Tuesday

Home Tirkashi : Dogaran Sarkin Kano sun fara gudu daga fadar Kano
Zirga-zirga ta ragu a fadar Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, bayan kaddamar da sababbin masarautun yanka guda hudu da gwamna Ganduje ya yi wanda suka hada da Bichi, Rano, Karaye da kuma Gaya.

Ranar Lahadin da ta gabata fadar a cike take da al'umma a lokacin da sarkin ya dawo daga aikin Umrah, inda dubunnan mutane suka fito suna yi mishi barka da zuwa a filin tashi da saukar jiragen sama na Malam Aminu Kano.


KU KARANTA: Abinda yasa Ganduje bai tsige sarki Sanusi II ba - Majiyar gwamnatin Kano. 

Mutanen sun biyo shi har zuwa fadar shi daga filin jirgin, inda suke yi mishi kirarin "mai martaba sarki"

Mun samu labarin cewa a yau Talatar nan zirga-zirga ta ragu sosai a fadar, duk yawan zirga-zirgar da aka saba gani a fadar ta mutane da ababen hawa komai ya ragu.
Mutane kalilan ne suka rage a fadar sai ma'aikatan fadar.

Wani Dogari wanda ya yi magana da manema labarai ya bukaci a boye sunansa, ya tabbatar da cewar sarkin ya zabi ya kadaice kanshi tun dawowar shi daga kasa mai tsarki.
Ya ce: "Tun dawowar Mai Martaba, bai sake magana ba. Ya samu ganin baki kalilan ne da suke zuwa ziyartar shi. Manema labarai da yawa sun zo domin yin hira da shi amma ya hana kowa ganinshi.

KU KARANTA: Sabbin sarakuna: Mu na tare da masarautar Kano, al'ummar Wudil sun bijirewa Ganduje. 

"Wannan kirkiro sabbin masarautu ya shafi yawaitar zirga-zirga a fadar nan, kuma ina mai tabbatar muku cewa Mai Martaba bai ji dadin abinda ya faru ba."

A cewar shi, Dogarai da yawa da suke fadar Sarkin Kanon sun bar fadar zuwa sauran masarautun da aka kirkira, musamman ma masarautar Bichi inda dan gidan Marigayi Ado Bayero ke Mulka.

news SOURCE By LEGIT. NG
No comments:
Write Comments