Tuesday

Home Mai rabo ka samu: Hukumar kwastam ta bude sahafin daukan sabbin ma'aikata 3,200
Ya ce za a bude shafin ne na tsawon sati uku domin masu sha'awar aiki da hukumar kwastam a matakin manyan jami'ai su cike bayanansu tare da aika takardun su.
Nigerian custom, aikin custon

Kanal Ali, wanda mukaddashin mataimakinsa mai kula da sashen albarkatun mutane, Sanusi Umar, ya wakilta, ya bayyana hakan ne a yau, Talata, a Abuja. Ya ce daukan sabbin ma'aikatan ya biyo bayan amincewar kwamitin zartar wa na gwamnatin tarayya, kuma za a dauki ma'aikatan ne bisa tsarin hukumar raba dai-dai a aiyukan gwamnatin tarayya (FCC).

Da ya ke karin bayani a kan daukan sabbin ma'aikatan, Kanal Ali ya ce za a dauki ma'aikata 800 a matakin 'superintendent', yayin da za a dauki mutum 2,400 a bangaren 'Insfekta' da bangaren kananan mataimaka.

Ya ce, domin tabbatar da cewar 'yan Najeriya sun samu labarin daukan ma'aikatan da hukumar za tayi, an saka sanarwa a manyan jaridun kasa guda 7.

Ya bayar da adireshin da masu sha'awar neman aiki zasu bayar da bayanansu kamar haka:

www.vacancy.customs.gov.ng.

Kazalika ya gargadi masu neman aiki da hukumar ta kwastam da su kula da 'yan damfara, wadanda zasu karbi kudinsu da sunan za su samar masu aiki.

READ MORE :  Da dumi dumi : Amina amala ta maka gabon a kotu ta nemi diyyar naira miliyan 50

No comments:
Write Comments