Thursday

Home LABARIN WANI KURMA DA BIRAI A GONAR ROGO.


A kwai wani kurma Bahadeje da ke da wata babbar garkar rogo a cikin kauyen su duk da irin karfin da Allah ya hore ma wannan kurma amma wasu mabannatan birai sun hana shi sakat ta hanyar zuwa suna tugar masa rogo suci su koshi sannan su kama jefe-jefen junansu da rogon har sai sun gaji sannan suyi tafiyar su, kurma yayi hakon, yayi tarkon yayi shigar burtun, yayi badda bami ga biran nan amma duk a banza kullum tamkar yana zuga su.

kuma shi wannan kurman yana jii amma ba sosai ba.

Rannan sai wata dubara ta fado ma wannan kurma ya tafi wani dakin sayar da maganin asibiti [chemist] ya sawo maganin sa barci watau baliyan mai yawan gaske ya wuce gida ya dauko kwatarniya ya hau kekensa ya nufi gona abinshi,zuwansa ke da wuya ya samu gindin wata dorawa ya gina rami yasa wannan kwatarniya ya gangara rafi ya debo ruwa ya cika wannan kwatarniya sannan ya dakko kunshin baliyan din shi ya zuba cikin ruwa ya dame sannan ya dauki keken shi yakai saman wata bishiyar tsamiya mai duhuwa ya hau ya daure sannan shima ya buya a saman wannan bishiya.

Jim kadan sai ko ga garken biran nan sun yo ayari ba tare da wani asha-ruwan-tsuntsaye ba suka fada cikin garkar rogon kurma su ka tuga,su ka ci,su ka koshi suna shirin su gangara rafi su sha ruwa su dawo su shiga wasan jifa sai guda ya tsunkayi wannan kwatarniya da kurma ya aje gidin dorawa sai yayi ma sauran inkiya su zo su taya shi kwasar arha gasassa.

Bayan birai sun sha ruwa sun yi tatul sun komo wasan jifa sai baliyan ta fara tambayar su, sai biri ya dauko rogo zai jefi dan uwanshi sai layi ya kama shi sai rogo ya kubce.

Kurma na saman tsamiya yana kallon ikon Allah sai da ya bari sunyi mankas sannan ya fara kwance kekensa ya fado tim cikin garka ko da birai suka ji karar fadowar keken kurma daga kan tsamiya sai suka tsorata su ka ce kafa me naci ban baki ba?kafa tace babu har baliyan kun bani ma'ana sai biri yayi yunkurin tsalle sai ya tuntsure kasa kurma kuwa baiyi wata-wata ba ya sakko ya kwashi guda shidda ya dora ya daure da danko a bayan keken shi yakai gida ya zuba a wani daki ya kulle ya dawo ya kara har sau hudu, kan hanya duk wanda ya game da kurma da birai ya tambaya sai kurma yace ''yau zan farke rogo na wurin mai banna zai ci ubanshi''
Kurma yai guzurin bulalai ya kai dakin birai ya hada ya kulle a daki yace sai da safe ta sake su sannan su gane kuskuren su.

Da garin Allah ya waye tun da dugu-dugu sai kurma ya je dakin barai ya bude ya tarar kuwa lokacin baliyan ta sake su bai yi wata-wata ba ya damko guda ya maida daki ya rufe ya kai shi wani daki na dabam sannan yace dawa Allah ya hada shi ba da wannan biri ba ya shiga kora mashi bulala to da yake kurman yana dan ji sama-sama in ana magana da karfi duk lokacin da ya daki biri sai ya tsaya ya dube shi yayi wa biri dakuwa yace''kai uwakah bannah,bannah,bannah,bannah can garkah za ka karah''yana nuna wa birin hanyar garka da dan yatsan shi na nune in biri yaji duka sai yace ''af,af,af,af,af'' sai kurma yace ''af,af baka biyu ba zaka koma kenan'' sai yaci gaba da dukan biri har sai sa'ad da yaji birin kukan shi na cewa ''ah,ah,ah,ah'' sannan sai kurma yace ''shege yanzu ka biyu kenan'' sannan ya sake shi ya jawo wani.

Tun daga wannan rana kurma da mutanen gari suka huta barnar birai.
No comments:
Write Comments