Dandalin Kannywood: Har yanzu ni yarinya ce karama,
ban isa aure ba - Rukayya Dawayya.

Shahararriyar jarumar da ta taka
muyimmiyar rawa a fina-finai da dama tare
kuma da bada gudummuwar ta musamman
ma wajen habakar masana'antar ta ayyana
cewa ita duka-duka yanzu shekarar ta 29 a
duniya.
NAIJ.com a cikin wani dan nazari da tayi
game da zancen nata ta binciko cewa indai
har hakan ta tabbata to lallai kenan jarumar
tana da shekaru 13 kacal a duniya ne ta fito a
cikin fim din Dawayya.
Shi dai fim din Dawayya kamar yadda
binciken namu ya tabbatar, an shirya shi ne
a shekara ta 2001 wanda yanzu kimanin
shekaru 16 kenan.
A lissafi kenan idan aka cire shekaru 16 daga
cikin 29 ya zama shekaru 13.
source :-- hausanaij.com
No comments:
Write Comments