Monday

Home Yadda APC ke shirin amfani da sojoji domin murde ma na zabe –PDP
Ini Ememobong, sakataren watsa labaran jam’iyyar PDP a jihar Akwa ibom, ne ya bayyana hakan a jiya, Lahadi.

“Atisayen da dakarun soji ke yi don nuna karfin iko a wasu kananan hukumomi 10 shiri ne na bawa jam’iyyar APC damar aikata magudi a zaben gwamna.
“Mun san cewar sun bullo da wannan salon yaudara ne bayan kokarin su na kwatar kujerar sanata da godswil Akpabio ya rasa a zaben ranar 23 ga watan Fabarairu bai cimma nasara ba.
“Wannan sanarwa da rundunar soji ta fitar ba wani abu ba ne face yunkurin yin amfani da karfi domin yin aringizon kuri’u da zai bawa APC nasara a zabe.
Buhari a Akwa Ibom
“A matsayin mu na jam’iyyar siyasa, ba mu ga wani dalili na bayyana kananan hukumomin a matsayin ma su hatsari ba. Kowa ya san cewar ba a samu asarar rai ko daya ba a zaben baya da aka yi a jihar Akwa Ibom.
“Mu na son yi wa rundunar soji tuni cewar aikin su shine tsaron Najeriya ba aiki irin na ‘yan sand aba duk da mun san cewar jam’iyyar APC na bugun kirji a kan cewar soja zai iya yin duk aikin da dan sanda zai yi ,” a cewar PDP.

PDP ta kafe kan cewar ba ta ga dalili na daukan matakin amfani da dakarum soji a yankunan da babu wata barazana ga zaman lafiya tare da kafa hujja da korafin da shugaba Buhari ya shigar a shekarar 2015 lokacin da ya ke takarar shugaban kasa a shekarar 2015.
No comments:
Write Comments