Monday

Home Rikicin masarauta a Kano: Hakimin Bebeji yayi murabus.
Haruna Sanusi, Hakimin karamar hukumar Bebeji da ke jihar Kano yayi murabus daga mukaminsa, bisa dalili na rashin lafiya da kuma sauyin tsarin masarauta da aka samu kwanan nan.
Ganduje Ans Sunusi

Hakimin garin, wanda ke rike da mukamin Dan Galadiman Kano, ya sanar da murabus dinsa a wata wasika zuwa ga Sakataren gwamnati, mai kwanan wata 10 ga watan Mayu.

Gwamnan jihar Kano, a ranar 8 ga watan Mayu ya samar da sabbin masarautu hudu da manyan sarakuna a jihar, inda aka yi zargin cewa yana so ya karya darajar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ne.

Legit.ng ta rahoto cewa Sarakunan da aka nada sune; Aminu Ado-Bayero, Bichi; Tafida Ila, Rano; Ibrahim Abdulkadir, Gaya da kuma; Ibrahim Abubakar ll, Karaye.

KU KARANTA KUMA: Dalilan da yasa kotu ta yi gaggawar dakatar da Ganduje   

A ranar Juma’a, wata babbar kotun jihar Kano da ke zama a Ungogo ta yi umurnin hana gwamnan kacaccala masarautar.
Amma a ranar Asabar sai gashi gwamnan ya gabatar da wasikun nadi ga sabbin sarakunan, cewa bashi da masaniya akan umurnin kotun.

SOURCE LEGIT.NG



No comments:
Write Comments