A yayin wata ziyara daya kai jihar Katsina,
tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa
Kwankwaso, kuma madugun kwankwasiyya, ya
gaud a dimbin masoya, kamar yadda NAIJ.com ta
gano.
Masoyan sun tare Sanata Kwankwaso ne a
garin Kankara, yayind a yake kan hanyarsa
ta zuwa jihar Katsina, inda ya fito daga
Motarsa, ya gana da masoyansa.
JAGORAN KWANKWASIYYA.
A ranar 30 ga watan Janairu ne ake sa ran
tsohon gwamnan na jihar Kano zai kai ziyara
jihar Kano don ganawa da masoyansa, karo
na biyu tun bayan daya sauka daga mukamin
gwamnan jihar.
Sai dai wasu masana harkar Siyasa sun
danganta ziyarar da tsohon gwamnan zai kai
jihar da shirin daukar damara kan burinsa
na sake tsayawa takarar shugaban kasar
Najeriya a shekarar 2019, inda tuni jita jita
ya watsu kan cewa zai fice daga jam’iyyar
APC.
SAURAN HOTUNA
Idan mai karatu zai tuna, tun bayan mika
ragamar mulki ga magajinsa, Gwamna
Abdullahi Ganduje, ba’a sake samun
kyakkyawar dangantaka tsakanin gwamnan
da Kwankwaso ba.
(GET LATEST NEWS AND MEDIA UPDATES.
Send Arewa24ng To 40404 its free, No charge)
SOURCE : HAUSA.NAIJA.NG
No comments:
Write Comments