Thursday

Home › › Dimbin jama’ar da suka fito don tarba ta a Kano, ya nuna zan sake cin zabe a Kano – Inji Buhari
A yayin jawabinsa a fadar Sarkin Kano,
Buhari yace ganin dimbin jama’n da duka yi masa maraba a jihar, ya nuna cewa zai iya sake cin jihar Kano a kakar zabe ta shekarar 2019.

Majiyar NAIJ.com ta ruwaito Buhari na cewa
“Na yi mamaki matuka da irin jama’an dasuka fito tarba ta, wannan na nuni da zamu cin zabe a jihar Kano, haka zalika hakan na nufin Kanawa na sane irin kokarin da muka yi musu a fannin tsaro da noma.”

Buhari ya cigaba da fadin> “Mun samu
nasarori a kokarin mu an cika alkawurran
muka dauka da suka hada da tsaro, tattalin arziki, da kuma yaki da rashawa. a yanzu haka hadakan kasashen Nijar, Chadi da Najeriya sun samu galaba a kan Boko Haram.”

Shugaba Buhari yace zaman lafiya a yankin
Arewa na da matukar tasiri a Najeriya gaba daya, ta yadda idan Arewa ta zauna lafiya, toh Najeriya ma ta zauna lafiya kenan, hakazalika idan akwai matsala a Arewa, Najeriya ma bata da lafiya kenan.

Dayake jawabi kan bambamcin mulkin Soja
da na farar hula, Buhari yace “A lokacin da nake mulkin Soja, na kama mutane da dama, a kan zargin cin hanci da rashawa, daga karshe ni ma na kare a Kurkuku. Amma tun daga 1994-2014, gwamnatin Najeriya ta samu kudi,
sai dai an yi bindiga da su.”

Daga karshe Buhari ya yaba ma masarautar
Kano, inda yace duk abin da ya zama a
rayuwarsa, ya zama ne a dalilin gudunmuwa
daya samu daga masarautar Kano.
No comments:
Write Comments