Tuesday

Home “Yadda Mu Ka Ga Buhari- A Fadin wani Gwamnan Kudu.”
Wata ziyara da wasu gwamnoni
da shugabannin jam'iyar APC a
Najeriya suka kai wa shugaba
Muhammadu Buhari,a gidan da
yake jinya a birnin London a
Birtaniya, ta kara fito da halin da
shugaban ke ciki wanda ya
kwashe wani tsawon lokaci yana
jinya a Birtaniya.




Fadar shugaban kasar Najeriya ta Aso
Rock, ta fitar da wata sanarwa kan
halin da shugaban Najeriya
Muhammadu Buhari ke ciki, bayan
da wasu gwamnoni da shugabannin
jam’iyar APC mai mulki suka
ziyarce shi a gidan da yake jinya a
birnin London.
Wata sanarwa dauke da sa hannun
mai bai wa shugaban shawara kan
harkar yada labarai, Femi Adesina,
wacce aka wa take da “Yadda Mu
Ka Ga Buhari- A Fadin Gwamna
Okorocha.” Ta nuna cewa
shugaban na samun sauki sosai,
Gwamnan jihar Imo Rochas
Okorocha na daya daga cikin
gwamnonin da suka ziyarci Buhari
a jiya Lahadi, shi ne kuma ya fadi
halin da Buhari ke ciki a cewar
sanarwa wacce aka rubuta ta da
harshen ingilishi.
“Gwamnan jihar Imo, Rochas
Okorocha, ya ce shugaba
Muhammadu Buhari na cikin
koshin lafiya – kuma yana nan da
wasansa na barkwanci.” Sanarwar
ta bayyana."
Shugaba Buhari wanda ya nuna
farin cikinsa da ziyarar
gwamnonin da shugabannin
jam’iyar, ya kwashe sa’a guda yana
tattaunawa da su kuma ga dukkan
alamu yana sane da duk abinda ke
faruwa a gida (Najeriya), a cewar
sanarwar.
Shugaba Buhari ya kuma tambayi
ministan kula da sufuri, Rotimi
Amaechi (wanda shi ma yana cikin
tawagar) kan halin da fannin
sufurin jirgin kasa kasar ke ciki.
A lokacin da aka tambayi shugaba
Buhari kan irin kalamai mara dadi
da ake fada a kansa, sanarwar ta
nuna cewa, “shugaban sai ya yi
dariya, ya kuma kwatanta kalaman
akan wadanda aka dasa su akan
karerayi. Kuma gwamna Okorocha
ya bayyana cewa babu wata da ta
nuna cewa Buhari ya damu da
maganganun da ake yi akansa –
maimakon haka sai ya ce yana
mika sakon gaisuwarsa ga ‘Yan
Najeriya.”
“Kada ‘Yan Najeriya su damu ko
kadan, shugaban Buhari zai dawo
nan ba da jimawa ba, da zaran
likitocinsa suka amince.” Sanarwar
ta kara fada.
“Da wannan ziyara da muka kai
yau (Lahadi) a London, karyar
masu yayata jita-jita ta kare,
saboda ‘yan Najeriya ba za su
yadda da jita-jitar da suke yadawa
ba, kuma duk wadanda suke bi-
biyan labaran karya, gara su yi
wani abu daban da lokacinsu.” In ji
Okorocha, kamar yadda sanarwa ta
bayyana.
Baya ga gwamna Okorocha na jihar
Imo da minsitan sufuri Amaechi da
ke cikin tawagar, har ila yau akwai
gwamnan jihar Nasarawa Umaru
Tanko Al-Makura, da Nasiru El –
Rufai na Kaduna da Yahaya Bello
na Kogi, da kuma shugaban
jam’iyar ta APC na kasa, Cif John
Oyegun.
No comments:
Write Comments