Wani jawabin da Manajan hukumar FAAN , Mrs Henrietta Yakubu, ta saki yau Alhamis, ta bayyana cewa jirgin ya fita daga kan hanya yayinda take kokarin sauka kuma ta makale a kan hanya. Henrietta Yakubu ta bayyana cewa an bude filin jirgin domin sufuri bayan rage titin gudu zuwa mita 3000.
Ta bada tabbacin cewa jirage da fasinjoji su koma sufuri kamar yadda ya kamata. NAIJ.com ta kawo muku rahoton cewa An kulle babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe International Airport, da ke birnin tarayya Abuja bayan wata jirgin sama ta toshe hanyar wucewar jirgi. Wanna abu ya faru ne misalin karfe 10 na daren jiya Laraba.
Majiya mai karfi sun bayyanawa jaridar Daily Nigerian cewa jirgin kira 5N BOD Gulfstream na tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff ne.
Thursday
WELCOME TO AREWASOUND
VISIT OUR NEW BLOG
- - Latest Hausa song
- - Newest Android games
- - Useful Android Apps
- - Hausa Novels
- - Health Tips
- - How to make money online 2019
AREWASOUND.COM>>> Is Your Best Solution.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Write Comments