Showing posts with label addini. Show all posts

Thursday

Bidiyo : Wata Sabuwa: Azumin Sitta 6 Shawwal Bidi'a Ne Inji Dr Ahmad Gumi
Dr, Ahmad Gumi Yakaranto A cikin Karatun littafin Imam Malik Cewa Azumin Shida Bayan Ramadan Bidi'a ce.
Asali ma Hadisin Da Ake Kafa Hujja Dashi Ba Ingantacce Bane, cewar ml gumi.
Shahararren Malamin addinin Islama dake garin Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya bayyana cewa azumin guda shida da Musulmai ke yi bayan kammala azumin watan Ramadana, a cikin watan Shawwal bai inganta ba, kuma bidi’a ne.
Gumi ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo daya watsa a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook a ranar Laraba, 5 ga watan Yuni, inda yace a fahimtar babban Malamin addinin Musulunci, Imamu Malik, Azumin Sittu Shawwal bai inganta ba, sahabbai, tabi’ai, duk basu yi ba.
Ga Bidiyon Nan Kasa
A cigaba da jawabinsa, Sheikh Gumi ya bayyana cewa, uwar muminai, matar Annabi Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, Aisha, bata rama azumin watan Ramadan sai a watan sha’aban ma, ma’ana da azumin shawwal ya inganta da an ruwaito tayi.
Bugu da kari Gumi ya bayyana ma masu fahimtar sahihancin hadisin dake kira ga azumin sitta shawwal cewa Malik ya san hadisin, kuma Malik a garin Madina ya rayu kafin Annabi ya cika shekaru 150 da mutuwa, don haka ya san hadisin, amma hadisin bai inganta ba. Daga karshe Malamin ya bayyana cewa akwai raini ga Imamu Malik cikin kiran mutane su yi azumin sitta Shawwal, saboda dama a ko ina akwai masu da’a da bin nagaba da kuma masu yin bore ga nagaba.
Asali ma Hadisin Da Ake Kafa Hujja Dashi Ba Ingantacce Bane, cewar ml gumi.
Shahararren Malamin addinin Islama dake garin Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya bayyana cewa azumin guda shida da Musulmai ke yi bayan kammala azumin watan Ramadana, a cikin watan Shawwal bai inganta ba, kuma bidi’a ne.
Gumi ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo daya watsa a shafinsa na kafar sadarwar zamani ta Facebook a ranar Laraba, 5 ga watan Yuni, inda yace a fahimtar babban Malamin addinin Musulunci, Imamu Malik, Azumin Sittu Shawwal bai inganta ba, sahabbai, tabi’ai, duk basu yi ba.
Ga Bidiyon Nan Kasa
Bugu da kari Gumi ya bayyana ma masu fahimtar sahihancin hadisin dake kira ga azumin sitta shawwal cewa Malik ya san hadisin, kuma Malik a garin Madina ya rayu kafin Annabi ya cika shekaru 150 da mutuwa, don haka ya san hadisin, amma hadisin bai inganta ba. Daga karshe Malamin ya bayyana cewa akwai raini ga Imamu Malik cikin kiran mutane su yi azumin sitta Shawwal, saboda dama a ko ina akwai masu da’a da bin nagaba da kuma masu yin bore ga nagaba.
Yadda Ake Chatting Da Bluetooth ba tare da Data Connection ba : Android tutorial https://t.co/7aPmfgvBKB https://t.co/7aPmfgvBKB June 06, 2019 at 11:09AM
— AREWASOUND (@Arewasound) June 6, 2019
Monday

Yanzu Yanzu: An ga wata, gobe take Sallah
Ta tabbata gobe Talata take Sallah yayin da sabon jaririn watan Shawwal ya bayyana a kasar Saudiya.
A gobe da ta kasance Talata, 4 ga watan Mayun 2019, za a gudanar da shagulgula na bikin karamar Sallah a kasar Saudiya yayin da jaririn watan Shawwal ya bayyana a Yammacin yau bayan an kai azumi na ashirin tara.
Ko shakka ba bu addinin musulunci ya shar'anta yin azumin farilla na tsawon kwanaki ashirin da tara ko kuma talatin a watan Ramadana inda kuma ake gudanar da bikin karamar Sallah watau Eid Ul Fitr yayin da watan jinjirin watan Shawwal ya bayyana.
A yayin da al'ummar Musulmi ke kirdado tare da laluben bayyanar sabon watan Shawwal a Najeriya, a yau ne za a kai azumi na 29 a wannan mafificin wata na Ramadana da aka fara gudanar wa tun a ranar 6 ga watan Mayun 2019.
KARANTA KUMA: Kwana Casa'in - Kashi Na Tara 9 | Cigaban shiri.
Jaridar Legit.ng ta ruwaito, Sarkin Musulmi Sultan na Sakkwato, Alhaji Abubakar Muhammad Sa'ad, ya hori al'ummar musulmi a Najeriya da su zura idanu tare da fita wajen laluben jaririn Shawwal daga yau daren Talata.
An ga wata
Hakika gobe ne 1 ga watan Shawwal na shekarar Alif dubu daya da dari hudu da arba'in bayan hijirar fiyayyen Halitta daga birnin Makkah zuwa Madinah.A gobe da ta kasance Talata, 4 ga watan Mayun 2019, za a gudanar da shagulgula na bikin karamar Sallah a kasar Saudiya yayin da jaririn watan Shawwal ya bayyana a Yammacin yau bayan an kai azumi na ashirin tara.
Ko shakka ba bu addinin musulunci ya shar'anta yin azumin farilla na tsawon kwanaki ashirin da tara ko kuma talatin a watan Ramadana inda kuma ake gudanar da bikin karamar Sallah watau Eid Ul Fitr yayin da watan jinjirin watan Shawwal ya bayyana.
A yayin da al'ummar Musulmi ke kirdado tare da laluben bayyanar sabon watan Shawwal a Najeriya, a yau ne za a kai azumi na 29 a wannan mafificin wata na Ramadana da aka fara gudanar wa tun a ranar 6 ga watan Mayun 2019.
KARANTA KUMA: Kwana Casa'in - Kashi Na Tara 9 | Cigaban shiri.
Jaridar Legit.ng ta ruwaito, Sarkin Musulmi Sultan na Sakkwato, Alhaji Abubakar Muhammad Sa'ad, ya hori al'ummar musulmi a Najeriya da su zura idanu tare da fita wajen laluben jaririn Shawwal daga yau daren Talata.
Tips to Growth Your Hair Faster - 1inch in a Week https://t.co/ODiJs2ISpN https://t.co/ODiJs2ISpN May 31, 2019 at 08:38PM— AREWASOUND (@Arewasound) May 31, 2019
Tuesday

Kungiyar Izala ta gabatar da muhimmiyar bukata a gaban gwamnati
Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS) ta bukaci Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi da su karfafa kokarinsu wajen ganin sun samar da isasshen wutar lantarki a fadin kasar.
Kungiyar ta cigaba da yin kira ga gwamnati a dukkan matakai da su mayar da hankali wajen samar da wutan lantarki a yankunan karkaran da ke kasar don inganta samar da ayyuka ga al’umma tare da inganta tattalin arzikin kasar.
Kungiyar ta bayyana kiran ne a taro na kasa na mako 26 na shekara shekara da kungiyan ta gudanar a Jos a ranar Talata, 30 ga watan Afrilu.
Sakon na dauke da sa hannun babban mai gudanarwa na kungiyar na kasa a taro da gasar alkur’ani, Hafiz Aminu Yusuf.
KU KARANTA KUMA: Dalilin Da Yasa Buhari Ya Kulle Ni A Kurkuku – Lamido Adamawa.
Har ila yau ya bukaci hukumomin tsaro dasu karfafa ayyuka wajen kau da laifuffuka a kasan don guje ma batanci ga martabar kasan.
Kumgiyar ta kuma roki gwamnatin tarayya da gwamnatin jihohi da su tabbatar an cimma buri, adalci da gaskiya wajen nadin alkalai a kotun Najeriya.

Friday

Manyan likitoci Biyar sun shigo Nigeria don Duba lafiyar Zakzaky.
A iya cewa wannan shine karon farko da gwamnatin Nijeria ta yarda wasu likitocin kasar waje samun damar ganawa da shugaban yan shi'a, Ml. Ibrahim Zakzaky domin duba lafiyarsa tun bayan kamashi da hukuma tayi a shekarar 2015.
Majiyar ta ruwaito cewa likitocin sun samu damar ganawa da ml. Zakzaky ne bayan samun umarni daga Alkalin wata babbar kotu dake garin Kaduna, wanda ke sauraron karar da gwamnatin jahar Kaduna ta shigar da Al-Zakzaky.
Duba da halin rashin lafiya da shugaban yan shi’an yake aciki ne yasa Alkalin yayi umarni ga hukumar tsaron sirri ta dss wadanda ke rike da Zakzaky da matarsa, dasu gaggauta gayyato masa likitocin da yake so don su duba lafiyarsa data matar sa.
Tunda a farko dai lauyan Al-Zakzaky, Femi Falana ne ya nemi wannan bukata daga Alkalin kotun, bayan ya bata bayanin cewa har yanzu Zakzaky da matarsa suna fama da matsanancin ciwo sakamakon raunuka da suka samu daga harbin bindiga da Sojoji suka yi musu a yayin da suke kokarin kamasu a shekarar ta 2015.
Haka kuwa aka yi, hukumar DSS ta bi umarnin kotu, inda ta baiwa likitocin damar ganawa da Zakzaky da matarsa a ranar Alhamis, 25 ga watan Afrilu a inda suke tsare dasu, sai dai basu bayyana ma manema labaru wata magana game da abin dake damun Malamin ba.
KU KARANTA: Yadda ake mayar da hakora suyi haske ƙal-ƙal a cikin awa daya
Idan za’a tuna a can kwanakin baya da dadewa an yi ta yada jita jitan Malamin ya mutu a hannun DSS, inda daga bisani hukumar DSS ta karyata batun, har ma ta bayyanshi ga manema labaru, kuma ya bayyana musu cewa yana samun kulawa, amma baya jin dadi sosai.
MAJIYA : LEGIT.NG

Tofa - An kayyade kudin sadakin aure a kafatanin kasar nan
Wani babban Malamin addinin Musulunci a kasarnan, Dr Abdulhameed Shu'aib Agaka, ya bayyana N13,438 a matsayin ainahin kudin sadakin aure a addinin musulunci.
Sannan ya kara da cewa, addini ya halatta, idan miji yana da hali ya biya fiye da yanda shari'a ta bayyana.
A lokacin da yake bayani, a gidan radiyo a garin Ilorin dake jihar Kwara, Dr. Agaka, wanda yake tsohon Malami ne a jami'ar Bayero dake Kano, yace duk wani aure da aka yi shi ba tare da an biya sadaki ba, to bai hallata ba a musulunci.
KU KARANTA: (Music Mp3) - Uban Abba Zama Daram - New song by Rarara&Ado gwanja - Download now.
Miji shine yake bada sadaki ga mata, domin nuna girmamawa a gareta, da kuma kara bada tabbacin cewa duk wasu lamura nata sun dawo kanshi.
Sannan ya kara da cewa a musulunce ana iya amfani da shanu, filaye, gonaki, zinare da wasu abubuwa dai masu muhimmanci wurin biyan sadaki.
A karshe Malamin ya shawarci Musulmi da su dinga bin dokar da Allah da Manzonsa suka gindaya, musamman ma ta fannin aure, domin kaucewa zinace-zinace.

Kotu ta daga sauraron karar El-Zakzaky har sai baba-ta-gani
Wata babbar kotun jihar Kaduna karkashin mai shari'a Gideon Kurada ta daga sauraron karar da gwamnatin jihar Kaduna ta shigar da shugaban kungiyar mabiya shi'a (IMN), Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, har sai baba-ta-gani.
Alkalin kotun ya bayyana cewar ya daga sauraron karar ne ba tare da saka ranar dawowa ba saboda nadin da aka yi ma sa a matsayin alkali a kotun sauraron korafe-korafen zaben shugaban kasa da na mambobin majalisar tarayya. Tun a shekarar 2015 gwamnati ta kama El-Zakzaky tare da matar sa, Zeenat, biyo bayan wata kazamar arangama tsakanin mabiyansa da dakarun sojin Najeria a garin Zaria dake jihar Kaduna.
Rahotann sun bayyana cewar an kashe mabiya shi'a kimanin su 300 yayin artabu da dakarun sojin. Ana tuhumar El-Zakzaky da matar sa da hada baki domin aikata kisa, taro ba bisa ka'ida ba, da tayar da tsugune tsaye da sauran su.
DUBA WANNAN :- Kano: Jami'an tsaro sun bawa hammata iska a cibiyar tattara sakamakon zaben gwamna.
Da yake gana wa da manema labarai bayan yanke hukuncin kotun, Femi Falana, lauyan dake kare wadanda ake tuhuma, ya ce wadanda yake karewa basu samu damar bayyana a gaban kotu ba saboda yanayin rashin koshin lafiya da su ke ciki. Ya ce tun ranar 14 g watan Disamba na shekarar 2015 da aka rufe su, ba a bawa lafiyar su kulawa ba, tare da bayyana cewar su na matukar bukatar a duba lafiyar su. Read more:

Kalli zakakuran da zasu wakilci Najeriya a gasar Al-Qur’ani ta duniya
An sanar da jerin sunayen zakakuran daliban Najeriya kuma mahaddata Al-Qur’ani da zasu wakilci Najeriya a gasar haddar Qur’ani ta duniya gaba daya da zata gudana a kasar Turkiyya, a watan Mayun shekarar 2019.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin wadanda zasu wakilci Najeriya a fannin Maza akwai Alaramma Abdurrahman Bunu daga jahar Bornu, da kuma Yusuf Yahaya daga jahar Edo, dukkaninsu sun ciri tuta wajen rera karatun Qur’ani da tajwidi.
KU KARANTA: Dalilin da ya sa ba mu yi abin da Buhari yace a Kano ba – inji Kwankwaso
Kungiyar cigaban Musulunci ta Najeriya, IPIN tare da hadin gwiwar gidauniyar Diyanet ta kasar Turkiyya ce suka shirya gasar sharan fagge a Najeriya, wanda ya gudana a babban Masallaci dake babban birnin tarayya Abuja, daga nan aka zabi wadanda zasu wakilci Najeriya.
Sakamakon gasar da aka kammala a Abuja ya nuna Alaramma Bunu ne yazo na daya a haddar izu sittin, yayin da Ismail Umar daga jahar Neja, da Abdulmalik Ahmad daga jahar Ogun suke bi masa.
Haka kuma Malam Yahaya yazo na daya a haddar Tangeemi, yayin da Ibrahim daga jahar Borno, da Ajmul Nura Shema daga jahar Katsina suka rufa masa baya a matsayin na biyu da na uku.
A bangaren Mata kuwa, Maimuna Abdurrahman daga Abaji ce ta zama zakakura a haddar izu 5, yayin da Aisha Sani daga Kuje ta lashe gasan haddar izu 10, Fauziyya Shehu daga AMC ta lashe haddar izu 20, Halima Muhammad Gwagwalada ta lashe izu 40, sai Surayya Muhammad ta lashe izu 60.
Dayake nasa jawabin, shugaban IPIN, Dakta Muhammad Kabir Adam ya bayyana cewa sun fara shirya gasar ne a shekaru hudu da suka gabata don karfafa ma daliban ilimi haddan Al-Qur’ani da sauti mai dadi da kuma tajwidi.

Subscribe to:
Posts (Atom)