Showing posts with label kasuwanci. Show all posts
Showing posts with label kasuwanci. Show all posts

Sunday

Yadda farashin kayan masarufi suka kasance yayin da ake gab da shiga watan Azumi

Binciken kamfanin dillancin labarai na kasa cikin kasuwannin Mil 12, Oke Odo, Oyingbo da Iddo da ke jihar Legas, ya tabbatar da cewa farashin kwando guda na tumatir da ake sayarwa N5000 makonni biyu da suka gabata ya tashi zuwa N12,000.
Watan Azumi: Kayan masarufi sun tashi a jihar Legas.

Kazalika farashin kwando guda na tattasai da aka saba sayarwa a kan N6,000 ya tashi zuwa N12,000. Farashin attaruhu da farashin sa makonni biyu ya ke a kan N5,000, ya koma zuwa N9,000 kamar yadda binciken ya tabbatar.

Wani jagoran kungiyar masu sayar da kayan gwari a kasuwar Mil 12, Haruna Muhammad, ya alakanta bazara da kuma tsadar sufuri da hauhawar farashin kayan miya. Sai dai ya ce duk wannan tsada an samu saukin farashin kayan masarufi idan an kwatanta da farashin su shekaru biyu da suka gabata.

A sabanin haka, an samu sauki na farashin wasu kayan masarufi irin su Albasa, Man ja da kuma Man gyada kamar yadda wani mai sayar da wake a kasuwar Iddo, Musa Yahaya ya bayar da shaida.

KARANTA KUMA: Ingantaccen Bude Baki Ga Mai Azumi ;>>>> 

Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan da jaridar Legit.ng ta ruwaito, Sarkin Musulmi Sultan na Sakkwato, Alhaji Muhammad Abubakar Sa'ad, ya nemi daukacin al'ummar Musulmi na Najeriya da su sanya idanun lura wajen laluben sabon watan Ramalana na shekarar 1445.

SOURCE LEGIT.NG

Thursday

An fara baje kolin kayan yawon bude ido a Ankara.

An fara baje kolin kayan yawon bude ido a Ankara.




A zauren helkwatar kungiyar 'yan kasuwa ta Ankara an fara bajekolin kayayyakin harkokin yawon bude ido na shekarar 2017.

Akwai kamfanonin Turkiyya da na kasashen waje da ke halartar baje kolin inda kasar Arewacin Cyprus ta zama babbar bakuwa sai lardin Diyarbakır na Turkiyya a matsayin bako na musamman.

Kasuwar za ta dauki tsawon kwanaki 4 inda larduna 42 tare da kasashe 7 suke halarta.

Baje kolin za ta samar da damar karfafa wa tare da hada 'yan kasuwa.