Showing posts with label films review. Show all posts
Showing posts with label films review. Show all posts
Wednesday

Film Trailer : "LABARINA" Staring:- Nafisa Abdullahi Nazir Sarkin waka
Film Trailer : "LABARINA" Staring:- Nafisa Abdullahi Nazir Sarkin waka
Wannan wani kayataccen shiri ne wanda haziki fasihin mai bada umurni Aminu saira yayi Film mai sunan 'Labarina'.
Wanda a ciki yake dauke da manya manyan jarumai:-
1. Nafisa Abdullahi
2. Hafsat Barauniya
3. Nuhu Abdullahi
4. Nazir M Ahmad sarkin waka
Da dai sauransu
CHECK MORE 🌏
@Arewasound
Tuesday

Nazari Tare Da Sharhin Film Din Apocalypto
Apocalypto movie hausa review.
JARUMAI:-
Rudy youngblood (a matsayin babban jarumi) itandehui Gutirrez (matar jarumi) Jonathan brewer (amatsayin namiji mara gamsar da iyali) morris birdyellohead (amatsayin mataimakin boss) carlos emilio baez (dan karamin yaron nan wanda suka shiga rijiya shi mahaifiyarsa) mel gibson a matsayin boss rafael velez a matsayin sarki da sauransu..
BADA UMARNI:- Mel gibson
MATAIMAKIN MAI BADA UMARNI:- adrian grunberg
RUBUTA LABARI:- Mel gibson da taimakawar farhada safinia
FURODUSA:- ned dowd
KAMFANI:- touchstone pictures tareda kamfanin Icon production
MANAZARCHI:- Shaikh Farouq Abdullahi Tukuntawa
GUNDARIN LABARI... Fim din apocalypto fim ne da yake bayani akan wasu mutane da suke gudanar da rayuwarsu cikin farin ciki da kwanciyar hankali a wani qungurmin daji mai yalwar ni'ima da manyan bishiyu tareda ruwa mai gudana da dabbobin farauta
Suna cikin wannan rayuwa ne sai Allah ya aiko musu da ibtila'i na shigowar wasu mutane marasa imani masu shiga kauyuka suna kama mutane tareda kaisu chan chikin garin su ana yanka su domin mika jininsu ga abun bautarsu
Mutanen sun kutso har wannan kauyen tareda yi musu gagarumar barna da nuna musu zallar rashin imani wajen karkashe musu mutane tareda kama sauran wanda suke raye sannan suka daura musu igiya suka tafi dasu cikin tsananin uquba izuwa inda za'a yankasu ga abin bauta
Bayan an kaisu ne har an samu damar yanka wasu daga cikin su a lokachin da ka kwantar da jarumin za'a yanka da yake Allah yasa yana da rabon sake shan ruwa a duniya sai a lokachin hasken rana ya dusashe wanda hakan yana nuna kenan abun bauta ya koshi da jini kamar yadda su wadannan miyagun mutane suka chamfa.
Duk da haka zamu iya cewa tsugune bata kare ba a wajen jarumi rudy youngblood wato jaguar paw domin kuwa wadannan mutane basu shirya qyale su ba hasali ma sai suka shirya musu wata gadar zare ta hanyar yi musu sakin talala da basu damar guduwa amma a nufin shine idan sun fara gudu susa mashi su soke su har lahira
Duk da haka Allah ya bawa jarumin nasarar tserewa tareda hallaka ƙanin boss wanda yake matukar kauna
Hakan ne ya kara batawa boss rai nan take ya bada umarnin a bishi duk inda ya shiga a kamo shi domin ya dauki fansar kashe masa qaninsa, anyi gumurzu iya gumurzu jarumi yasha bakar wahala daga karshe ya kubuta har ya isa izuwa ga wata rijiya wacce ya boye matarsa mai tsohon ciki tareda karamin dansa aciki duk da wannan tsananin wahalar matarsa ta haifa masa kyakkyawan jariri a cikin rijiya a yayin da ake tsaka da kwarara ruwan sama.
SCREENSHOTS :-
ABUBUWAN BURGEWA
Anyi amfani da zunzurutun qwarewa wajen shirya wannan fim sannan jaruman fim din sunyi kokari wajen taka rawar da ake bukata afilm din
Anyi amfani da na'urorin zamani masu kyau wajen daukar wannan fim
Yanayin shigar mutanen chiki (tufafin su) da kuma yanayin dazuzzukan ya dace da labarin.
KURAKURAI...
Fim din ya tsaru yadda ake so kurakuran dake chiki ba su da yawa ba su wuCe na rashin nuna makomar kananan yaran da aka bari a hannun wannan karamar yarinyar da tace zata kula dasu ba, ya kamata ace a karshen fin din an nuno su
Sannan a karshen fim din lokachin da kungiyar kiristochi suka kawo musu taimako a jirgin ruwa bai kamata yaki binsu ba
Lokachin ake shigar dasu inda Za'a hallaka su acikin matan da suke shafa musu shudiyar kala an nuno wata mata sanye da rigar zamani a a maimakon rigar mutanen daji.
Wannan Kenan Daga abun da na nazarta bayan na kalli fim din.
Shaikh farouq Tukuntawa
Whatsapp me here
08135079888
Saturday

Bayani Akan Shirin Kwana Casa'in 90 : 90-DAYS HAUSA DRAMA REVIEW
KWANA CASA'IN REVIEW , 90 DAYS REVIEW.
Shirin "Kwana Casa'in" Shirine Wanda tashar Arewa24 suka fito dashi Kuma suke haskashi a kowanne mako,
![]() |
90 DAYS REVIEW |
Shirine Wanda Yake dauke da darussa masu Yawan gaske, a gefe guda Kuma ga nishadantarwa!
Kacokam zamu iya Cewa wannan shiri Yana Nuni NE zuwa ga rayuwarmu da muke a Ciki yanzu, Kama tun Daga yanda Yan Siyasa suka mayar damu, da lalacewar da ilimi yayi a wannan Qasa tamu, da irin yanda zakaje asibitocin gwamnati ka tadda Babu magani Babu maaikata, wani asibitin ma ko wutar lantarki zaka tarar Babu a Ciki saidai majinyata su dinga yin fifita da mafici!
Zance na gsky Banga wani film Mai tarin ma'ana a wannan Lokacin kamar wannan shiri Mai suna kwana Casa'in ba!
Ko Kadan Babu maganar Bata Tarbiyya a Cikinsa! Saidai maa gyarata, zaka iya Umartar iyalinka da kallon wannan Shirin domin kuwa zasu koyi darussa masu Yawan gaske a Cikinsa!
Inama ace Yan Kannywood da Suke ikirarin suna gyara Tarbiyya a kullum, zasu kwaikwayi irin wannan shiri su dinga yin makamancinsa?
Na gamsu da tashar Arewa24 100% Kuma Ina jinjina musu game da irin qoqarin da sukeyi na qara wayar da Kan mutanen arewacin qasar Nan Dama Duniya Baki Daya!
Rubutawa : Abubakar Haruna Sani.
READ ALSO
The new drama series from AREWA24, ‘Kwana Casa’in’ (90 Days), has come with new plots and styles that are quite different from the Kannywood movies we watch every day. The story tells about Nigerian politics and what has really been happening in our universities and in our daily lives. For decades, our Kannywood movies should be pointing out the kind of problems we were faced with; instead, our Hausa movies portray dancing, music, and modeling. In the 90 days drama series, there is a very high-quality picture which is different compared to Kannywood movies. This is because high-quality equipment has been used in the film making to give viewers a quality picture. And the locations used in the drama are quite amazing, places such as hospitals, offices, homes, universities and a radio station. Really, AREWA24 has used a collection of professionals and they deserve a thump up. Looking at the places in the drama, even if someone is living outside Nigeria, they can fully understand what the story is trying to portray. This alone shows that AREWA24 is one of a kind and with professionals.
Whenever I am watching ‘Kwana Casa’in,’(90 Days) I feel like am watching a reality drama, because the drama shows the way people in power and the way the poor life. Today, people in power make good use of the poor to subjugate high positions by all means. I believe that, before the end of this drama, many people will learn different lessons in life. When I first saw the faces of some Kannywood actors and actress, I felt weak and fear engulfed my heart - - the fear of sabotaging the drama the way they always did in their movies. But, to my surprise, they appear to be different and serious in this drama without making us bored with watching it. This showed me that, if they can have a good story and equipment, and invite educated people in their productions, I feel that they might be even better in the Kannywood film Industry. The way these artists showed commitment and expertise; it is very impressive.
Even those who watch foreign movies will salute them because developed countries were producing dramatic series about issues facing them in their countries, unlike the trash in the films we’re used to watching. It seems like the 90 days drama will overshadow AREWA24’s drama series, Dadin Kowa, as there is no single drama from the Kannywood [film industry] to rub shoulders with Dadin Kowa so far. It may only be AREWA24 that can be able to shine again with its new and well-produced drama series, 90 days (Kwana Casa’in). During the long time I have been watching Kannywood’s Hausa films, I realized that there is a school for Kannywood to learn more. Gradually AREWA24 will replace Hausa dramas because they are treating issues that are affecting us in this country, not just singing and dancing on our TV screens. Fadila H Aliyu Kurfi is a writer and analyst on current affairs and an activist. She can be contacted through email: fadilakurfi@gmail.com, Facebook: Fadila H Aliyu Kurfi.
Subscribe to:
Posts (Atom)





