Saturday

Home A karshe Dai : Atiku ya tashi zuwa kasar Amurka
A cewar The Cable wani daga cikin iyalin tsohon shugaban kasan ya tabbatar da cewa an bashi takardan izinin shiga kasar.

A watan Oktoba, Direkta Janar na yakin neman zaben Atiku Presidential Campaign Organisation (APCO), Gbenga Daniel ya yi ikirarin cewa Amurka ta fadawa Atiku cewa zai iya neman visar.


A yayin da ake yi tambaya a kan batun a ranar Juma'a, Jami'in hulda da jama'a na ofishin jakadancin Amurka da ke Legas, Brussel Brooks ba yi tsokaci kan batun ba inda ya ce sirri ne.

A baya, an ganin kamar Atiku ba zai iya shiga Amurka ba saboda ana zargin cewa ya hada baki da wani dan majalisa a Amurka, William Jefferson wajen karbar rashawa kuma shi dan majalisar an tabbatar da laifinsa a Amurka.

Duk da cewa Atiku ya jadada cewa bai aikata wani laifi ba, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta dade tana kallubalantarsa ya tafi Amurka idan har ya tabbatar bashi da laifin.
A ranar Alhamis, Ministan yada labarai na Najeriya, Lai Mohammed ya gargadi Amurka da kada da sake ta bawa Atiku visa idan har ba ta son nuna fifiko tsakanin 'yan takarar shugabancin kasa na shekarar 2019.

An ruwaito cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin Amurka ta bawa Atiku izinin shiga kasar.
No comments:
Write Comments