QISSAR HARUTA DA MARUTA
.
Asalin tsafi.
.
Shin Mala'iku Ne Su Ka Koyar da Tsafi?
.
Daga Cibiyar Tarbiyyah Islamiyyah, Masu Yin Ruq'yah Da Harhada Magungunan Musulunci. Lambar waya 08162600700.
.
Allah Madaukakin Sarki Ya ambaci sunayen Haruta da Maruta sau daya a cikin Alqur'ani mai girma, acikin Suratul Baqarah.
.
Ruwayoyi da dama sun zo akan Qissar wadannan sunaye na Mala'iku ko kuma Sarakuna amma dai za mu dauki jigon ruwayar da Ahmad ya fitar acikin Musnad, da kuma ibnu Hibban aciki Sahihinsa daga ibn Umar رضي الله عنهما
sai mu shigar da bayanin sauran ruwayoyin a ciki.
.
.
Ga cikakkiyar Qissar :
.
Lokacin da Allah Madaukakin Sarki Ya saukar da Annabi Adam ﻋﻠﻴﻪ السلام
daga Aljanna zuwa kasan duniya, sai Mala'iku suka dinga cewa "Ya Ubangiji, yanzu ka sanya wadanda za suy 6arna su dinga zubar da jinin junansu a duniya?!, alhali mu muna girmamaKa tare da gode maKa kuma muna kaskantar da kai a gareKa?".
.
Sai Allah Ya ce "Ni Na san abinda baku sani ba".
.
Sai su ka ce "Ya Ubangiji mu fa mun fi yi maKa biyayya sama da 'yanAdam, inda mu ne ka saukar da mu duniya to ba za mu sa6a maka ba".
.
Sai Allah Ya ce musu "To ku kawo Mala'iku guda biyu a cikinku. Sai Mu saukar da su kasan duniya, don Mu ga yadda za su yi. (za suy biyayya ko ba za suy ba?!)".
.
Sai suka ce "Ya Ubangiji Ga Haruta da Maruta mun za6e su a kaisu"
.
Sai aka saukar da wadannan Mala'iku biyu zuwa duniya, aka sauke su a garin Babila.
.
Lokacin da aka sauke su sai aka ce musu ga Tsafi nan ku dinga koyawa mutane amma duk wanda ya zo zai koya ku gaya masa in ya aikata ya zama kafuri.
.
A wata ruwayar kuma an ba su Sihiri ne domin su dinga yiwa mutane gargadi akan su guje shi kada su aikata shi.
.
To bayan an saukar da su sai Allah Ya mayar da Zahr', wato wannan babbar tauraruwar da muke gani a kuma da wata, sai aka mayar da ita siffar mace.
.
Sai ta zo wajensu a sura kyakkyawa.
.
Da su ka ganta sai su ka nemeta. Sai ta qi amincewa ta ce musu "Saidai in za ku kafurta to zan yarda da ku".
.
Da su ka ji haka sai su ka ce basu yarda ba.
.
Sai ta fi, ta sake dawowa da wani jariri a hannunta. Sai su ka kuma nemarta. Sai ta qi amincewa, ta ce "Saidai in za ku kashe wanan yaron, to zan ba ku hadin kai".
.
Sai su ka ce basu yarda ba. Sai ta tafi, ta sake dawowa da tukunyar giya a hannunta.
.
Suka nemeta. Sai ta ce bata yarda ba sedai in za su sha giya tukuna. Sai su ka yarda su ka sha giyar.
.
Bayan sun sha sai maye ya kama su, su kay zina da wannan matar sannan kuma suka kashe wannan jaririn.
.
.
Lokacin da suka farka sai Allah Ya tambayesu alqawarin da sukay akan ba za su sa6a masa ba.
.
Daga nan sai aka ba su za6i akan su za6i irin azabar da za ay musu. Shin a duniya suke so ay musu azaba ko kuma a bari sai an je Lahira?!.
.
Sai suka ce ai azabar Lahira bata karewa, mun za6i ta duniya.
.
Shikenan sai aka kai daya inda rana take 6ullowa. Kullum idan rana ta 6ullo sai ta tafasa masa kansa.
.
Dayan kuma sai aka kaishi inda rana take faduwa, kullum in rana zata fadi sai ta kona shi.
.
Ita kuma Zahra' sai aka mayar da ita tauraruwa ta koma sama.
.
.
To a lokacin ne aka ba su sihiri, (bisa sa6anin ruwaya).
.
Sai aka ce duk wanda ya zo yana so su koya masa.
.
Sai suka dinga koyawa mutane da Aljanu yadda ake raba tsakanin miji da mata amma basa koyawa kowa sai sun ce masa "Tabbas mu fitina ne!, don haka kada ka kafurta".
.
In Mutum ko Aljan ya yarda zai kafurta sai su koya masa.
.
Daga nan sai harkar Sihiri da tsafi ta yadu a tsakanin mutane da Aljanu.
.
.
Malamai sun yi raddi sosai akan wannan qissa musamman kasancewar Mala'iku basa sa6o da kuma maganar cewa su ne suka koyar da tsafi sannan ruwayoyin yawanci Isra'iyliyyat ne, sedai abinda aka samu na 6angarorin qissar daga Alqur'ani da kuma ruwayar ibnu Umar daga Manzon Allah صلى الله عليه وسلم
kamar yadda muka ambata.
.
Harkar Bokanci, Sihiri, Tsafi, Surkulle, Rufa-ido, Tsibbace-tsibbace da makamantansu, sun samu shahara sosai da kar6uwa a wajejen aiko Annabi Sulaiman عليه السلام
shi yasa ya zamto yana daga cikin manyan abubuwan da Annabi Sulaiman yay fada da su kuma ya yaqi masu aikata shi.
.
Sannan wannan harka ta samu kar6uwa ne da matsayi da shiga zukatan al'umma a wajenjen zamanin Annabi Musa عليه السلام،
inda a lokacin ake ganin wanda ya iya sihiri tamkar wani shugaba kuma wani abin ay wa biyayya sannan abin tsoro.
.
Za mu kawo cikakkiyar qissar yadda Annabi Sulaiman عليه السلام ya yaqi masihirtan zamaninsa da kuma dalilin da yasa bayan ya yi wafati Shaidanu suka ce ya mulki duniya ne ta hanyar tsafi.
.
Sannan za mu sake duba qissar Haruta da Maruta tare da bayanin yadda Annabi Musa ya fuskanci matsafan zamaninsa.
.
Duk wannan zai zo insha Allahu a cikin posting din mu mai taken "ASALIN TSAFI", Domin Allah Madaukakin Sarki Ya fada acikin Suratuz Zariyari cewa:
.
ﻓَﻔِﺮُّﻭﺍ ﺇِﻟَﻰ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺇِﻧِّﻲ ﻟَﻜُﻢْ ﻣِﻨْﻪُ ﻧَﺬِﻳﺮٌ ﻣُﺒِﻴﻦٌ * ﻭَﻻ ﺗَﺠْﻌَﻠُﻮﺍ ﻣَﻊَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺇِﻟَﻬﺎً ﺁﺧَﺮَ ﺇِﻧِّﻲ ﻟَﻜُﻢْ ﻣِﻨْﻪُ ﻧَﺬِﻳﺮٌ ﻣُﺒِﻴﻦٌ * ﻛَﺬَﻟِﻚَ ﻣَﺎ ﺃَﺗَﻰ ﺍﻟَّﺬِﻳﻦَ ﻣِﻦْ ﻗَﺒْﻠِﻬِﻢْ ﻣِﻦْ ﺭَﺳُﻮﻝٍ ﺇِﻻَّ ﻗَﺎﻟُﻮﺍ ﺳَﺎﺣِﺮٌ ﺃَﻭْ ﻣَﺠْﻨُﻮﻥٌ [ ﺍﻟﺬﺭﻳﺎﺕ :50 - 52] .
.
.
Ma'ana: "Kamar haka ne (Su wadannan mutanen) babu wani Annabi da ya zo wajen wadanda suka gabace su face sai sun ce masa mai Sihiri ko kuma mai hauka".
.
Wannan ayah tana nuna cewa tun zamanin Annabi Nuhu ﻋﻠيﻪ ﺍﻟﺴﻼﻡ
duk da cewa shi ne farkon Manzanni, duk Annabin da Allah Ya aiko sai Kafurai sun ce masa mai sihiri ne. Kenan tun a lokacin ana yin sihiri.
.
Wasu Malaman kuma suna ganin sihiri ya samo asali ne daga hannun Aljanu kuma dalilansu sun fi karfi gaskiya.
.
Insha Allahu za mu kawo cikakken bayani a cikin "ASALIN TSAFI", wannan bayani zai zo nan gaba kadan da yaddar Allah.
.
Daga shafin Bashir Halilu Tarbiyyah Islamiyya.
Lambar waya 08162600700, 08134434846.

No comments:
Write Comments