Wankin hula na neman ya kai Jam’iyyar APC a jihar Bauchi dare inda hukumar Zabe ta amince da a sake kirgi sakamakon zaben da aka yi na karamar hukumar Tafawa Balewa sannan an tabbatar da yin aringizon kuri’un da aka soke a karamar hukumar Ningi cewa 2,533 ba 25,330 kamar yadda aka bayyana a da.
Idan ba a manta ba Dominion Anosike, wadda ita ce Jami’ar Tattara Sakamakon Zaben Gwamna na Karamar Hukumar Tafawa Belewa a Jihar Bauchi, ta bayyana cewa rayuwar ta na cikin hatsari, domin ana yi mata barazana da kisa a Jihar Bauchi.
Ta yi wannan ikirarin ne a cikin wata wasikar da ta aika wa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), inda a ciki ta ke rokon a ba ta dama ta bayyana a gaban kwamitin bincike domin ta fadi gaskiyar abin da ya faru har aka soke sakamakon zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa.
A cikin wasikar, wadda ta aika wa Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, a ranar 13 Ga Maris, 2019, ta amince ta bayyana ta fadi abin da ta sani.
Sai dai kuma ta yi rokon cewa ta fi so a yi zaman kwamitin a Abuja, ba a Bauchi ba.
Anosike ta ce ta na fuskantar Barazana cewa za a kashe ta matsawar aka gan ta ko a cikin Bauchi ko a kewayen Bauchi.
“Ni ce na shugabanci zaben da aka gudanar a Karamar Hukumar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi, don haka nay i amanna cewa akwai bukatar na zo na bayar da bayanin abin da ya faru har Kwamishinan Zabe na Bauchi ya soke zaben Tafawa Balewa.” Inji Anosike.
PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda jami’ar tattara sakamakon zabe na Karamar Hukumar Tafawa Balewa, Dominion Anosike ta ce ‘yan bangar siyasa sun kwace sahihin kwafen sakamakon zaben, wato Form EC 8C 1.
Babban Jami’in INEC mai bayyana sakamakon zabe, Mohammed Kyari ne ya ki amincewa da sakamakon zaben Karamar Hukumar Tafawa Balewa, Bayan da aka yi zargin ‘yan bangar siyasa sun hargitsa dakin taron da ake tattara sakamakon zaben.
Anosike ta ce akwai sakamakon zabe na wata mazaba guda daya da aka keta kwafin takardar da ya ke ciki, sai ta yi amfani da kwamfuta ta rubuta sakamakon.
Sai dai kuma shi Kyari, ya ce ba zai yi amfani da sakamakon wanda ta rubuta ba, domin kafin ta zartas da hukunci ba ta tuntube shi ba. kuma ya ce ba ta nemi izni ko shawarar Kwamishinan Zabe na Jihar Bauchi ba.
PREMIUM TIMES ta gano cewa INEC ta kafa kwamitin bincike a karkashin jagorancin Festus Okoye, kuma har kwamitin ya gana da masu ruwa da tsaki a zaben. Kuma za su mika sakamakon binciken da suka gano ga INEC.
DUBA WANNAN : N400 Per Refferal, No Payment Needed - Try it
DUBA WANNAN : N400 Per Refferal, No Payment Needed - Try it
A yanzu dai alamomi sun nuna cewa Anosike yanzu a boye ta ke, domin a cikin wasikar wadda ta aika wa Shugaban INEC, ta fadi lambobi da sunan wanda za a iya tuntuba, idan har ana neman ta.
A dalilin haka, bisa ga nazarin da hukumar zaben tayi, an samu tabbatattun takardun da aka shigar da sakamakon zaben Karamar hukumar Tafawa Balewa din da hakan ya sa dole ita hukumar ta dauki wannan matsayi.
Hukumar ta ce za ci gaba da bayyana zaben kamar yadda a ka far a baya sannan ta canja wanda zai ci gaba da bayyana sakamakon zaben bisa ga korafin da Anosike ta yi na wasu na bibiyan sai sunga bayan ta.
Bayan haka kuma INEC ta amince da korafin kara yawan kuri’un da aka soke a karamar hukumar Ningi, an yi kari. Ad dai an saka sama da kuri’u 25,000 ne amma bayan samun ainihin takardun da aka shigar da sakamakon zaben an gano kuri’u 2000 ne kacal suka lalace a Ningi din.
No comments:
Write Comments