A kalla mutane bakwai ne jami’an kiwon lafiya suka tabbatar da mutuwarsu a sakamakon barkewar cutar Sankarau a jihar Nejan Najeriya.
Daraktan kula da lafiyar jama’a a ma’aiktar lafiya ta jihar Neja Dr Muhammad Usman, ya ce cutar ta barke ne a kananan hukumomin Agwara, Kontagora da kuma karamar hukumar Magama, amma ya bayyana cewa kawo yanzu an sami shawo kan lamarin domin an tura jami’an kiwon lafiya.
Da yake hira da wakilin sashen Hausa na muryar Amurka Mustapha Nasiru Batsari, ta wayar tarho, Dr Muhamad, ya bayyana cewa a karamar hukumar Magama ne lamarin ya fi ta’azzara, domin a karamar hukumar ne mutanen bakwai suka rasu.
Shugaban karamar hukumar Magama, Alhaji Muhammad Mamman Auna, ya bayyana cewa shigowar zafi kuma mutane na kwana cikin dakunansu yasa lamarin ya faru duk da shike an aika da ma’aikata domin fadakar da jama’a kan illar kwana a daki cikin zafi, da kuma samar da magunguna domin tallafawa jama’a.
Yawancin wadanda suka rasu kananan yara ne a cewar shugaban karamar hukumar, kuma a ranar Talatan nan ake sa ran ma’aikatar lafiyar jihar zata yiwa manema labarai cikakken bayani akan barkewar wannan cuta a jihar Neja.
No comments:
Write Comments