Wani jirgin kasan fasinjoji dake hanyar sa ta
zuwa Kano daga Legas ya samu matsala a
tsakiyar jeji dake nesa da babban birnin
Osogbo a jihar Osun.
Mafi yawan fasinjojin dake cikin na hanyar
su ta zuwa Kano domin bikin sabuwar
shekara da iyalansu. Saidai a halin yanzu sun
fara fitar da tsammanin cikar wannan buri
na su.
Jirgin kasa dauke da fasinjojin zuwa Kano ya lalace a
tsakiyar daji
Wani daga cikin fasinjojin jirgin kuma
matashi mai hidimtawa kasa ya fadawa
jaridar Daily Trust cewar tun bayan samun
matsalar jirgin, jami'an hukumar kula da
jiragen kasa dake cikin jirgin sun gaza yin
abinda ya kamacesu ta fuskar nuna damuwa
ko kulawa ga fasinjojin dake cikin jirgin.
Matashin ya kara da cewa "Wannan jirgin
yana tafiya zuwa Kano ne daga Legas, amma
ya samu matsala jim kadan bayan barin
Osogbo. Muna tsakiyar daji tun misalin karfe
7 na safe, ga shi har yanzu babu cigaba da
aka samu. Muna cikin mawuyacin hali, domin
gaskiya muna shan wahala, ga shi jami'an
hukumar NRC dake cikin jirgin basu da
kyakykyawar mu'amala da mutane".
Hakazalika ragowar fasinjojin dake cikin
jirgin sun koka da halayyar ma'aikatan jirgin
ta nuna halin ko-in-kula da halin da
fasinjojin suka tsinci kansu.

No comments:
Write Comments