Za a fafata da dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, a zaben gwamnoni da mambobin majalisar dokoki da za a yi ranar Asabar, 9 ga watan Maris.
A wani hukunci da kotun daukaka kara ta kara ta yanke a yau, Alhamis, kotun ta dakatar da hukuncin da kotun farko ta yanke na umartar hukumar zabe ta kasa (INEC) a kan ta cire sunan dan takarar jam’iyyar PDP daga cikin jerin ‘yan takarar gwamna da za su fafata a zaben neman kujerar gwamnan jihar Kano.
A ranar Litinin ne Jastis Lewis Allagoa na babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Kano ta yanke hukuncin a hana PDP shiga zaben saboda jam’iyyar ba ta gudanar da zaben fidda ‘yan takara bisa ka’ida ba. Ali Amin-Little, daya daga cikin wadanda su ka nemi jam’iyyar PDP ta tsayar da su takarar gwamna a jihar Kano ne ya shigar da karar kalubalantar tsayar da Abba a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP.
A ranar 2 ga watan Oktoba na shekarar 2018 ne aka bayyana cewar Abba, surukin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a matsayin wanda ya kasha zaben cikin gida da PDP ta yi da adadin kuri’u 2,421 yayin da mai biye ma sa, Jafar Sani Bello, ya samu kuri’u 1,258.

No comments:
Write Comments