Da safiyar yau Talata ne maraha suka tare wata mota mai dauke da wani injiniya dan kasar waje, suka yi garkuwa da shi, sannan kuma suka harbe direban da ke tuka shi.
'
Wadanda abin ya faru kan idon su, da kuma rundunar ‘yan sandan jihar Jihar Kano ta tabbatar da haka.
Ganau yace abin ya faru ne daidai karfe 7:40 na safiyar yau Talata.
Wanda aka harbe din dai ya na aiki ne a kan titin kusa da shataletalen Dangi, inda ake aikin titi da gada a Kano, daidai mahadar Titin Gidan Zoo da Zaria Road.
Har zuwa yanzu dai ba a tantance sunan wanda aka sace din ba, kuma ba a san ko dan wace kasa ba ne.
Ganau ya shaida wa JARIDAR PREMIUM TIMES cewa ‘yan sanda sun je daga baya sun daiki gawar direban.
Shi kuma Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Kano, Abdullahi Haruna ya tabbatar da afkuwar kisan da yin garkuwar.
Ya ce jami’an su na nan sun dukufa bincike.
No comments:
Write Comments