Biyo bayan kisan wani hafsan soja mai mukamin Laftanar a rundunan mayakan sojan kasa a ranar 15 ga watan Maris, wani abokinsa ya bayyana hirar da suka yi da shin a karshe.
Hafsan soja marigayi Oguntoye
Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewa mayakan Boko Haram sun hallaka wani hafsan soja mai suna Laftanar Akinwale Christopher Oguntoye a wani harin da suka kai a kauyen Magumeri na jihar Borno ranar 15 ga watan Maris.
Bayan mutuwar tasa sai wani abokinsa mai suna Empire Okorie ya bayyana hirar su ta karshe da sojan.
Abokin nasa yace: “Ban ma san ta inda zan fara jimami ba, musamman yadda abokinmu ya sadaukar da rayuwarsa ga Najeriya, abokina nane na kud da kud, har yanzu ina cikin dimuwa. Allah ya jikanka.”
Ga hoton Yadda hirar tasu ta kasance:
An kashe laftanar Oguntoye ne yayin da suke kan hanyar su ta dawowa daga filin atisayen hari a garin Monguno.
KARANTA WANNAN:- "Dolene Fa Buhari Ya Mike Tsaye" : inji el-rufa'i
No comments:
Write Comments