Hukumar tayi barazanar cewa za'a ga ba
daidai idan har wani abu ya sami shugaban
hukumar ta EFCC. Yan bindigan sun kai hari ne a gidan Magu da ke unguwar Karchi da ke βirnin tarayya Abuja inda suka kashe jami'in dan sanda da ke gadi a gidan.
“
A sanarwan da shugaban kungiyar Farfesa
Ishaq Akintola ya bayar, yayi bayani cewa
babu shakka wasu daga cikin barayin
dukiyar kasa ne da Magu ke bincika suke
kokarin halaka shi domin sun san cewa shi
mutum ne mai gaskiya da jarumtaka wajen
aikin sa.
Ya kara da cewa dole ne gwamnatin tarayya
tayi duk mai yiwuwa domin kare lafiyar
Magu da na iyalansa domin yaki da rashawar da yakeyi zata amfani zuri'ar mu da zasu nan gaba.
Farfesa yace idan aka bari miyagun mutane
sukayi nasarar kashe Magu, duk wani wanda
zai zo bayan sa ba zai iya gudanar da aikin sa cikin rashin tsoro da adalci ba idan har ya san gwamnatin Najeriya ba za ta iya bashikariya ba.
Post By : Vast Media
No comments:
Write Comments