Saturday

Home Fati Gombe - An hana ni takara a PDP don na ki amince ayi lalata da ni - Read more:
Wata mai neman tikitin takarar majalisar jiha a Gombe a jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Hajiya Fati Gombe ta ce an ki tantance ta domin tsayawa takara a jam'iyyar ne saboda ta ki amincewa wasu gurbatattun shugabanin jam'iyyar suyi lalata da ita.


 "Rashin tantance da kwamitin tayi bai bani mamaki ba saboda akwai daya daga cikin 'yan kwamitin da ya bukaci in same shi a otal ko kuma in bayar da cin hancin N100,000 muddin ina son a tantance ni. "Ina da shaida saboda lokacin da ya nemi in zo in same shi a otal din nayi amfani da waya ta na dauki maganar kuma nan gaba zan bayyana wa duniya wannan hirar kuma in fadi sunansa," inji Fati.

 Mawakiyar wadda ke da gidauniyar tallafawa mata, marayu da sauran marasa galihu da shawarci Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo na jihar Gombe da uwar jam'iyyar PDP suyi bincike tare da magance gurbatattun da ke jam'iyyar.

No comments:
Write Comments