Alhaji Hashim Suleiman, babban mai bawa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, shawara a kan raya birane, ya mika takaradar sa ta yin murabus daga mukamin sag a sakataren gwamnatin jihar Kano a yau, Laraba. A takardar sa ta yin murabus din, ya bayyana cewar dalilinsa na dauka wannan mataki shine saboda gwamna Ganduje ya ki amincewa da kayen da dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, ya yi ma sa. Suleiman ya ce Abba ne ya lashe zaben na ranar Asabar da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana a atsayin wanda bai kammalu ba.
Ganduje da Abba Gida-Gida Source: UGC A takardar da Suleiman ya rubuta da hannun sa, y ace: “na rubuta wannnan takarda ne domin sanar da kai cewar na ajiye mukamina na bayar da shawara a kan raya birane bisa radin kai na.
“Ina mai godiya gare ka bisa damar ka bani na yin aiki a gwamnatin ka.” Sannan ya kara da cewa kamata ya yi gwamnan da ke amsa sunan ‘Khadimul-Islam’ ya kasance mai rungumar kaddara da yarda da ikon Allah a duk halin da ya tsinci kan sa.
No comments:
Write Comments