Saturday

Home "Wadanda suke tsoron kar na fallasa su sune suke yakata" : Ibrahim magu



Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin
hanci da yiwa tattalin arziki zagon kasa wato
EFCC, Ibrahim Magu, ya ce wadanda suke tsoron
ka da a fallasu ne suke yakar sa.

Mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim
Magu

A makon da ya gabata ne dai majalisar dattawan
kasar ta ki amincewa da Ibrahim Magun a
matsayin tabbataccen shugaban hukumar ta
EFCC.

Kuma wannan shi ne karo na biyu da majalisar
ke kin tabbatar da Ibrahim Magu.

'Yan majalisar dai na kafa hujja da cewa sun
sami rahoto kan Magu daga hukumar tsaron farin
kaya, DSS, ta kasar.

Rahoton dai ya nuna Ibrahim Magu na da tabon
laifi abin da ke sanya shakku kan yiwuwar yakar
cin hanci da rashawa.

A baya shafin NAIJ.com ya ruwaito cewa wani dan
majalisa, Sanata Dino Melaye yace babu yadda
za ayi shugaba Buhari ya kara turo sunan
Ibrahim Magu a matsayin shugaban EFCC don
kuwa akwai dokar Majalisa da ta haramta hakan.
Melaye yace don haka Majalisa ba za ta kara
la’akari da Magu ba a matsayin shugaban EFCC.
No comments:
Write Comments