Wednesday

Home › › Tuna baya: Abubuwan da Sa'adu Zungur ya fada a kan makomar arewa shekaru 61 da suka wuce
A yayin da arewacin Najeriya ke fama da kalubale daban-daban da suka hada da na tsaro, tabarbarewar tarbiyya da lalacewar tattalin arziki, Legit.ng tayi waiwaye domin kawo maku kalaman fasihin mawaki, Marigayi Sa'adu Zungur, a cikin daya daga cikin waken sa mai taken: 'Arewa Jamhuriyya Ko Mulukiyya? ".
Sa’adu Zungur (1914-- 1958): Arewa Jamhuriya Ko Mulukiya?
“Matukar a arewa da karuwai,
‘Yan daudu da su da Magajiya.
Da samari masu ruwan kudi,
Ga mashaya can a gidan giya.
Matukar ’ya’yan mu suna bara,
Titi da Loko-lokon Nijeriya.
Hanyar birni da na kauyuka,
Allah baku mu samu abin miya.
Sun yafu da fatar bunsuru,
Babu mai taryonsu da dukiya.
Babu shakka’ yan kudu za su hau,
Dokin mulkin Nijeriya.
Marigayi Sa'adu Zungur
In ko ’yan kudu sunka hau,
Babu sauran dadi, dada kowa zai
sha wuya.
A Arewa zumunta ta mutu,
Sai karya sai sharholiya.
Camfe-camfe da tsibbace tsibbacen,
Malaman karya ’yan damfara.
Sai karya sai kwambon tsiya,
Sai hula mai annakiya.
Ga gorin asali da na dukiya,
Sai kace dan annabi fariya.
DUBA WANNAN: Abun kunya: An bawa hammata iska tsakanin Abdullahi Abbas da Kwankwaso
Jahilci ya ci lakar mu duk,
Ya sa mana sarka har wuya.
Ya sa mana ankwa hannuwa,
Ya daure kafarmu da tsarkiya.
Bakunan mu ya sa takunkumi,
Ba zalaka sai sharholiya.
Wagga al’umma mai za ta yo,
A cikin zarafofin duniya.
Kai Bahaushe ba shi da zuciya,
Za ya sha kunya nan duniya.
“Mu dai hakkin mu gaya muku,
Ko ku karba ko ku yi dariya.
Dariyar ku ta zam kuka gaba,
da nadamar mai kin gaskiya.
Gaskiya ba ta neman ado,
Ko na zakin muryar zabiya.
Karya ce mai launi bakwai,
Ga fari da baki ga rawaya.
Ga kore ga kuma algashi,
toka-toka da ja sun garwaya”.
No comments:
Write Comments