mala'iku ko kuma Sarakuna amma dai za mu dauki jigon ruwayar da Ahmad ya fitar acikin Musnad, da kuma ibnu Hibban aciki Sahihinsa daga ibn Umar رضي الله عنهما
sai mu shigar da bayanin sauran ruwayoyin a ciki.
..
Ga cikakkiyar Qissar :
.Lokacin da Allah Madaukakin Sarki Ya saukar da Annabi Adam ﻋﻠﻴﻪ السلامdaga Aljanna zuwa kasan duniya, sai Mala'iku suka dinga cewa "Ya Ubangiji, yanzu ka sanya wadanda za suy 6arna su dinga zubar da jinin junansu a duniya?!, alhali mu muna girmamaKa tare da gode maKa kuma muna kaskantar da kai a gareKa?".
Sai Allah Ya ce "Ni Na san abinda baku sani ba".
Sai su ka ce "Ya Ubangiji mu fa mun fi yi maKa biyayya sama da 'yanAdam, inda mu ne ka saukar da mu duniya to ba za mu sa6a maka ba".
Sai Allah Ya ce musu "To ku kawo Mala'iku guda biyu a cikinku. Sai Mu saukar da su kasan duniya, don Mu ga yadda za su yi. (za suyi biyayya ko ba za suy ba?!)".
Sai suka ce "Ya Ubangiji Ga Haruta da Maruta mun za6e su a kaisu"
.
Sai aka saukar da wadannan Mala'iku biyu zuwa duniya, aka sauke su a garin Babila.
Lokacin da aka sauke su sai aka ce musu ga Tsafi nan ku dinga koyawa mutane amma duk wanda ya zo zai koya ku gaya masa in ya aikata ya zama kafuri.
A wata ruwayar kuma an ba su Sihiri ne domin su dinga yiwa mutane gargadi akan su guje shi kada su aikata shi.
To bayan an saukar da su sai Allah Ya mayar da Zahr', wato wannan babbar tauraruwar da muke gani a kuma da wata, sai aka mayar da ita siffar mace.
Sai ta zo wajensu a sura kyakkyawa.
Da su ka ganta sai su ka nemeta. Sai ta qi amincewa ta ce musu "Saidai in za ku kafurta to zan yarda da ku".
Da su ka ji haka sai su ka ce basu yarda ba.
Sai ta fi, ta sake dawowa da wani jariri a hannunta. Sai su ka kuma nemarta. Sai ta qi amincewa, ta ce "Saidai in za ku kashe wanan yaron, to zan ba ku hadin kai".
Sai su ka ce basu yarda ba. Sai ta tafi, ta sake dawowa da tukunyar giya a hannunta.
Suka nemeta. Sai ta ce bata yarda ba sedai in za su sha giya tukuna. Sai su ka yarda su ka sha giyar.
Bayan sun sha sai maye ya kama su, su kayi zina da wannan matar sannan kuma suka kashe wannan jaririn.
Lokacin da suka farka sai Allah Ya tambayesu alqawarin da sukayi akan ba za su sa6a masa ba.
Daga nan sai aka ba su za6i akan su za6i irin azabar da za ayi musu. Shin a duniya suke so ayi musu azaba ko kuma a bari sai an je Lahira?!.
.
Sai suka ce ai azabar Lahira bata karewa, mun za6i ta duniya.
Shikenan sai aka kai daya inda rana take 6ullowa. Kullum idan rana ta 6ullo sai ta tafasa masa kansa.
Dayan kuma sai aka kaishi inda rana take faduwa, kullum in rana zata fadi sai ta kona shi.
Ita kuma Zahra' sai aka mayar da ita tauraruwa ta koma sama.
.
To a lokacin ne aka ba su sihiri, (bisa sa6anin ruwaya).
Sai aka ce duk wanda ya zo yana so su koya masa.
Sai suka dinga koyawa mutane da Aljanu yadda ake raba tsakanin miji da mata amma basa koyawa kowa sai sun ce masa "Tabbas mu fitina ne!, don haka kada ka kafurta".
In Mutum ko Aljan ya yarda zai kafurta sai su koya masa.
Daga nan sai harkar Sihiri da tsafi ta yadu a tsakanin mutane da Aljanu.
.
Malamai sun yi raddi sosai akan wannan qissa musamman kasancewar Mala'iku basa sa6o da kuma maganar cewa su ne suka koyar da tsafi sannan ruwayoyin yawanci Isra'iyliyyat ne, sedai abinda aka samu na 6angarorin qissar daga Alqur'ani da kuma ruwayar ibnu Umar daga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
kamar yadda muka ambata.
.
Harkar Bokanci, Sihiri, Tsafi, Surkulle, Rufa-ido, Tsibbace-tsibbace da makamantansu, sun samu shahara sosai da kar6uwa a wajejen aiko Annabi Sulaiman عليه السلام
shi yasa ya zamto yana daga cikin manyan abubuwan da Annabi Sulaiman yay fada da su kuma ya yaqi masu aikata shi.
Sannan wannan harka ta samu kar6uwa ne da matsayi da shiga zukatan al'umma a wajenjen zamanin Annabi Musa عليه السلام،
inda a lokacin ake ganin wanda ya iya sihiri tamkar wani shugaba kuma wani abin ay wa biyayya sannan abin tsoro.
Za mu kawo cikakkiyar qissar yadda Annabi Sulaiman عليه السلام ya yaqi masihirtan zamaninsa da kuma dalilin da yasa bayan ya yi wafati Shaidanu suka ce ya mulki duniya ne ta hanyar tsafi.
.
Sannan za mu sake duba qissar Haruta da Maruta tare da bayanin yadda Annabi Musa ya fuskanci matsafan zamaninsa.
.
Duk wannan zai zo insha Allahu a cikin posting din mu mai taken "ASALIN TSAFI", Domin Allah Madaukakin Sarki Ya fada acikin Suratuz Zariyari cewa:
.Ma'ana:
ﻓَﻔِﺮُّﻭﺍ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺇِﻧِّﻲ ﻟَﻜُﻢْ ﻣِﻨْﻪُ ﻧَﺬِﻳﺮٌ ﻣُﺒِﻴﻦٌ * ﻭَﻻ ﺗَﺠْﻌَﻠُﻮﺍ ﻣَﻊَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺇِﻟَﻬﺎً ﺁﺧَﺮَ ﺇِﻧِّﻲ ﻟَﻜُﻢْ ﻣِﻨْﻪُ ﻧَﺬِﻳﺮٌ ﻣُﺒِﻴﻦٌ * ﻛَﺬَﻟِﻚَ ﻣَﺎ ﺃَﺗَﻰ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻣِﻦْ ﻗَﺒْﻠِﻬِﻢْ ﻣِﻦْ ﺭَﺳُﻮﻝٍ ﺇِﻻَّ ﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﺳَﺎﺣِﺮٌ ﺃَﻭْ ﻣَﺠْﻨُﻮﻥٌ [ ﺍﻟﺬﺭﻳﺎﺕ :50 - 52] .
.
"Kamar haka ne (Su wadannan mutanen) babu wani Annabi da ya zo wajen wadanda suka gabace su face sai sun ce masa mai Sihiri ko kuma mai hauka"..
Wannan ayah tana nuna cewa tun zamanin Annabi Nuhu ﻋﻠيﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
duk da cewa shi ne farkon Manzanni, duk Annabin da Allah Ya aiko sai Kafurai sun ce masa mai sihiri ne. Kenan tun a lokacin ana yin sihiri.
Wasu Malaman kuma suna ganin sihiri ya samo asali ne daga hannun Aljanu kuma dalilansu sun fi karfi gaskiya.
Insha Allahu za mu cigaba da kawo muku bayanai masuamfani, zasu zo nan gaba kadan da yaddar Allah.
Sunday

YADDA AKE YIN ISTIKHARA : Neman zabin Allah.
YADDA AKE YIN ISTIKHARA : Neman zabin Allah.
* Sai dai wurin Mustahabbi ana iyayi idan suncikaro, misali: mutum ne yake son yaje umra karona biyu a lokaci guda kuma yana so yaje watakasa neman ilimi, to yana iya neman zabin Allahakan ya zaba masa wanda yafi Alkhairi a cikin su.
* Hakika Duk wanda ya nemi zabin Mahalicci,kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma yayi azama a cikinlamarin sa, to ba zai yi nadama ba Insha Allah.Domin Allah Madaukakin Sarki ya ce: "Kuma kashawarce su cikin lamarin ka, idan kuma kaquduri aniya, to ka dogara ga Allah" [Ali-Imran :159].
* Hadisi ya gangaro Jabir ibn Abdullah, Allah yakara yarda dashi da Maihaifin saya ce : Manzon Allah (SAW) ya kasance yanakoya mana yin Istikhara (neman zabin Allah) acikin dukkanin al'amura kamar yadda yake koyamana sura daga cikin surorin Alqur'ani. Ya kance: ''Idan dayanku yayi niyyar yin wani al'amarito yayi sallah raka'a biyu ba farillah ba sannanya ce:
"Allaahumma innii astakhiiruka bi ilmika,wa'astaqdiruka bi kudiratika, wa'as'aluka minfadlikal azeem, fa innaka takadiru wala akadiru,wa ta'alamu wala a'alamu, wa anta allamulguyube, Allahumma inkunta ta'alamu anna hazalamri kharal lii fii deenii wama'ashii wa'akibati amrii, aajilihi wa'aajilihi faqadirhu lii wayassirhulii thumma baariklii fiihi, wa'inkunta ta'alamuanna hazar amra sharrullii fii deenii wama'ashiiwa'akibati amrii aajilihi wa aajilihi fasrifhu'anniiwasrifnii anhu wakadur liyal khaira haithu kaana thumma raddini bihi."Da Harshen Larabci
MA'ANA
"Ya Ubangijina! ina neman zabin ka da ilimin Ka,kuma ina neman tabbatuwar ikon Ka, ina rokanfalalar Ka Mai gaima, Kai ke da iko ni banda shi,Kai ne Masani ni ban san (komai ba) Kai nemasanin abin da yake boye. Ya Ubangiji na! Inkana ganin wannan abu ('sai ya fadi abin da yakeistiharan a kai') shi yafi min a addinina da rayuwata da qarshen lamarina, to ka tabbatar min dashi, ka sauqaqe min sannan ka yi min albarka acikinsa, in kuwa kana ganin wannan abu sharri negare ni a addinina da rayuwata da qarshenlamarina, ka juyar da shi daga gare ni, ni ma kajuyar da ni dagagare shi, ka kudurtarmin da alkhairi sannan kaamintar min da shi" [Bukhari]
* Na tabbata banbanci ya bayyana a fili gama'abota hankulla da tunani tsakanin wannankarantarwar ta shugaban talikai SAW, da Tsirfe-tsirfe da shafi fadin, wasu marubuta littattafankarya don neman kudi, da masu tsibbace tsibbace
* Ita dai wannan Sallah Mustahhabbi ce anso kayita (domin sunnah ce mai karfi, sannan zakasamu lada idan kayi), amma idan bakayi babalaifi.
* Wannan Addu'a ta istarawa ana yin tane bayanka sallame, sallar nan da kayi mai raka'a biyu,duk da wasu malaman na ganin ana karanta tane,bayan tahiya da salatin manzon Allah SAW kafinSallama, domin mafi Al-khairin bijiro da addu'aacikin sallah shine sujuda da bayan tahiya, saidai magana mafi rinjaye shine bayan Sallama.Allah shine Mafi Sani..* Babu Laifi ga mutum ya maimaita istakharasama da daya, hakam ya tabbata daga cikinmagabata, kamar Abdullahi dan zubair Allah yakara yarda dashi yayi istakhara sau ukku.[Muslum - 970].
ALLAH YA TAIMAKE MU Ameen

Kadan Daga cikin Sharrukan sanya security code a wayoyin mu | karanta ko ka fadaka.
SANYA PASSWORD A WAYA YAKAN IYA ZAMA SHIRIRITA WAI ZANI DA ALJIHU. - Abokai uku sukayi hatsari a mota duk suka jikkata. Saiga wani mutum yakawo musu agaji yana neman yakira wanda zai kawo dauki. Ga wayoyi guda 6 motar ammana kowacce da password dinta. Sanadiyyar hakan suka rasa rayukansu.
- Wata mai ciki ta fadi kasa sumammiya a gidan babu kowa sai wata yarta karama wacce batada waya. Yarinyar batasan meke faruwa ba tadai ga mahaifiyarta tana numfasawa da kyar. Tadauki wayar mahaifiyartan don ta kira mahaifinta, ammana wayar akwai password. Sai akayi sa'a wani yayanta yabar wayarsa a kan gado yatafi makaranta domin anhansu xuwa da phone makaranta. Tadauka ta kira mahaifinta cikin ikon Allah aka ceto rayuwarta saboda wayar yayanta (danta) babu password. Da ace ta rasa ranta da laifin waye?.
- Wasu yanfashi suka je fashi wani gida. Wani yaron gidan yana wani karamin daki wanda yanfashin suka zata store NE basu shigaba. Yaron bashida waya, sai kuma yazamana ga wayar Abbansa a dakin tana caji. Yayi kokarin Kira domin a kawo musu agaji ammana wayar akwai password. Sukayiwa yanmatan gidan fyade suka kashe su duk, sukabar wannan yaron Shi kadai domin basu ganshi ba. Duk abinda yake faruwa yana gani ta window. Kusa dasu kuwa akwai police station ga kuma army barrack ma ba nisa dasu kuma duk yanada numbers din ammana babu yadda zaiyi domin wayar Addan nashi akwai password.
- Wani matashi ya mutu wanda yakeda wassu maqudan kudi a wani banki. Duk bayanan suna wayarsa. Ammana babu wanda zai iya gano bayanan saboda wayar tashi akwai password. Shawara gareku Yan'uwa masu hankali da tunani: Kimar ka/ki yafi daraja sama da bayanan da kake/ kike kokarin 6oyewa. Idan yazama dole zaka/zaki 6oye sirrin, yazama password din a whatsapp, text messages, facebook, files, da sauransu za a sanya sai a bar wajen yin kira a bayyane babu password domin tayiyu watarana ka ceci rayuwarka ko rayuwar na Kusa dakai.
Wednesday

Salah mistakes series : A free Guide video
Ya kai Dan uwa, Ya ke "Yar uwa, ku daure ku kalli wannan videon domin gyara tsakaninka da mahaliccin ka , Saboda ita sallah itace ta farko a cikin gerin rukunan musuluncin nan guda biyar, ganin haka ne ma yasa mukace bari mu bayar da wannan videon don gani da kuma kwaikwayon yadda Annabi Muhammad S.A.W ya dinga gudanar da sallarsa a iya tsawon rayuwarsa da fatan Allah ya karbi sallolin da muke gabatarwa AmeenCLICK HERE TO DOWNLOAD VIDEO
Sunday

Kadan Daga cikin Sharrukan sanya security code a wayoyin mu | karanta ko ka fadaka
- Abokai uku sukayi hatsari a mota duk suka jikkata. Saiga wani mutum yakawo musu agaji yana neman yakira wanda zai kawo dauki. Ga wayoyi guda 6 motar ammana kowacce da password dinta. Sanadiyyar hakan suka rasa rayukansu.
- Wata mai ciki ta fadi kasa sumammiya a gidan babu kowa sai wata yarta karama wacce batada waya. Yarinyar batasan meke faruwa ba tadai ga mahaifiyarta tana numfasawa da kyar. Tadauki wayar mahaifiyartan don ta kira mahaifinta, ammana wayar akwai password. Sai akayi sa'a wani yayanta yabar wayarsa a kan gado yatafi makaranta domin anhansu xuwa da phone makaranta. Tadauka ta kira mahaifintan cikin ikon Allah aka ceto rayuwarta saboda wayar yayanta (danta) babu password. Da ace ta rasa ranta da laifin waye?.
- Wassu yanfashi suka je fashi wani gida. Wani yaron gidan yana wani karamin daki wanda yanfashin suka zata store NE basu shigaba. Yaron bashida waya, sai kuma yazamana ga wayar Abbansa a dakin tana caji. Yayi kokarin Kira domin a kawo musu agaji ammana wayar akwai password. Sukayiwa yanmatan gidan fyade suka kashe su duk, sukabar wannan yaron Shi kadai domin basu ganshi ba. Duk abinda yake faruwa yana gani ta window. Kusa dasu kuwa akwai police station ga kuma army barrack ma ba nisa dasu kuma duk yanada numbers din ammana babu yadda zaiyi domin wayar Addan nashi akwai password.
- Wani matashi ya mutu wanda yakeda wassu maqudan kudi a wani banki. Duk bayanan suna wayarsa. Ammana babu wanda zai iya gano bayanan saboda wayar tashi akwai password. Shawara gareku Yan'uwa masu hankali da tunani: Kimar ka/ki yafi daraja sama da bayanan da kake/ kike kokarin 6oyewa. Idan yazama dole zaka/zaki 6oye sirrin, yazama password din a whatsapp, text messages, facebook, files, da sauransu za a sanya sai a bar wajen yin kira a bayyane babu password domin tayiyu watarana ka ceci rayuwarka ko rayuwar na Kusa dakai.
Saturday

KO Ka shiga tsarin N-power: Maza-Maza ka Shiga nan Don ganin yadda ake Register A saukake.

A yaune Za'a fara yin jarabawar , kuma kamar dai yadda aka sanar cewa wadanda suka zabi bangaren N-VOID wato Haraji sune za'a fara yiwa jarabawar tantancewa.
Ga wadanda basuyi register ba zasu shiga shafin n-power ta hanyar danna wannan link N-Power Online Registration
Abubuwan da ake bukata sun hada da
- LAMBAR ACCOUNT
- BVN NUMBER
- LAMBAR WAYA
- d.s
DOMIN FARA TANTANCEWA
sai a dannan nan.
N-power test
A jiya ne hukumar ta sanar da fara jarrabawar gwaji wanda
hakan yana daya daga cikin hanyoyin tantancewa da hukumar npower keyi.
Thursday
GUDUNMAWAR SHEIK ZAKIR NAIK GA MUSULUNCI DA KUMA KALUBALEN DA YAKE FUSKANTA.
- TARIHIN RAYUWARSA A
- TAKAICECikakken sunansa shine Zakir Abdulkareem Naik.
An haife shi a ranar 18 Oct. 1965 a birnin India na Mumbai a Maharashtra.
Zakir ya hallaci makarantu da dama inda ya samu shaidar zama likitan tiyata wato
"Bachelorof Medicine and Surgery".
Zakir Naik na tare da mai dakinsa Farhat
Naik, dakuma 'yaya biyu Fariq Naik da Rushdaa Naik. .
Zakir Naik ya tsinci kansa cikin sahun masuDa'awah a shekarar 1991, lokacin da Muslunci ya tsinci kansa cikin tsangwama da muwiyacin hali a kasar India saboda gallazawar da masu addinin Hindu kewa Muslunci da Musulmi.
Zakir ya tasirantu ne da salon da'awar
sannanen malam nan wato Sheikh Ahmad Deedat wanda
Zakir ya hadu dashi a shekarar 1987, kamar yadda Naik na sheda a 2006, saboda tarin baiwa ta ilimi da Allah yayiwa Zakir yasa Deedat da kansa yake masa lakabi da "Deedat-Plus" wato kamar kace, "Malam da rabin Malam".
- RUGUZA MASALLACIN BABRI
(masallacin) Babri mai dadden tarihi a cikin garin Ayodhya bayan haka suka ruguje masallatai masu yawa a yankin, masallacin Babri an gina shine tun qarni na 16 kimanin shekaru 500 da suka
wuce. Rushe masallacin ya jawo gagarumar riga wadda tayi sanadiyar asarar dukiyoyi masu tarin yawa da kuma mutuwar mutane fiye 2,000 wadanda yawancinsu Musulmi ne.
Hakika wannan rigima ta kara jefa Musulman India cikin halin ha'ula'i, zullumi da kaskanci, suka zamo basu da wata ta cewa, Muslunci ya zama abin zolaya gami da tsokana. Ana cikin wannan hali ne, Allah yayi nufin dawo
da martabar Muslunci da Musulmi ta hannun Sheikh Dr. Zakir Naik, kamar yadda Muhammad Reyaz ya sheda.
- DEBATES DINSA
da sanannen masanin kimiyar nan Dr. William Campbell a birnin Chicago ta Amurika.
Campbell ya kwashe shekaru yana nazari kafin daga bisani ya wallafa wani littafi da yace Qur'an yaci karo da kimiyar zamani (modern science).
Muhawarar mai taken "The Qur'an and the Bible in the Light of Science" ta daukaka Naik saboda yadda yayi kaca-kaca da littafin da aka dau shekaru ana wallafa shi da hujja cikin kankanin lokaci,
hakan yasa Zakir ya zama abin tsoro tsakanin masu yiwa Muslunci zambo, kamar su Ali Sina wani dan asalin Iran mai tsananin adawa da Muslunci.
.
Zakir Naik wanda zaka iya kwatanta
kwakwalwarsa data "computer" saboda
kaifin rike abu, ya gudanar da lakcoci kusan 4000 a fadin duniya baki daya wanda ya hada da zuwansa Nigeria har sau biyu.
- NASARORINSA
i :- tashoshin satellite na Peace TV English, Peace TV Bangla, Peace TV Urdu da kuma Peace TV Chinese. Tashoshin wadanda babu kamar su wajen yada addini, kimanin mutane miliyan 150
ne suke iya kama Peace TV a kasashe fiye da 200.
Zakir Naik ya samar gami da jagorantar
ii :- "Islamic Research Foundation" (IRF) wato cibiyar bincike ta addinin Muslunci, a karkashin IRF aka samar da (IIS) wato "Islamic International School".
iii :- Sai kuma (UIA) "United Islamic Aid" wadda aikinta shine bada tallafin karatu ga nakasassuda masu rauni.
Irin wannan nasarori da Zakir Naik ya samu, gami da dawo da martabar Musulmai a India dama duniya baki daya, sune suka tsone idanun
munafukai musamman masu son gani bayan Muslunci, tako wace fuska.
Gazawar masu son ganin bayan Muslunci a sakamakon Zakir, yasa suke kokarin ganin bayansa, ta hanyar tsomashi cikin ayyukan ta'addanci, zargin da ako yaushe yake musawa.
Karku manta jam'iyar Bharatya Janata Party (BJP) wacce ta taka rawa wajen gallazawa Musulman India itace ke mulki yanzu. Kuma Prime Minister na yanzu Narendra Modi babban
yaron Lal Krishna Advani ne, wanda ya
jagoranci ruguza masallatan Ayodhya a 1992. Saboda haka babu mamaki cikin sabon salon rufe bakin Musulmai ta hanyar gamawa da Zakir Naik a farko.
.
- MUSULMAI MASU ADAWA DASHI.
Amma yawancin qungiyoyin musulmai na mara masa baya kamar su: Sheikh Abdulkadir Jilani Foundation, Darul Uloom da kuma All-India Sunni Board.
- BARAZANA GA RAYUWARSA
Vishva Hindu Parishad (VHP) wato Sadhvi ya bada sanarwar bada tukyici na dalar Amurika $78,000 ga duk wanda ya fillo kan Zakir Naik. Hakan yazo kwana daya bayan wata kungiyar Shi'a maiwa
kanta laqbi da Hussaini Tigers. ta sanya ladan $23,000 ga wanda ya kashe Zakir Naik.
- DAUKAKARSA
mutane 100 dake da karfin fada aji a India kasar dake da mutane fiye da biliyan daya da miliyan dari uku.
(1.3 bn) ya sake zama na 82 a shekarar 2010 kamar yadda The Indian Express ta sanar.
Monday
Tambayoyi Bayan An Rufe Mutum A Kabarin sa.
Sheikh Isa Ali Pantami
Annabi (SAW) Ya ce idan mutum ya mutu, Mala’iku biyu za su zo masa sannan su masa tambayoyi hudu a kabarinsa.
Wadannan
Tambayoyi Sune:
- 1 Waye Mahaliccinka?
Amsa: ALLAH. - 2 Menene addininka?
Amsa: Addini na shine Musulunci - 3 Me za ka ce akan wannan da
aka aiko muku?
Amsa: Muhammad, kuma Manzon Allah - 4 Menene ilminka?
Amsa: Na karanta littafin Allah,
kuma na yi Imani da shi.
Annabi Muhd (SAW) Ya ce duk wanda ya amsa ko ta amsa tambayoyin nan dai dai a kabari, za a rubuta sunansa/ta a cikin “ILLIYUN”. Wanda shine rejista ta sunayen ‘yan Aljannah.
(Abu Daud, 4753; Ahmad, 18063; Saheehul Jamiy, 1676).
Wednesday

MANYA MANYAN MATSALOLIN DA DANDALIN FACEBOOK YAKE KUNSHE DA SU
Facebook a wajen abokai ko 'yan matansa - yana ganin ai shi wani dan birni ne wayayye, mai amfani da wata hanyar sadarwa mai tasiri da a tunaninsa kowa da kowa suka yarda da shahararta - bayan ya ga wannan kasida kuma yaji hankalinsa ya tashi. Wannan ka'ida ce ta rayuwa. Don haka sai mu kiyaye.
Kamar yadda muka yi bayani a baya, wannan dandali ya shahara, ya kasaita, ya kuma tumbatsa a duniyar Intanet. Wanda ya mallaki wannan dandali, watau Mark Zuckerberg, a halin yanzu yana daga cikin matasa masu kudi a duniya. Wannan ke nuna cewa hatta a bangaren kasuwanci dandalin ya bunkasa. To amma kuma akwai matsaloli masu dimbin yawa da ke tattare da wannan shafi na dandalin
Facebook. Wadannan matsaloli sun kasu kashi biyu. Na farko sun samo asali ne daga shafin shi kanshi; yadda aka tsara shi, da yadda ake tafiyar da shi. Na biyu kuma sun samo asali ne daga yadda masu mu'amala da shafin ke amfani da shi. Babban abin da ya zaburar da ni wajen kawo wadannan bayanai dai shi ne don mutanenmu Hausawa da suka fara yaduwa da barbazuwa a shafin, ta hanyar mallakar shafukansu na kashin kansu, wadanda kuma galibinsun matasa ne; maza da mata. Wajibi ne mu fahimci cewa akwai bambancin al'ada da addini a tsakaninmu da mafi yawancin masu amfani da wannan shafi a wasu kasashe, musamman kasashen yammacin duniya. Wannan zai taimaka mana wajen daina kwaikwayon da yawa cikin abubuwan da suke yi marasa kyau a shafin, wadanda kuma muna gani, muna karantawa. Ire-iren wadannan matsaloli ne ma tasa wasu daga cikin malaman addinin musulunci musamman suke ganin kamar haramun ne musulmi ya rika mu'amala da shafin ko a shafin. Kuma ba komai ya kawo wannan fatawa mai zafi ba sai don ganin abin da ke faruwa a shafin dandalin Facebook. Ni dai a iya 'yar gajeriyar fahimta ta, ya danganci yadda ka yi amfani da shafin. Idan ya zama ka kiyaye dokokin Ubangiji a matsayinka na musulmi a yayin da kake mu'amala da jama'a a wannan dandanli, to, hakika ka tsira. Amma idan ka dauki tafarkin 'yan duniya, masu ganin ai yanzu duniyar ta waye, dole ne a tafi da zamani, to kai ka jiwo, sautun mahaukaciya. Kada mu tsawaita, a halin yanzu ga wasu daga cikin wadannan matsaloli. Da fatan za mu kiyaye. Allah ya mana jagora, amin.
Cin Mutuncin Addini
Wannan ita ce matsala ta farko daga cikin matsalolin da suka fi shahara a dandalin Facebook. Kuma daga cikin addinan da wannan matsala ta shafa akwai addinin musulunci. Kuma wannan matsala ta cin mutuncin addini ta samo asali ne daga wajen masu amfani da wannan shafi. Shekaru biyu da suka gabata wata kungiya da ba a san ko su waye ba sun bude wani shafi da ke kira zuwa ga zanen hoton Manzon Allah (SAW), a daidai lokacin da suke gab da bikin farin cikin zagayowar ranar da wani mai zane dan kasar Denmak ya aiwatar da wannan mummunar aiki, kamar yadda suka sanar. Wannan lamari ya tayar da kura a dandalin gaba daya, inda har musulmai suka bude shafi don nuna damuwarsu kan wannan lamari. Nan take sauran musulmi da ke dandalin suka fara bore. Aka kirkiri wata rajista ta musamman don baiwa kowane musulmi sanya hannu kan kira ga shugabannin Dandalin Facebook su rufe wancan shafi da ke kira zuwa aibanta Manzon Allah ta hanyar zana hotonsa. Cikin awanni ashirin da hudu aka samu musulmi sama da dubu hamsin da takwas da suka rattafa hannunsu kan wannan rajista. Bayan nan kuma, musulmin kasar Pakistan sun yi zanga-zanga a gaban ginin majalisar dokokin kasar don kira ga majalisar ta fitar da dokar da za ta haramta mu'amala da shafin
Facebook a kasar gaba daya. Ganin haka ke da wuya sai hukumar dandalin
Facebook ta rufe wancan shafi.
Faruwar wannan lamari ya baiwa da yawa cikin musulmi haushi, inda suka yi ta fita daga dandalin, suka ta rufe shafukansu, kuma suna ta kira ga duk wani musulmi ya fice daga wannan dandali. Duk da cewa hukumar Facebook
ta kulle wancan shafi da ke batanci ga Annabi Muhammad (SAW), da yawa cikin musulmi basu sake da ita ba, domin a yarjejeniyar asali da hukumar shafin ta tanada, sun nuna cewa kowa yana da hakkin bayyana ra'ayinsa na siyasa ne ko na addini, muddin ba zai ci mutuncin addinin wani ko al'adarsa ba. In kuwa haka ne, to bai kamata ma tun asali hukumar ta bar masu wancan shafi na batanci har su kai gaci ba, tunda ra'ayin da suke kokarin bayyanawa ya ci karo da wannan yarjejeniya. To me yasa ba a hana su ba har sai da musulmi suka nuna damuwarsu, har aka yi kokarin kawar da shafin daga kasar Pakistan, sannan suka rufe? Wannan, a cewar da yawa cikin musulmin kasar, alama ce da ke nuna cewa lallai hukumar Dandalin Facebook basu dauki addinin musulunci a bakin komai ba. Wannan matsala ta farko kenan.
Gulma da Hirar Banza
Ba dandalin Facebook kadai ba, duk inda majalisar Intanet take, ana samun yawaitar gulmace-gulmace da karairayi marasa tushe. To amma wanda ake samu a dandalin Facebook ya fi kowanne yawaita da maimaituwa. Ba don komai sai don hanyoyin mu'amala da shafin sun yawaita matuka. Bayan kwamfuta da ake iya amfani da ita wajen shiga dandalin, kana iya amfani da wayar salularka, wacce kake damfare da ita a duk inda kaje, muddin akwai Intanet a ciki. Wannan ke bayar da damar ganin a kowane lokaci ka fadi wani abu, ko halin da kake ciki, ko inda kaje, ko wani abin da ka gani, ko abin da wani ya fada. Duk wanda ke ziyartar shafukan Hausawanmu matasa a
Facebook zai fahimci abin da nake nufi. Bayan zumunci, wanda ake yinsa sosai kuma abin alfahari ne a garemu, akwai batanci da ke samuwa, da zage-zage ga wasu daga cikin shugabanninmu wadanda suka shude ko suke kan mulki. Dukkan wannan, a riyawar masu shafukan da kuma wadanda suka assasa shafin, fadin albarkacin baki ne. To amma da za a auna wa mutum nauyin kalmomin da yake fada miyagu a kan wasu, da irin hukuncin da ke jiransa a kabari ko a kiyama, da ba haka ba. Wajibi ne kowane musulmi ya san cewa, kamar yadda za a tambayeshi kalmomin da ya fada da harshensa, da wadanda ya daka ko ya yafuta da hannunsa ba tare da hakki ba, to haka za a titsiye shi ya yi bayanin abin da ya rubuta da hannunsa a filin kiyama. Wannan matsala ta gulmace-gulmace da hirar banza marasa alfanu su suka fi yawa a shafukan dandalin Facebook. Tabbas akwai raha da ake yi a tsakanin abokai, ko magoya bayan wasu kungiyoyi na kwallo ko na siyasa. Wannan raha da ake yi dole ne yana da ma'auni. Ma'auninsa kuwa shi ne tabbaci ko rashin tabbacin kalmomin da ake fada a yayin da ake rahan. Ma'ana, gaskiya ko rashin gaskiyar kalmar da aka fada. Don haka sai a kiyaye. Sai matsala ta gaba.
Haifar da Tsana da Hassada
Daga cikin matsalolin dandalin Facebook
manya akwai haifar da tsana da hassada. Watakila mai karatu zai yi mamaki, musamman ganin cewa rubuce-rubuce ne kawai ake yi a shafukan. Da farko dai babu abin da ke haifar da yawan tsana a tsakanin masu mu'amala da shafin sai gulmace-gulmace. Ire-iren wadannan matsaloli kan haddasa yankewar alaka a tsakanin wadanda abin ya shafa, ko da kuwa a zahirin rayuwa suka hadu. Yawan zage-zage, da gulma, da rade-radi marasa tushe, da kuma fadi-ba-tambayeka ba, duk su ne ke haddasa tsana a tsakanin dandalin. Babban abin da ke haddasa samuwar hassada kuma shi ne yadda wasu ke sifata rayuwarsu da abin da suke riya cewa sun mallake shi wanda karya ne, ko darajan ilminsu, ko martabarsu a rayuwa, ko wasu mukamai da aka basu a shafi ko dandalin. Mai karatu zai mamakin jin cewa akwai mukamai na sarautar gargajiya da ake dasu a shafukan Facebook; bangaren dandalin Hausawa nake nufi. Wadannan mukamai na sarauta don raha ne aka kirkiresu. Amma shaharar masu mukaman ko ganin yadda suka samu karbuwa a wajen mambobin da ke dandalin, na iya haifar da hassada a zukatan wasu. Wannan a tabbace yake, domin hatta a Majalisun Tattaunawa na Yahoo! da Hausawa suka mallaka, ana samu wannan matsala. To, a shafukan
Facebook ma akwai ta. Ba komai ya dada taimakawa ba sai ganin cewa gilli da hassada wasu dabi'u ne da Allah ya rakkaba dan adam a kansu wajen halitta. Maganinsa na samuwa ne ta hanyar karantar ilmin addini da kuma aiki da shi. Sai matsala ta gaba.
Gajiya da Damuwa
A duniyar Intanet, babu abin da ya fi haddasa gajiya da damuwa (Stress and Fatige) kamar shafukan abota irinsu
Facebook. Hakan na samuwa ne sanadiyyar dadewan zama ana abu daya, da kallon gilashin kwamfuta ko wayar salula masu dauke da sinadaran hasken da ke cutarwa a hankali a yayin da ake karatu ko rubutu, da kuma tsawaita tunani ko damuwa ko bakin ciki kan abin da ya faru ko yake faruwa a shafi ko dandalin da mutum ya mallaka. Bayan haka, idan mutum ya kamu da mummunar shakuwa kan Intanet, watau
Cyber Addiction, wata matsala mai zaman kanta na iya samuwa. Matsalar kuwa na iya nuna kanta ne ta hanyar zazzabi a duk lokacin da ba a samu damar shiga dandali ko shafin ba, da kuma tsawaita bakin ciki mara misali da ma'ana kan abin da mai shafin yake kullawa. Kai a takaice ma dai, ana iya kaiwa wani mataki wanda shi kanshi mai shafin ba zai taba samun natsuwa da jama'ar da yake rayuwa da su a gida ko unguwarsu ba, sai ya shiga dandalin
Facebook da ke wata duniya tsakanin mafarki da hakika. Sai matsala ta gaba.
Kashe-Kashe da Ta'addanci
Nau'ukan kashe-kashe da ta'addanci mara misaltuwa – wadanda kafafen labarai suka hakaito da wadanda ba a hakaito ba – ruwan dare ne a duniyar Intanet, kuma hakan ya fi shahara ne a kasashen yammacin duniya. To, watakila mai karatu yace ai mu ba ruwanmu da wannan bakin rayuwa. A a, daga na gaba ake ganin zurfin ruwa. Idan gemun dan uwanka ya kama da wuta, maza ka nemi gulbi ko tafki ko kududdufi ka tsoma naka a ciki. A dandalin Facebook an samu ire-iren wadannan matsaloli, inda masu sace kananan yara ke amfani da adireshin gidajen iyayensu, ko barayi ko kuma wadanda aka tura su don kashe wani, galibi sukan yi amfani ne da shafukan
Facebook don sanin fici-da-shigin wanda suke son kamawa ko kashewa ko masa ta'addanci. Domin dandalin Facebook
taska ce inda galibin turawa sukan rubuta duk abin da ya shafi rayuwarsu baki daya. Sannan ko tuntube suka yi a kan titi, sai sun rubuta. To, haka ma mutanenmu da ke dandalin. Sai ka ga mutum ya rubuta cewa, yanzu bacci nake ji, ko yunwa nake ji, ko ba ni da lafiya, ko jiya na je wajen wance ta wulakanta ni, ko na fi sha'awan abin ci ko abin sha nau'i kaza. Dukkan wadannan bayanai ne na sirri da suka shafi rayuwarka, kuma wani abokin gaba na iya amfani da su wajen cutar da kai, kamar dai yadda muke jin labari a wasu kasashen. Tabbas babu abin da zai faru da kowane dan adam sai abin da Allah ya kaddara masa, to amma Allah da kansa ya sanar da mu cewa mu kiyaye. Don haka sai a kiyaye. Sai matsala ta gaba.
Dodorido
Kalmar dodorido ta shahara a dandalin Hausawa a Intanet. Kuma abin da kalmar ke nufi shi ne yin amfani da fuska ko sunan wani daban don boye kai. Ma'ana wani ya bude shafi da sunan wani shahararren mutum, yana nuna cewa shi ne wannan mutumin, alhali ba haka bane. Yana iya nemo hoton mutumin ya lika, ya samo ra'ayoyinsa na siyasa ko na addini, ya kattaba a shafin, yana muzurai wai shi ne wane. Duk wannan na samuwa ta hanyar dandalin
Facebook. In kuwa haka ne, to ya kamata ka san da wa kake mu'amala. Karairayi da yaudara sifofi ne guda biyu da suka shahara a duniyar Intanet. Dole ne ka zama mai iya tantancewa; da wani irin mutum kake alaka? In kuwa ba haka ba, za ka sha mamaki. Wani abin bakin shi ne, masu irin wadannan dabi'u na boye kai sun fi shahara a shafukan abota irin su Facebook da Twitter. Don haka sai a kiyaye. Sai matsala ta gaba.
Batsa da Ashararanci
Yadda batsa da ashararanci suka yadu a duniyar zahiri da muke rayuwa a ciki, to haka suka yadu a duniyar Intanet. Akwai shafuka na musamman masu sayar da zina ko hotunan batsa. Amma a dandalin Facebook galibi hanyoyin "hada waya" ne ake da su. Ma'ana, ta hanyar wannan dandali da yawa cikin masu wannan dabi'a kan hadu, su yi abota, su shirya wurin haduwa, sannan a yi abin da ake son yi. Kowa da jama'arsa! Galibin abotan da ake shiryawa ko kullawa a ire-iren wadannan shafuka – ko dai tsakanin maza da mata, ko tsakanan mata da mata, ko kuma tsakanin maza da maza. Al'amuran sai dai addu'a. A wajen masu wannan dabi'a, dandalin Facebook wajen neman abokan hulda ne da harka. Domin a wajen bayanan da suka shafi mutum kana iya sanin manufarsa idan ya rubuta. Maza yake son abota da su ko mata kadai. Mace take son yin abota da ita ko maza kadai, duk za ka samu. Bayan haka, wasu ma kan wuce gona da irin shukawa, su bayyana hakikanin abin da suke nufi ko so. Wasu kalmar baka ce kadai, ba sa nufin abin da suka rubuta, amma wasu kuma da gaske suke yi. Sai an latsa ake iya bambancewa. Allah kiyashe mu mummunar latsi. Sai a kiyaye. Sai matsala ta gaba.
Yawan Shagaltuwa da Shagaltarwa
Da yawa cikin makarantun da ke kasar Amurka da sauran kasashen yammacin duniya, sukan sanya wa shafin dandalin
Facebook takunkumi, ta yadda idan a makarantar kake, ba za ka iya shiga shafin ba. Ba don komai ba sai don yadda dalibai suka jarabtu da shafin, wajen abota da hirarraki marasa alfanu. Wanda kuma hakan yana mummunar tasiri kan karatunsu. Domin ba su samun daman zama su yi nazarin darussan da aka karantar da su. Haka hukumomi da ma'aikatun da ke wadannan kasashe, har da ma kasashe masu tasowa, sukan sanya wa wannan shafi takunkumi a ma'aikatar, ta hanyar masarrafar garkuwar wuta, watau
Firewall. Domin an lura cewa galibin ma'aikata kan shagaltu da wannan shafi, har kadarin aikin da suke yi ya ragu. Wannan na cikin abin da ke dada harzuka masu wadannan ma'aikatu, har dai a karshe suka ga ba sarki sai Allah, suka katange ma'aikatansu daga wannan bala'i.
Wadannan dabi'u na shagaltuwa da shagaltarwa a bayyane suke a wannan dandali. Domin idan ka fara mu'amala ko abota da mutane, gaba daya zuciyarka za ta koma kan dandalin ne kacokam. Za ka ji in ba shafin kaje ba, kamar baka samu cikakkiyar rayuwa ba. Idan har ka fara jin haka, to ka san cewa lallai wadannan miyagun dabi'u guda biyu sun shige cikin kwaroron jinin jiki da zuciyarka, kamar yadda guban cizon sauro ke kwararowa cikin jiki. A matsayinka na wanda makaranta ko ma'aikatar da kake aiki basu katangeka daga wannan matsala ba, ka san cewa kana da aiki mai girma. Domin babu abin da ya fi wahala irin tarbiyyantar da kai. Don Allah a rika kiyayewa, a san cewa lokaci yana da tsada, kuma da zarar ya wuce fa, ba zai kara dawowa ba.
Matsalolin Gudanarwa
Matsalolin da za mu dakata a kansu su ne matsalolin gudanarwa da wannan dandali ke fama da su. Da farko dai, akwai rade-radin da ya game duniyar Intanet mai nuna cewa lallai hukumar gudanarwar dandalin Facebook na sayar da bayanan da suka shafi jama'a, wanda suke taskancewa cikin kwamfutocinsu, ga kamfanonin kasuwanci da binciken dabi'un mutane a Intanet. Wannan, in har gaskiya ne – wanda kuma akwai alamar hakan – ba karamar cin amana bace. Domin a cikin kundin yarjejeniyar da kowane mamba ke yarda da su kafin a bashi shafi, sun nuna cewa ba za su bayyana bayanansa na sirri ga wani daban ba. Yanzu kuma a samu labarin cewa kamfanin na sayar da wadannan bayanai da suka shafi sirrin rayuwar jama'a ga wasu, ba karamar cin amana bace.
Bayan haka, idan kana mu'amala da shafin Facebook, a duk lokacin da ka shiga matsala, to ba ka da wanda zai warware maka matsalar da ka tsunduma ciki. Da zarar ka je shafin neman taimako, watau Help Page, babu abin da za ka ci karo da shi sai tsofaffin bayanan da ko kadan ba za su dace da matsalarka ba. Wannan matsala kuwa ta samo asali ne saboda masu gudanar da wannan shafi basu ajiye wani mutum na hakika, wanda zai rika zama yana amsa matsalolin masu shafuka a dandalin ba. Manhajar kwamfuta ce suka tanada, wacce da zarar ka tura musu bukatar a warware maka wata matsala, sakonka na isa inda take, sai kawai ta cillo maka rariyar likau din da za ta kaika wajen wancan shafi da muka yi bayaninsa a sama. Wannan ke nuna mana cewa lallai araha ba ta ado.
Sannan a wasu lokuta ba abin mamaki bane ka nemi shiga dandalin ma gaba daya, sai a ce maka: "Yi hakuri, a halin yanzu muna fuskantar wasu 'yan matsaloli ne…nan da minti daya ka sake kokarin shiga." Minti daya na karewa idan ka nemi shiga za ka sake samun wannan sako. Wannan ba karamar matsala bace. Domin idan ya zama rayuwarka da farin cikinka gaba daya suna cikin shafin Facebook ne, to watarana idan aka yi rashin sa'a kwanakinka suka kare, sai buzunka. Wajibi ne a kan masu gudanar da wannan dandali su tanadi kwamfutoci masu dimbin yawa da girman mizani, da masarrafai ko manhajoji masu nagarta da tasiri wajen tsare bayanai da iya mika su cikin lokaci. In kuwa ba haka ba, abin da ya samu shafuka irin su MySpace, zai same su. Abin da yaci Doma, ko kadan ba zai bar Awe ba. Muddin mutane ba su samun daman shiga shafukansu a lokacin da suke so, kamar yadda aka musu alkawari, to, da zarar an samu wani shafi da yafi shi nagarta, kowa zai kaurace masa ne.
Sai matsala ta karshe, watau "goge" shafi daga kwamfutocin kamfanin
Facebook. Idan ka gaji da mu'amala da shafinka na Facebook, ba ka da wata hanyar goge shafin gaba daya, sai dai ka "kulle". Idan ka je bangaren "Settings" da ke shafinka na Facebook, a can kasa, za ga an rubuta "Deactivate Your Account". Kalmar "Deactivate" na nufin ka kulle shafin ne daga amfani da shi, amma dukkan bayananka, da hotunanka, da sauran abubuwanda suka shafeka, suna nan daram-dakam a kwamfutocinsu. Ma'anar wannan kalma ta sha bamban da kalmar "Delete",
wanda duk masanin harkar sadarwa ya san gogewa ake nufi. Wannan kuma ke nuna cewa nan gaba suna iya amfani da su. Watakila mai karatu ba zai fahimci matsalar da ke tattare da hakan ba, tunda mu a nan bamu cika damuwa da sirrin bayanan da suka shafe mu ba. Amma ga wadanda suke wasu kasashe, ba karamar matsala bace da kuma barazana ga rayuwa ko mutuncinsu. Duk da yake wasu sun gano wata sabuwar hanyar da ake bi a goge shafin baki daya, amma da sauran rina a kaba. Musamman ganin cewa masu gudanar da wannan shafi sun ki fitowa fili karara don nuna wa masu mu'amala da shafukansu yadda za su iya goge dukkan abin da suka rubuta ko adana a ciki. To me yasa suka ki bayyanawa? Oho! Allah kadai ya san addu'ar kurma. Abin da yake wajibi ga mai mu'amala kawai shi ne, ya san irin bayanan da zai rika zubawa a ciki, da irin kalmomin da zai rika amfani da su, don komai na iya faruwa a kowane lokaci. Allah mana jagora, amin.
Friday

IDAN AN MATSAMIN IN YI JIMA'I FA? DAKATA KAYI TUNANI !!!!!
To ka Dakata ka yi tunani tukunna!
Gaskiyar: Ba kowa ba ne yake yi.
Hakika, kila ka karanta game da yawan mutanen da suke yi. Alal misali, wani bincike da aka yi a Amirka ya nuna cewa a lokacin da matasa suka gama makarantar sakandare, matasa 2 cikin 3 a kasar sun riga sun yi nisa wajen yin jima’i. Amma kuma hakan yana nufin cewa 1 cikin 3—ba sa yin haka kuma wannan adadi ne mai yawa.
Wadanda suke yi fa? Masu bincike sun gano cewa yawancin irin matasan nan suna fuskantar irin wadannan halaye.
Bakin ciki. Yawancin matasa da suka yi jima’i kafin aure sun ce sun yi da-na-sani daga baya.
Rashin Aminci.
Bayan sun yi jima’in, su biyun za su soma tunani, ‘to wa ya sani ko da wa kuma ya ko ta taba yin jima’i?’
Bacin rai. A cikin zukatansu, ’yammata da yawa sun fi son wanda zai kāre su, ba wanda zai yi lalata da su ba. Kuma samari da yawa ba sa son yarinyar da suka riga suka kwana da ita.
Gaskiyar Al’amari: Jikinki da mutunci yake, kada ki zub da mutuncinki ta wajen bayar da jikinki. Ki nuna cewa kina da dabi’a sosai ta bin dokokin Allah game da guje wa yin jima’i kafin aure. Ranar da ki ka yi aure za ki iya yin jima’i. Kuma a lokacin za ki more shi sosai—ba tare da wani damuwa, bacin rai, da kuma rashin amincewa da ke tattare da yin jima’i kafin aure ba.
Wednesday

INA MASU SHANYA KAYA A DAKI KO A INDA BA RANA, to ku biyomu kusha labari........
– Domin kuwa wani sabon ilimin da aka samu yin hakan yakan janyo ma mutum wani babban matsala musamman idan mutum yana da matsalar shanyewar jiki kokuma asma
A kwanakin bayane dai aka samu wani mutum a garin Boston ya kamu da matsalar sassan numfashin jikinsa sun lalace sakamakon kayan da yake shanyawa a cikin daki ko wani wajen da babu rana.
Craig mather wanda dan shekara 34 ne da haihuwa an dai bayyana cewar yana da Pulmonary Aspergillosis, inda likitan ya rubutamasa maganin nan mai suna Antimicrobial inda yace nan bada dadewa ba zai samu lafiya .
Inda likitan ya kara bashi shawaran daya daina shanya kayan sawan sa a cikin gidan sa , Craig y dauki shawaran likitan kasan cewar yana da yara uku, kuma yana son yaga girman yaran . Bayan shekara guda sai Craig ya tabbatar da ya samu lafiya sosa bayan dayabi shawarar likitan nashi .
An dai bayyana abun ne da cewar busassun kayan suna komawa ne cikin dakin kwanan mutum inda suke komawa jikin dan Adam daga baya , haka kuma masu matsalar asma da kuma matsalar numfashi suna saurin kamuw da irin wannan matsalar ta shanyan kaya a cikin daki .
Haka ma mutanen da suke da cutar HIV ko kuma wa ’ anda akayi musu Kemo suma duk zasu iya kamuwa da wannan cutar ta Pulmonary Aspergillosis. Wannan cutar yanada saukin kama mutum kuma nan da nan yake batama mutum hanyoyin numfashin jikin sa .
Sunday

ILLOLIN ZINA
( ILLOLIN ZINA )
YANA DAGA CIKIN ILLOLIN DA ZINA TAKE
HAIFARWA TUN ANAN DUNIYA....
1-RUSHEWAR TATTALIN ARZIKI: annabi (saw)
ya bayyana acikin hadisi cewa dukkan
society da suka ta‘allaQa da aikata al-fasha
Allah madaukaki yana dankwafar dasu ta
fiskan tattalin arziki dss,
2-GUSHEWAR KUNYA: annabi (saw) yace da
imani da kunya dan-juma ne da dan-jummai,
muddin 1 ya tafe to 1n ma baya zama,
3-YA‘DUWAR ANNOBA / CUTUTTKA: annabi
(saw) yace zina bazata bayyana ba (kowa
yana aikatawa ba shuwagabanni da
mabiya ) face sai Allah me girma da daukaka
ya sauQar wada mutane annoba / cututtuka,
Dan-uwa ka dubi yanda HIV/ AIDS yake
kashe mutanenmu, Allah ya kyauta,
4-MUDDIN KAYI SAI WANI YAYIWA NAKA:
annabi (saw) yace ita zina BASHI ce, inkayi
sai an maka,
Duk wanda yayi zina da “yar-wani ko uwar-
wani ko yayar-wani, to shakka babu sai anyi
da nashi akwan atashi
Allah sarki hakan ya faru a yankin mu
Wani mutum ya kasance me tsanani wa
yarsa (mace) kasancewar ta girma ya hanata
fita koda makaranta ne, kullun haka---
Rannan saiga “ya“ da ciki,
Karshe yasa mata wuQa awuya kota fa‘da
wanda yayi mata ko ya yanka ta,
Qarshe tace - ina wannan Qawarta me zuwa
yau-da kullum akace ‘ei‘ tace ba mace bace
namiji ne,
Kaga illan zina kenan
5-GUSHEWAR MUTUNCI/KIMA ACIKIN JAMA‘A:
ka kula duk wanda yake zina to Allah saiya
cire masa kima da kwarjini acikin jama‘a
zakaga bashi da kima acikin mutane.
6-MUTUWA BA IMANI: annabi yace duk me
aikata zina al-fahsha to Allah ze zare imani
daga gareshi Qarshe ya mutu ba imani
Annabi yace duk wanda yayi zina da matan
aure- to Allah ze kwashe dukkan aiyukansa
na al-khairi yabawa mijinta
Aranar tashin al-Qiyama kuma Allah ze masa
azabar rabin wannan al-ummah ita matar
ma haka.
Innalillahi wa‘inna ilaihir-raju‘un !!
Annabi yace babu laifi da Allah yafi kyama
sama da mutum ya saka AL-AURANSHI A CKIN
FARJIN HARAM !!
Dan-uwa na ka sani aduniya dayan shirka
wa Allah da kisan kai babu laifi dayafi Qirma
sama da zina !!
Allah ka mana katangar Qarfe da aikata zina
Friday

SAKO DAGA SHAIDAN ! !! !!! !!!! !!!!!

GARABASA TUN A GIDAN DUNIYA
Wata rana Imamu Ahmad bin hambalI yayi tafiya
zuwa wani gari...
Inda ya tsinci kansha CIKAKKEN BAKO..
Duk da cewa sunan shi ya bazu a duniya; sai dai
ba kowa ba ne ya sanshi a fuska..
Saboda a wancan lokacin babu hoto..
Saboda haka ya sauka a wani masallaci...
Da dare yayi mutane suka watse, sai wani daga
cikin masu gadin masallacin ya nemi ya fitar
dashi..
Saboda dokar su ta hana kwana a masallaci...Sai
Imam Ahmad ya fito ya zauna bakin kofa...Mai
gadin nan ya Kara biyo shi yace lallai sai ya
tashi...
Da yaga imam ahmad zai bata mashi Lokaci, sai
ya kama kafarshi ya jawo shi har bakin hanya...
Dadai wurin da ya ajiye shi Akwai shagon wani
dattijo yana gasa gurasa...
Sai ya tausaya ma wannan bakon, ya bashi wuri
a shagon shi ya kwana...
Shi kuma ya cigaba da aikinshi, yana kwaba
filawa amma kuma bakin shi yana anbaton Allah:
*SUBHANALLAH
*WALHAMDU LIL LAH
*LAA. ILAHA ILLALLAH
*ALLAHU AKBAR
Haka ya cigaba har gari ya waye..
Imam Ahmad yayi mamaki, sai ya tambaye shi:
��Tun yaushe kake wannan azkar?
��Tun ina matashi na saba ma baki na da
anbaton Allah, sai Allah ya sauqaqa min Shi
kamar yadda nake numfashi..
��sai Imam Ahmad yace. To wane fa'ida ka
samu albarkacin wannan kyakkyawa aiki...
��babu abinda zan roki Allah ya hana ni..!
��yanzu duk abinda ka roki Allah ya baka!?
��kwarai kuwa, sai dai abu guda daya...
��sai Imam Ahmad yace menene shi?
��sai yace na roki Allah ya nuna min Ahmad
bin Hanbal, amma har yanzu ban amsa min
ba...ALLAHU AKBAR.........
Da imam Ahmad ya ji haka sai yace:
ALLAHU AKBAR, yau gashi Allah ya kawo ma
Ahmad har shagon ka ana janshi a kasa...
Ya Dan Uwa na Ban San wata falala da zaka
samu ba idan ka yawaita zikiri kuma ka tura
wannan sako ga abokai da yan uwa
Amma dai nasan annabi yace:
Wanda yayi nuni zuwa ga wani aikin alheri, yana
da kwatankwacin ladan Allah ya bamu ikon yin
aiki da umurni da aikin alkhairi Ameen





