Farfesa Femi Williams wanda sanannen likitan Anatomic Pathology na Landan da Ireland ya bayyana cewa shugaba Buhari na fama da Anemiya.
Farfesa Willaims yayi wanna bayani ne a wata hira da jaridar The Nation inda yace:
“Yanzu mun san abinda ke damun Buhari bisa ga gwajin da akayi kuma yana nuna cewa yana fama da Anemiya.
“An wallafa sakamakon gwajinsa a ranan 26 ga watan Fabrairu, 2017 a jaridar The Nation inda ak fadi cewa an kara masa jinni.
“Amma sakamakon da aka samu daga baya ya nuna cewa ya samu sauki kuma ya daina cutan Anemiya.
“Samun karfinsa bayan Karin jinni da kuma dawowansa ya nuna cewa an samu nasara wajen warkar da Anemiyan.”
KARANTA WANNAN :- WAKAR RARARA NEW (BARKA DA ZUWA BABA BUHARI) : up dated
Ana sa ran dai ranan Litinin, Shugaba Muhammadu Buhari zai koma bakin aiki.
No comments:
Write Comments