Tuesday

Home Alhaji Tanko yakasai Ya Aikewa da Buhari Sako, "kar ka dauka kayi nasara akan Atiku : cewar yakasai
Kar ka dauka ka gama samun nasara a kan Atiku - Tanko Yakasai ya aika sako ga Buhari 

Yakasai a wata hira da jaridar The Sun yace akwai illa sosai tattare da yasar da Atiku a lissafin mulkin kasar.

Tanko yakasai


Da yake Magana akan shirin Atiku na zuwa kotu akan sakamakonzaben Shugaban kasa da ya gudana a ranar Asabar, 23 ga watan Fabrairu, Yakasari yace Atiku yayi amfani da duk wata dama da yake da ita.

Yace: “A koda yaushe zan goyi bayan mutane da su je kotu saboda kotu ce mai sulhunkarshe. Bana son a cuci kowa. Ya je duk inda yake da dammar baje kwanjinsa.”
Yakasai yace kada Shugaban kasar ya dauka ya gama samun galaba akan Atiku domin a cewarsa shugaba Buhari ya lashe ikon siyasa ne kawai nyayinda Atiku ya lashe ikon tattalin arzikin kasar.

A wani lamari na daban, mun ji cewa an nemi tsohon babban alkalin alkalai na kasa (CJN), Walter Onnoghen, an rasa shi a gaban kotun ladabtar da ma'aikata ta kasa (CCT), inda ake ci gaba da yin shari'arsa kan zarginsa da gaza bayyana kadarorinsa.
Lauyansa, Adegboyega Awomolo (SAN), a yayin da yake gabatar da dalilin rashin zuwan wanda ya ke karewa, ya shaidawa kotun cewa, a daren ranar Litinin, an sanar da shi cewa mai shari'a Onnoghen na fama da ciwon hakori.
Ya gabatarwa kotun takardar asibiti da ta tabbatar da wannan ikirari na sa.
No comments:
Write Comments