Naira tayi abin da ba ta taba yi ba.
Darajar Naira ta fadi kasa war-was
– Yanzu haka Dala ta kai N520 a kasuwar
canji
– Ba a taba samun haka ba a Tarihin
Najeriya
Tun da ake ba a taba samun lokacin da
farashin Naira ya zube kasa ba kamar
wannan lokaci. A yau dai Nairar tayi
irin dukan kasar da ba ta taba yi ba.
Yau dai Litinin, an wayi gari an samu
Dalar Amurka tana kan Naira 520.
Yanzu haka Dalar ‘Pound’ na Ingila ta
kai Naira N635 yayin da Euro kuma ta
kai N545. Tun da ake dai Naira ba ta
taba sukurkucewa ta lalace irin haka ba.
Za dai a iya duba sauran farashin a
shafukan mu.
Masana sun ce farashin ma na iya fin
haka muni nan gaba. Wasu na cewa
Dala na iya kai Naira N1000 idan ba a
iya wasa ba. Haka wani gawurtaccen
Fasto TB Joshua kuma ya bayyana daga
cikin abubuwan da ya hango.
A wancan makon Majalisar kula da
tattalin arziki na kasa watau NEC ta
nemi Gwamnan babban bankin CBN
yayi wani abu game da yadda Naira ta
fadi war-was.
Gwamna Emiefele yace
CBN na kokari game da hakan sai dai a
kara masa lokaci wanda yanzu an fara
shirin sayar da Dala Miliyan daya ga
manyen ‘yan kasuwar canji a kowane
mako.
hausapost28 on facebook
Darajar Naira ta fadi kasa war-was
– Yanzu haka Dala ta kai N520 a kasuwar
canji
– Ba a taba samun haka ba a Tarihin
Najeriya
Tun da ake ba a taba samun lokacin da
farashin Naira ya zube kasa ba kamar
wannan lokaci. A yau dai Nairar tayi
irin dukan kasar da ba ta taba yi ba.
Yau dai Litinin, an wayi gari an samu
Dalar Amurka tana kan Naira 520.
Yanzu haka Dalar ‘Pound’ na Ingila ta
kai Naira N635 yayin da Euro kuma ta
kai N545. Tun da ake dai Naira ba ta
taba sukurkucewa ta lalace irin haka ba.
Za dai a iya duba sauran farashin a
shafukan mu.
Masana sun ce farashin ma na iya fin
haka muni nan gaba. Wasu na cewa
Dala na iya kai Naira N1000 idan ba a
iya wasa ba. Haka wani gawurtaccen
Fasto TB Joshua kuma ya bayyana daga
cikin abubuwan da ya hango.
A wancan makon Majalisar kula da
tattalin arziki na kasa watau NEC ta
nemi Gwamnan babban bankin CBN
yayi wani abu game da yadda Naira ta
fadi war-was.
Gwamna Emiefele yace
CBN na kokari game da hakan sai dai a
kara masa lokaci wanda yanzu an fara
shirin sayar da Dala Miliyan daya ga
manyen ‘yan kasuwar canji a kowane
mako.
hausapost28 on facebook
No comments:
Write Comments