A cigaba da sauraran qarar da jam’iyyar PDP ta shigar a gaban kotun sauraran qararakin zave da ke Katsina an fara gabatar da shaidu dangane da rashin ingancin zavan gwamnan da ya gabata wanda jam’iyyar PDP ta yi zargin an tafka maguxi.
Sanata Yakubu Lado danmarke na jam’iyyar PDP suka shigar da qarar inda suke qalubalantar nasarar da gwamna Aminu Bello Masari ya samu wanda hakan ya qara tabbatar da shi a matsayin zavavan gwamna a karo na biyu a qarqashin jam’iyyar APC.
DUBA WANNAN : Sunayen Tsaffin gwamnonin APC 3 da Buhari zai nada ministoci.
Lauya ya qara da cewa akwai abubuwa mahimahimcin a wannan shari’a da ya kama jama’a su sami wanda da shi ne suke sa ran za su samu nasaraa wajan wannan shari’a ake fafatawa.
Sai dai kuma da muka tuntuvi vangaran gwamnati wanda sune aka yi qara domin jin martanin da za su maida dangane da wannan batu na rashin cikakun takardun shaidar Ilimi da suke zargin gwamna Masari. Xaya daga cikin jagorarin wannan shari’a a vangaran gwamnati Ernest Obunidike ya ce wanda muke karewa yana da takardun yin takarar gwamnan jihar Katsina kuma ya yi takara ya ci zave ya sake yi ya ci zave saboda haka ya cancanta.
Wannan shari’a dai na cigaba da xaukar hankali musamman yadda aka zargin cewa xan takarar jam’iyyar PDP Sanata Yakubu Lado Xanmarke ya sayar da takarar ta sa tun kafin zave zargin da ke neman ya zama shafa labari shuni.
SOURCE Leadershiphausa

Sai dai lauyan da ke jagorantar wannan shari’a a vangaran jam’iyyar Adawa ta PDP Gordy Uche ya bayyanawa manema labarai cewa bisa ga yadda suke ganin wannan shari’a na tafiya akwai alamu nasara so sai. “Muna da qyaqqyawar fatan cewa za a samu nasara kai tun daga ranar da muka shigar da wannan qara muke da qyaqqyawar fatan cewa akwai nasara a wannan shari’a da ake yi kuma za a samu canji na yi maku alqawarin cewa zaku ga canji ba da jimawa ba”. Inji Gordy Uche
Lauya ya qara da cewa akwai abubuwa mahimahimcin a wannan shari’a da ya kama jama’a su sami wanda da shi ne suke sa ran za su samu nasaraa wajan wannan shari’a ake fafatawa.
“Abu mai matuqar mahimmacin da nake so a sani shi ne, Bangaran da wannan qara ta ya shafa wanda yake da mahimmanci a garemu, wanda kuma muke yawan nanawa tun lokacin da muka shigar da wannan qarar shi ne, wanda muke qara wato gwamna Aminu Bello Masari baya da cikakkun takardun ilimi da ya kamata ya tsaya takarar gwamnan jihar Katsina” inji shi.
Sai dai kuma da muka tuntuvi vangaran gwamnati wanda sune aka yi qara domin jin martanin da za su maida dangane da wannan batu na rashin cikakun takardun shaidar Ilimi da suke zargin gwamna Masari. Xaya daga cikin jagorarin wannan shari’a a vangaran gwamnati Ernest Obunidike ya ce wanda muke karewa yana da takardun yin takarar gwamnan jihar Katsina kuma ya yi takara ya ci zave ya sake yi ya ci zave saboda haka ya cancanta.
Ya qara da cewa “Abu na biyu shi ne ba mu da buqatar yin musayar maganganu da lauyan wanda ya yi qara saboda maganar tana gaban kotu har yanzu, idan har gaskiya ne zargin da suke yi su kare shi a gaban kotu amma ba za mu yi masanyar kalamai da su ba tukuna”.
Wannan shari’a dai na cigaba da xaukar hankali musamman yadda aka zargin cewa xan takarar jam’iyyar PDP Sanata Yakubu Lado Xanmarke ya sayar da takarar ta sa tun kafin zave zargin da ke neman ya zama shafa labari shuni.
SOURCE Leadershiphausa
No comments:
Write Comments