Ma'aikatar JAMB ta bayyana cewa ta kama wani dalibin aji uku a fannin ilimin kiwon lafiya da kuma wani dan jami’a suna yunkurin rubuta ma wadanda za suyi jarabawar JAMB na bana.
Babban shugaban sashin labarai na kungiyar, Dr Fabian Benjamin ya bayyana hakane a wani tattaunawa da yayi da NAN a ranar jumaa a jihar Lagos.
NAN ta bada rahoto cewa an fara jarabawar JAMB dinne a ranar 11 ga watan Aprilu a cibiyoyi 678 a kasar .
Benjamin ya bayyana cewa, duk da cewar an jajirce wurin ganin cewar an kauda duk abinda zai kawo sata a jarabawar amma duk a banza sai da wasu suka yi yunkurin yin hakan.
Ya bayyana ma NAN cewa an kara kama wani a Jihar Benin,wanda dalibi ne a jami’ar jihar.

Yace: "An kama wata budurwa a daya daga cikin cibiyar jarabawar a Jihar Kano tana kokarin zama domin ta zana ma daya daga cikin masu jarabawar."
Yayinda aka gudanar da bincike, an gano cewa budurwar dalibace a bangaren kiwon lafiya a jami’ar Usman Dan fodio dake Sokoto."
Ya bayyana ma NAN cewa an kara kama wani a Jihar Benin,wanda dalibi ne a jami’ar jihar.
A karshe yace: "Ma'aikatarmu ba zata lamunci irin wadannan alamuran da zasu kawo tangarda ba da nagarta wurin gudanar da jarabawar."
DUBA WANNAN : Hotuna : A karon farko Anyi Nasarar Daukar Hoton Ramin Zurmiya Na Duniya (Black Hole)
Hotuna : A karon farko Anyi Nasarar Daukar Hoton Ramin Zurmiya Na Duniya (Black Hole) https://t.co/heoUKnMz1g https://t.co/heoUKnMz1g April 12, 2019 at 02:51PM— AREWASOUND (@Arewasound) April 12, 2019
No comments:
Write Comments