Monday

Home Tsohon gwamnan Plateau na kwance a asibiti bayan ya kamu da rashin lafiya a gidan yari
An bayyana cewa an kwashi Dariye wanda aka yankewa shekaru 10 a gidan yari saboda satar kudin kasa zuwa asibitin koyarwa na Abuja, Gwagwalada tun a watan Disambar da ya gabata.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa wata majiya kusa da tsohon gwamnan ta fada ma yan jarida cewa baya cikin kyakyawar yanayi.

Dan majalisan, wanda ya kasance a kurkukun Kuje dake Abuja ya kasance a asibiti tun watar Disamba da ya gabata.
Sanata Dariye na fama da matsalar gazawar koda a gidan yari
A cewar majiyin gwamnati wanda ya nemi a boye sunansa yace Dariye na matukar bukatan addu’a sosai.

Majiyin yace: ”na je ganin shi. Daga binciken likitoci, yana fuskantar kalubale a kiwon lafiyarsa, yana matukar fama da matsalar koda.

Kakakin hukumar Firson na Najeriya (NPS), reshen Babban Birnin Tarayya Chukwuedo Humphrey, ya tabbatar da cewa Dariye na a asibiti, amman ya ki bayyana yanayin ciwon.
Ya ce tun daga watan Oktoba na shekaran da ta gabata ne hukumar ke kula da rashin lafiyarsa.
No comments:
Write Comments