Sunday

Home Rikicin Kano: Gwamna Ganduje ya ba Sarki Sanusi II zabi guda 3
Watakila za a kai Sarkin Kano Muhammad Sanusi II a gaban kotu a game da yadda aka batar da kudin Masarautar kasar a lokacin da ya dare kan gadon sarauta bayan rasuwar Marigayi Sarki Ado Bayero.
Ganduje and Sunusi

Daily Trust ta rahoto yadda Sarkin na Kano ya samu matsala da Gwamna mai girma Abdullahi Umar Ganduje. A cikin makon da ya gabata ne hukumar da ke binciken satar dukiyar gwamnati a jihar Kano ta taso fadar Kano a gaba.

Hukumar tana zargin Masarautar da barnar dukiya don haka ta soma bincike bayan gwamnati ta kuma kirkiro wasu sababbin Masarautu, wanda tuni an nada masu Sarakuna yanzu haka. A cikin mako guda dai duk aka yi wannan.

KU KARANTA: Halittu Guda 5 Da Allah Yayi musu baiwa da tsayin Rayuwa.

A makon jiya ne Isa Sanusi Bayero, wanda shi ne tsohon Sakataren Sarkin Kano, ya bayyana a gaban hukumar da ke binciken fadar Kano. Ana zargin Sarki Sanusi II ne da wawure duk makudan kudin da aka bari cikin asusun fadar.

Rahoton na Daily Trust cewa bayan Sarki ya samu labarin cewa ana shirin maka sa gaban kotu idan an gama bincike ne yayi maza ya ruga wajen Aliko Dangote, wanda ya nemi ya nema masa alfarma wajen gwamna mai-ci Ganduje.

KU KARANTA: Bidiyo : Gwamnan Kano Dr, Abdullahi Umar Ganduje Yayin Tabbatar da Nadin sarakunan Yanka. 

Gwamnan ya fadawa Aliko Dangote cewa Sarki Sanusi II yana da zabi har 3; ko kuma ya sauka daga kan gadon sarauta da kan sa, ko kuma a kirkiro sababbin Masarautu a jihar, ko kuma a tsige sa daga kan karagar mulki da karfin tsiya.

A karshe dai gwamnatin Kano ta kirkiro sababbin Masarautu 4 wanda kuma tuni aka nada masu Sarakuna. Ba don sa bakin Aliko Dangote ba, ana tunanin cewa da tuni Mai girma Abdullahi Ganduje ya tsige Sarki Sanusi daga kan mulki.
Sai dai kuma ana tunanin cewa Ganduje zai iya aika Sarki Sanusi II zuwa wata Masarauta a jihar, sannan ya maye gurbin sa da wani daga cikin sabbabin Sarakunan da aka nada a cikin kwananin nan.

SOURCE  LEGIT.NG
No comments:
Write Comments