Thursday

Home Babu Batun cire tallafin mai a Najeriya - NNPC ta magantu
Kamfanin NNPC ya ce duk irin yadda farashin kayayyakin man fetur ke ta shi, amma hakan ba zai sa a cire tallafin man fetur ba, inda ya tabbatar wa da 'yan Najeriya cewa za a cigaba da sayar da man fetur akan farashin da aka san shi wato naira 145 Duk da karuwar farashin kayayyakin man fetur, za a cigaba da sayar da man fetur akan naira 145, in ji kamfanin man fetur na Najeriya NNPC.
cire tallafin mai, buhari ya cire tallafin mai

A wata hira da ya yi da manema labarai a waya jiya Laraba a Abuja, babban jami'in hulda da jama'a na kamfanin man fetur din, Mista Ndu Ughamadu, ya ce kamfanin zai ci gaba da amfani da farashin da aka saba amfani da shi na naira 145.

ta tabbatar da haka Source: UGC Ughamadu ya ce, "Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata cigaba da sayar da man fetur akan farashin da aka san shi na naira 145 a kowacce lita. Kamfanin NNPC ba zai cire tallafi ba. A jiya Laraba ne kamfanin NNPC ya musanta kashe dala biliyan 22 na aikin ginin kamfanin LNG.

KU KARANTA: Gudun abin kunya: Yadda Tsohon shugaban kasa ya harbe kan sa.

A wata sanarwa da ya bayar ga manema labarai a Abuja, Ughamadu ya ce kamfanin ya kashe dala biliyan 1.2 kawai a aikin ginin kamfanin.

Ughamadu ya bayyana cewa kamfanin ya bayar da bayani a kwamitin majalisar wakilai lokacin da ake gabatar da bincike akan kudaden. A satin da ya gabata ne dai bankin IMF ya bai wa gwamnatin tarayyar Najeriya shawarar ta cire tallafin man fetur, domin ta samu wata hanyar da kudi zai dinga shigo mata, ganin irin yadda kasar ke fama da matsalar tattalin arziki.

READ MORE: SOURCE LEGIT.NG
No comments:
Write Comments