Saturday

Home Dalilan da yasa kotu ta yi gaggawar dakatar da Ganduje
A jiya Juma'a ne wata Kotun Koli a jihar Kano da ke unguwar Ungogo ta dakatar da gwamnan jihar Dr. Abdullahi Umar Ganduje daga daukar matakin raba masarautar jihar zuwa gida biyar.
image© legit.ng

Masarautun da gwamnan zai kara guda hudu sun hada da Masarautar Rano, Masarautar Bichi, Masarautar Gaya da kuma Masarautar Karaye.

Umarnin kotun ya biyo bayan karar da Rabi'u Sule Gwarzo ya kai inda yake kalubalantar gwamnan jihar akan yunkurin shi na kirkiro sababbin masarautu hudu a jihar.

Alkalin kotun, mai shari'a Nasiru Saminu, ya ba da umarni ga dukkanin masu hannu a lamarin akan su saurara domin a tabbatar da yiwuwar hakan.

Bayan haka kuma, mai shari'a Saminu, ya ba da umarni ga gwamnan jihar da kuma masu buga takardu na gwamnati akan su dakata da wallafa dukkanin takardu da suke da alaka da sababbin masarautun.
Mai gabatar da karar shi ne Rabiu Sule Gwarzo, yayin da kakakin majalisar jihar ya ke kalubalantar karar.

KU KARANTA: Bidiyo : Gwamnan Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje Yayin Tabbatar da Nadin sarakunan Yanka.  A yau Asabar

Bugu da kari, majalisar dokokin Kano ita ce mai kalubalantar kara ta biyu, sai gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje a matsayin na uku da zai kalubalanci karar, alkalin alkalan jihar kuma kwamishinan shari'a na jihar shine na hudu da zai kalubalanci karar sai kuma masu wallafa takardu na gidan gwamnatin Kano a matsayin na biyar.

Alkalin kotun ya bayyana ranar Laraba 15 ga watan Mayu a matsayin ranar da za a cigaba da sauraron karar da kuma albarkacin bakin jama'a.
MAJIYA LEGIT.NG
No comments:
Write Comments