Saturday

Home › › Buhari ba zai watsa ma 'yan Najeriya kasa a ido - Orji Kalu
A jiya ne tsohon gwamnan Jihar Abia, Dakta
Orji Uzor Kalu, ya ce ya tabbata Shugaba
Buhari zai kai 'yan Najeriya birnin dadi. Don
haka ne ya yi kira ga daukacin 'yan Najeriya
da su mara ma sa baya don kai ga ci.

Kalu ya bayyana hakan ne ga manema
labarai a wurin wata jana'iza da ya halarta.
Ya ce jama'a su kan manta da sashin ayyuka
na badini, na bin doka da kuma gudanar da
lamurra yadda ya kamata, wanda sai da shi
ne ayyukan zahiri su ke tabbata.

A cewar sa, jama'a ba su fahimtar cigaban da
a ke samu ne saboda sun saba da ci a zaune,
a na dauko kudi a na basu kyauta. A yanzun
kuwa an samu cigaban da matasa tsaye su ke
su na neman na kan su. Sun dukufa da noma
da kiwo da sana'o'i daban daban.
Game da maganar yiwa kasa garabbawul da
canja salon tsarin mulki kuwa, ya ce ba wani
abun tayar da jijiyan wuya ba ne. Abun da a
ke cewa shi ne Gwamnatin Jihohi su dauke
wasu nauyin da ya rayata a kan Gwamnatin
Tarayya. A cewar sa, ko Buhari ya yi magana
a kan hakan.

Kalu wanda hamshakin dan kasuwa ne, ya ce
sam Najeriya ba ta kai ga fita daga kuncin
tattalin arziki ba, wata kila dai za ta fita a
watan Disamba na 2018 sakamakon aiki
tukuru da a ke yi don bunkasa tattalin arziki.
No comments:
Write Comments