Showing posts with label exam. Show all posts
Showing posts with label exam. Show all posts

Tuesday

Sakamakon Jarrabawa: Hukumar JAMB ta yi karin haske

Kamar yadda jaridar Premium Times ya ruwaito, hukumar JAMB ta ce a kwana-kwanan nan za ta tura sakonnin tas ga dalibai masu neman shiga jami'o'i domin sanar da su a kan lokacin da za ta saki sakamakon jarrabawar bana da zarar ta kammala tantancewa.
Jamb 2019 result,  2019 Jamb result,  Jamb result 2019

Shugaban cibiyar sadarwa na hukumar, Dakta Fabian Benjamin, shi ne ya bayar da shaidar hakan cikin wata hira yayin ganawar sa da 'yan jarida na kamfanin dillancin labarai a ranar Lahadi cikin birnin Legas.

A cewar sa, Dakta Benjamin ya nemi dalibai da su kauracewa sauraron jita-jitar masu yada kanzon kurege da rade-radi marasa tushe a kan sakamakon jarrabawar bana musamman a kafofi da dandalan sada zumunta.

KARANTA KUMA: Yadda ake mayar da hakora suyi haske ƙal-ƙal a cikin awa daya  

Rahotanni sun bayyana cewa, fiye da dalibai miliyan 1.8 masu neman shiga jami'a a Najeriya sun zana jarrabawar JAMB ta bana cikin dukkanin jihohi da ke fadin kasar nan a tsakanin ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu zuwa ranar Laraba, 18 ga watan Afrilun 2019.

Hukumar JAMB bisa jagorancin Farfesa Ishaq Oloyede, ta yaba da salo, tsari da kuma yanayi na gudanar da jarrabawar bana da a cewar ta wannan karo ta tsarkaka daga ababe na magudi ko kuma kalubale sabanin yadda ta fuskanta a baya.


MAJIYA : LEGIT. NG

Yadda muka damke mutane sama da 50 dake rubutawa wasu jarabawar UTME : JAMB

Hukamar ta JAMB tace, ta samu nasarar damke mutum sama da hamsin wanda ke kiran kansu ‘kwararrun masu rubuta jarabawa’ wadanda suka shahara wajen rubutawa mutane jarabawa saboda a biyasu .
jamb malpractice, jamb result 2019

Fabian Benjamin, shugaban hukamar mai kula da sashen labarai ya rubuta wannan labari a shafinsu musamman na fitar da labarai mai taken ‘JAMBULLETIN’ a ranar Litinin. Manema labarai sun bayyana cewa sama da mutane miliyan daya da dubu dari takwas ne zasu rubuta wannan jarabawa ta UTME wacce aka fara tun ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu a fadin kasar nan.

KU KARANTA: Ana shan bakar wuya a mulkin Buhari - Fitacciyar jarumar fim.

Hukumar tace, tayi nasarar zakulo wata kungiyar dake da taken ‘kwararrun masu rubuta jarabawa’ wadanda suka shahara wurin rubuta jarabawar domin a biyasu. A sanarwar da suka fitar, bisa ga jajircewa da hukumarmu tayi ta hanyar amfani da bayanai na sirri mun samu damar cafke sama da mutane hamsin wanda ke tafka wannan ta’asa a cibiyoyin rubuta wannan jarabawar dake fadin kasar nan.

Mun sama damar fahimtar cewa, wasu daga cikin masu laifin suna da digiri na biyu wato ‘Masters’ kenan a turance inda kuma wasun su daliban jami’o’ine dake kasar nan.

 Zancen ya sake fayyace mana cewa su wadannan mutane sun hada kaine da masu wadannan cibiyoyi na zana jarabawar ta JAMB inda suke zuwa yayinda za’a dauki hoton yastun wanda yazo rejista domin rubuta jarabawar sai suma ayi amfani harda nasu.


“Lokacin da ake tuhumar masu laifin, jigo daga cikinsu ya shaida mana cewa suma din ana daukar hoton yatsun nasu ne tare da asalin masu zana wannan jarabawa tare da biyansu kudi masu tarin yawa.
“Wannan dalilin ne ya sanya hukumar zata sake yin wani hoton yan yatsu na masu zana jarabawar a karo na biyu domin ya basu damar damke wadanda ke shirya magudi da kuma cuta akan wannan jarabawa tare da masu basu goyon baya.
“A karshe hukamar na shirin bin hanyoyin shari’a domin a gurfanar da masu wannan laifi a gaban kotu kana kuma ayi musu hukuncin da ya dace dasu. A cewarta cigaba da aukuwar irin wannan laifin zai kawo cikas da kuma tabarbarewar gudanar da jarabawar ga baki daya.

SOURCE LEGIT. NG READ MORE

Friday

Yadda aka kama wasu daliban jami’a 2 suna zanama wani jarabawar JAMB

Ma'aikatar JAMB ta bayyana cewa ta kama wani dalibin aji uku a fannin ilimin kiwon lafiya da kuma wani dan jami’a suna yunkurin rubuta ma wadanda za suyi jarabawar JAMB na bana.
Jamb result 2019

Babban shugaban sashin labarai na kungiyar, Dr Fabian Benjamin ya bayyana hakane a wani tattaunawa da yayi da NAN a ranar jumaa a jihar Lagos.

NAN ta bada rahoto cewa an fara jarabawar JAMB dinne a ranar 11 ga watan Aprilu a cibiyoyi 678 a kasar .

Benjamin ya bayyana cewa, duk da cewar an jajirce wurin ganin cewar an kauda duk abinda zai kawo sata a jarabawar amma duk a banza sai da wasu suka yi yunkurin yin hakan.



Yace: "An kama wata budurwa a daya daga cikin cibiyar jarabawar a Jihar Kano tana kokarin zama domin ta zana ma daya daga cikin masu jarabawar."
Yayinda aka gudanar da bincike, an gano cewa budurwar dalibace a bangaren kiwon lafiya a jami’ar Usman Dan fodio dake Sokoto."

Ya bayyana ma NAN cewa an kara kama wani a Jihar Benin,wanda dalibi ne a jami’ar jihar.

A karshe yace: "Ma'aikatarmu ba zata lamunci irin wadannan alamuran da zasu kawo tangarda ba da nagarta wurin gudanar da jarabawar."

DUBA WANNAN : Hotuna : A karon farko Anyi Nasarar Daukar Hoton Ramin Zurmiya Na Duniya (Black Hole)

Thursday

Yanzu Yanzu: Ababe 10 da hukumar JAMB ta haramtawa Dalibai shiga da su dakin jarrabawa -

A yayin da a yau Alhamis, 11, ga watan Afrilun 2019, aka fara gudanar da jarrabawar neman shiga jami'a da hukumar JAMB ke shiryawa a fadin kasar nan, an haramtawa dalibai shiga da wasu ababe dakin jarrabawa.
jamb result 2019

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, za a gudanar da jarrabawar cikin jihohi 36 da ke fadin kasar nan da kuma birnin tarayya. Ana sa ran za a shafe tsawon mako guda gabanin kammala jarrabawar.

Kakakin hukumar JAMB cikin wata hirar sa da mamena a daren Larabar da ta gabata, ya ce akwai wasu ababe da hukumar ta haramtawa dalibai shiga da su dakin jarrabawa domin tabbatar da tsari da kuma aminci na hukumar.

KARANTA KUMA: Mun san komai: Da magudin zabe ka samu nasara a Kano - Abba ya caccaki Ganduje.

ma'aikatan gwamnati - Gwamnatin tarayya
Kimanin dalibai miliyan 1.99 masu neman shiga jami'o'i za su zana jarrabawar a bana cikin fadin kasar nan. Ana horar da su akan bibiyar tsari da kiyaye duk wata doka da kuma sharadi da hukumar ta gindaya.
Jaridar Legit.ng ta kawo jerin ababe da hukumar ta haramtawa dalibai shiga da su dakin jarrabawa kamar haka:



1. Agogo
2. Fensir/Biro
3. Na'urar lissafi (Kwakuleta)
4. Wayoyin Salula
5. Na'urar daukan hoto (Kamera)
6. Na'urorin sauraro da watsa sauti
7. Katin Banki (ATM)
8. Abin goge rubutu (Kilina)
9. Littafin da dukkanin dangin kayan karatu da rubutu
10. Yari da zobe masu fasahar zamani
11. Na'urorin ajiya na USB, CD da Hard disks
12. Tabarau mai kunshe da fasahar zamani

SOURCE LEGIT. NG

Wednesday

WAEC GCE Time table 2017 {Nov/Dec} Released – Download Pdf Here





The West African Examinations Council, WAEC has published the comprehensive timetable for the 2017 General Certificate Examination, GCE for candidates writing the exam.

The Waec Gce exam is scheduled to commence on Tuesday, 15th August and end on Wednesday, 4th October, 2017.

Candidates are to view the full time-table below;


WEST AFRICAN SENIOR SCHOOL CERTIFICATE EXAMINATION FOR PRIVATE CANDIDATES, 2017 FINAL INTERNATIONAL TIMETABLE

Candidates can download Weac Gce time-table in Pdf from the link below;
>> Download timetable here

* Available to candidates in Ghana only

** Available to candidates in Nigeria only

*** Available to candidates in The Gambia and Sierra Leone only

**** Available to candidates in Liberia only


Important Notes:

1. Difference in Time on Question Paper and Timetable: Where the duration indicated on the question paper differs from that on the timetable, the one on the question paper should be followed.

2. Question Papers to be Given Out in Advance of the Dates They Are to be Taken
– Visual Art 3;
Paper 3A – Instructions will be given to supervisors two weeks before the paper is due to be taken.
Paper 3B – Question papers will be given to candidates two weeks before the paper is due to be taken.

3. Extra Time for Blind, Deaf and Dumb Candidates: Blind, deaf and dumb candidates should be allowed one and half times the time allotted to other candidates.

The West African Examinations Council is West Africa’s foremost examining board established by law to determine the examinations required in the public interest in the English-speaking West African countries, to conduct the examinations and to award certificates comparable to those of equivalent examining authorities internationally.

The exam body remains Africa’s foremost examining body, providing qualitative and reliable educational assessment, encouraging academic and moral excellence and promoting sustainable human resource development and international
co-operation.