Showing posts with label Nishadi. Show all posts
Showing posts with label Nishadi. Show all posts

Tuesday

Wasan Sallah! Wasan Sallah | S.I Media And Ict Services hadin Gwiwa da SHOPRITE.

S.I. MEDIA AND ICT SERVICES da Hadin Gwiwar SHOPRITE sun Shirya Wasan Sallah don bawa Mawaka da Jarumai da Comedians damar gabatar da wakokinsu a gaban Dubunnan Masoyansu cikin bukukuwan Sallah da hakan zai basu damar a kara sanin su.

Sannan bayan taron akwai hirar awa 1 a gidan Radio ga duk Wanda ya Shiga wannan wasan Sallah.

Akwai Form da za'a siya akan N2,000.

KARIN ARMASHI:
Za'ai wannan wasa tareda Fitattun "YAN FILM Kamar: Ali Nuhu, Adam Zango, Maryam Yahaya, Baba Ari, Daushe, Bosho, " "Yar Auta, Hadiza Gabon, Amina Amal, Kaura Entertainment, Dorayi Entertainment da sauransu.

MAWAKA na Hausa, Turanci, Hip Hop da Nanaye Kamar: Umar M. Sharif, Nura M. Inuwa, Whizkid, Hamisu Breaker, Maryam Fantimoti, Malik Fresh, BOC, DJ AB, Kebbi Art, Murja Baba, Naja'atu Ta'annabi da sauransu

MANUFA:
Hada alaka ta musamman da Kananan Mawaka da Jarumai Mawaka har Jarumai Masu tasowa, Kuma akwai damar ganin " yan Jaridu daga Kafofin Yada Labarai na gida Dana Waje da suma zasu nuna yadda suke aiki.

ABIN LURA
Munada adadin Mutanen da Mukeso don haka a gaggauta siyan Form don muna samun adadin mutanen zamu siyar.

ZA'A GABATAR KAMAR HAKA:⤵⤵

RANA: Cikin Bukukuwan Sallah

WURI: SHOPRITE, KANO.

LOKACI: Karfe 12 na Rana zuwa 9 na Daren Kowacce Rana.

NEWS SONG : Rarara ft Gwanja - Ganduje a Next Level - Kubar Tsula a O'level Mp3.

Don Siyan Form ko Karin Bayani a kira: ArewaBlog 08148337698

SAI MUN JIKU

NB: Don Allah a yada don bawa Kananan Mawaka da Jarumanmu damar Shiga wannan gagarumin SHOW!.

Saturday

Mu sha Dariya: Labarin Lado da Tanko Dariya Dole

Mu sha Dariya: Labarin Lado da Tanko Dariya Dole.



LADO yana zaune, a kusa da Abokin sa TANKO. Sai LADO yace:- Kai duniya ana abubuwan mamaki. .
Sai TANKO yace:- Me kuma ya faru...?

 Sai LADO yace:- Wai ina zaune,kusa da wata kwata, saiga wata Mata mai ciki tazo zata tsallaka.

Sai naji dan cikin nata na cewa:- Ina kwana Baba...! Sai Matar nan ta lura, sai tace mun, kana kamada Babansa shiyasa ya gaidakai.... 

Sai shima TANKO yace:- Mhmmm... Yo wannan har abun mamaki ne...?

 Nida aka yima abunda na kusa zaucewa. .

 Sai LADO yace:- Wane abune...?

 Sai TANKO yace:- Wai tun daga Kaduna direban motar mu ya rasu, amma bamu saniba, sai da mukazo Kano... Mun je gidan mai, anan aka tambayeshi na nawa za'azuba...?

 Sai aka ga ashema Direban ya rasu, harma ya tsandare...!

 Sai LADO Yace, Wallahi karyane dan Ubanka!!! 

Sunday

Mp3 Music : Audio Gwanja Ft Danko X Chizo X Oli X Sisqo -Zance.

Music : Gwanja Ft Danko X Chizo X Oli X Sisqo -Zance. 

Umar m shariff, ado gwanja,  nazir sarkin waka,  Music : Audio Gwanja Ft Danko X Chizo X Oli X Sisqo -Zance.

              Audio Gwanja Ft Danko X Chizo X Oli X Sisqo -Zance.


Sabuwar wakar Su Ado Gwanja Tare Da Husaini Danko da Haruna Chizo Da Bello Sisqo Da Oli mai aringizo a cikin wakarsu mai suna ” Zance ” wakar ta hada wannan manyan mawakan domin nuna ranar da waka tayi musu.
GA KADAN DAGA BAITIN WAKAR:-
– Adamu gwanjane na mai dawayya
– Nida husaini danko zantukan ba karya
– Da bello sisqo da small mai gashi da oli mai gwano kunji zance na
– Ban raina kowaba karda a rainani

SOURCE : ©®@Arewablog


– Ban zagi kowaba karda ku zageni
– Innai abun gani karda kuki nuna ni
– Waka nake gareni taimin amani
– Takaini inda Allahu ya mikani.

                DOWNLOAD AUDIO NOW

Thursday

Videon : - Yaron Da Yace Gwara Adam A Zango Da “Baba Buhari”

Wannan Wani Yaro Ne Da Yake Son “Adam A Zango” Kamar Yayansa Na Ciki Daya. idan Ku ka Kalli Wannan Video, Za kuji Yaron Ya Fiye Zumudi So Sai Kamar Ace Zango Ne Ubansa.
©pressloaded Yaron Ya Fadi hakan Da Bakinsa Ya Ce, Ganin Adam Zango Yafi Ganin “Baba Buhari” Domin Shi A Gurinsa Baiga Amfanin “Baba Buharin Ba”. Ya Kuma Kara Da Cewa Allah yasa Yaga Zango Koda Sau Dayane, Click Below Here Yo Download This Video And watch After Downloading….
DOWNLOAD VIDEO

LABARIN WANI KURMA DA BIRAI A GONAR ROGO.



A kwai wani kurma Bahadeje da ke da wata babbar garkar rogo a cikin kauyen su duk da irin karfin da Allah ya hore ma wannan kurma amma wasu mabannatan birai sun hana shi sakat ta hanyar zuwa suna tugar masa rogo suci su koshi sannan su kama jefe-jefen junansu da rogon har sai sun gaji sannan suyi tafiyar su, kurma yayi hakon, yayi tarkon yayi shigar burtun, yayi badda bami ga biran nan amma duk a banza kullum tamkar yana zuga su.

kuma shi wannan kurman yana jii amma ba sosai ba.

Rannan sai wata dubara ta fado ma wannan kurma ya tafi wani dakin sayar da maganin asibiti [chemist] ya sawo maganin sa barci watau baliyan mai yawan gaske ya wuce gida ya dauko kwatarniya ya hau kekensa ya nufi gona abinshi,zuwansa ke da wuya ya samu gindin wata dorawa ya gina rami yasa wannan kwatarniya ya gangara rafi ya debo ruwa ya cika wannan kwatarniya sannan ya dakko kunshin baliyan din shi ya zuba cikin ruwa ya dame sannan ya dauki keken shi yakai saman wata bishiyar tsamiya mai duhuwa ya hau ya daure sannan shima ya buya a saman wannan bishiya.

Jim kadan sai ko ga garken biran nan sun yo ayari ba tare da wani asha-ruwan-tsuntsaye ba suka fada cikin garkar rogon kurma su ka tuga,su ka ci,su ka koshi suna shirin su gangara rafi su sha ruwa su dawo su shiga wasan jifa sai guda ya tsunkayi wannan kwatarniya da kurma ya aje gidin dorawa sai yayi ma sauran inkiya su zo su taya shi kwasar arha gasassa.

Bayan birai sun sha ruwa sun yi tatul sun komo wasan jifa sai baliyan ta fara tambayar su, sai biri ya dauko rogo zai jefi dan uwanshi sai layi ya kama shi sai rogo ya kubce.

Kurma na saman tsamiya yana kallon ikon Allah sai da ya bari sunyi mankas sannan ya fara kwance kekensa ya fado tim cikin garka ko da birai suka ji karar fadowar keken kurma daga kan tsamiya sai suka tsorata su ka ce kafa me naci ban baki ba?kafa tace babu har baliyan kun bani ma'ana sai biri yayi yunkurin tsalle sai ya tuntsure kasa kurma kuwa baiyi wata-wata ba ya sakko ya kwashi guda shidda ya dora ya daure da danko a bayan keken shi yakai gida ya zuba a wani daki ya kulle ya dawo ya kara har sau hudu, kan hanya duk wanda ya game da kurma da birai ya tambaya sai kurma yace ''yau zan farke rogo na wurin mai banna zai ci ubanshi''
Kurma yai guzurin bulalai ya kai dakin birai ya hada ya kulle a daki yace sai da safe ta sake su sannan su gane kuskuren su.

Da garin Allah ya waye tun da dugu-dugu sai kurma ya je dakin barai ya bude ya tarar kuwa lokacin baliyan ta sake su bai yi wata-wata ba ya damko guda ya maida daki ya rufe ya kai shi wani daki na dabam sannan yace dawa Allah ya hada shi ba da wannan biri ba ya shiga kora mashi bulala to da yake kurman yana dan ji sama-sama in ana magana da karfi duk lokacin da ya daki biri sai ya tsaya ya dube shi yayi wa biri dakuwa yace''kai uwakah bannah,bannah,bannah,bannah can garkah za ka karah''yana nuna wa birin hanyar garka da dan yatsan shi na nune in biri yaji duka sai yace ''af,af,af,af,af'' sai kurma yace ''af,af baka biyu ba zaka koma kenan'' sai yaci gaba da dukan biri har sai sa'ad da yaji birin kukan shi na cewa ''ah,ah,ah,ah'' sannan sai kurma yace ''shege yanzu ka biyu kenan'' sannan ya sake shi ya jawo wani.

Tun daga wannan rana kurma da mutanen gari suka huta barnar birai.