Showing posts with label labaran abin Al'ajabi. Show all posts
Showing posts with label labaran abin Al'ajabi. Show all posts

Thursday

Bidiyo : Wata mata ta kashe mijinta ta yi yunkurin kone gawarsa.

Wani ma'abocin amfani da dandalin sada zumunta  ya yada labarin wata mata da ta kashe mijinta sannan ta saka wa gawarsa wuta bayan sun yi wani kazamin fada.
na Facebook

A cewar wanda ya yada labarin, lamarin ya faru ne a jihar Bayelsa, sannan ya kara da cewa lamarin ya jawo hankalin makwabtan ma'auratan wadanda suka kira 'yan sanda. Ya kara da cewa, jami'an 'yan sanda sun zo sun dauki gawar mijin sannan sun tafi da matar.

Ko a kwanakin baya wata Mata ta yi yunkurin Kashe Mijinta Ta Hanyar Burma Masa Wuka A Ciki Saboda Zai Yi Mata Kishiya Ana zargin wata mata mai suna Amina Banaga Maru dake garin Gusau babban birnin jihar Zamfara da niyar hallaka mijinta ta hanyar soka masa wuka a ciki har sau uku.

Lamarin wanda ya auku a RANAR Litinin, 24 ga watan Yuni, bincike ya nuna cewa matar ta yi niyar halaka mijin nata ne saboda tsantsar kishi. Bayanan da muka samu sun tabbatar mana da cewa ana zargin Amina ta yi wa mijin nata wannan danyen aikin ne saboda niyyar da yake da ita na yi mata kishiya.

GA BIDIYON NAN KASA


Saturday

Yanzu Yanzu: Jirgin sama ya kwace ya shiga jeji yayin sauka a Fatakwal ; Hotuna

Wani jirgin sama na kamfanin Air Peace ya ketare titin sa a filin tashi da saukan jirage na Fatakwal da ke jihar Rivers yayin da ake ruwan sama da bakin kwarya.


A cewar daya daga cikin fasinjan da ke jirgin, lamarin ya faru ne a yayin da jirgin ke sauka a filin saukan jiragen.


Fasinjojin jirgin Air Peace yayin da ake tallafa musu fitowa daga jirgin da ya shige daji a Fatakwal .

DUBA WANNAN : Rikici : Iran ta tarwatsa Jirgin leƙen Asiri na Amurka.  

Jirgin ya yi birki a cikin daji kimanin mita 200 daga titin sa. Wani shaidan ganin ido ya ce an fitar da dukkan fasinjojin da ke cikin jirgin an koma da su wurin da ya dace jirgin ya tsaya tun farko.

Fasinjojin jirgin Air Peace yayin da ake tallafa musu fitowa daga jirgin da ya shige daji a Fatakwal Source: legit.ng.

Monday

Yadda Mohammed Morsi ya yanke jiki ya fadi matacce a kotu

Tsohon shugaban kasar Misra (Egypt), Mohammed Morsi, da sojoji suka yi wa juyin mulki a shekarar 2013, ya mutu a kotu, kamar yadda gidan Talabijin na kasar ya rawaito.

Sashen Turanci na jaridar BBC ya rawaito cewar Morsi ya suma a cikin kotu inda ake tuhumarsa da aikata laifin satar muhimman bayanan sirri (Espionage). Shekarunsa na haihuwa 67.

An hambarar da gwamnatin Morsi bayan shekara daya da hawansa mulki biyo bayan wata zanga-zanga mai zafi.

Tun bayan lokacin yake tsare a kotu.
Morsi ne zababben shugaban kasar Misra na farko, ya hau mulki ne bayan an tursasa tsohon shugaban kasar, Hosni Mobarak, yin murabus.

Bayan an tunkude Morsi daga kan mulki, hukumomin kasar Misra sun shiga farautar magoya bayansa da 'yan kungiyarsa ta 'yan uwa Musulmi (Muslim Brotherhood).

Saturday

Subhanallahi , Yadda wani malami ya rataye kanshi a kano.



Jami'an hukumar 'yan sandan jihar Kano sun bada sanarwar mutuwar wani malamin makaranta, mai suna Femi Oguntumi dake zaune a unguwar Dakata, wanda aka tabbatar da cewa ya kashe kanshi ne.
Har yanzu dai ba a gano dalilin da ya sanya malamin kashe kanshi ba.

Mutumin mai shekaru 40 a duniya, wanda yake ma'aikaci ne a Kwalejin Karish, dake unguwar Kawaji, an iske shi ya rataye kanshi a jikin rufin dakin shi.

KU KARANTA: A Kano: Budurwa ta kashe kanta saboda an saki Mahaifiyarta. 

Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar, DSP Haruna Abdullahi, ya tabbatarwa da manema labarai faruwar lamarin, ya ce yanzu haka sun kai gawar marigayin asibitin Murtala domin gabatar da bincike akan shi.

Ya kara da cewa jami'an su sun fara gabatar da bincike akan dalilin da yasa Femi ya rataye kanshi.

Ba wannan ne karo na farko da ake samun irin wannan lamari na kisan kai ba, a lokuta da dama akan iske mutum ya sha guba ko ya rataye kanshi, inda wasu suke alakanta hakan da yawan damuwa da kuma bakin talauci da mutane ke fama dashi a wannan lokacin.

Thursday

Kano: Budurwa ta kashe kanta saboda an saki Mahaifiyarta

Wata budurwa mai suna Sadiya Shehu, 'yar shekaru 17 a duniya wacce ke zaune a unguwar Tudun Murtala dake karamar hukumar Nasarawa cikin jihar Kano, ta kashe kanta saboda wani sabani da ya shiga tsakanin mahaifanta, wanda har yayi sanadiyyar rabuwarsu. Sadiya ta rasu bayan ta sha madarar fiya-fiya, wanda yake ajiye a dakin mahaifiyarta saboda kashe sauro da kwari

A yayin da jaridar Aminiya ta kai ziyara gidan da lamarin ya faru a unguwar ta Tudun Murtala, Aminiya ta tarar da dumbin mutane suna tururuwar zuwa gidan don yin jaje ga iyayen yarinyar.

Malam Shehu Lawan shi ne mahaifin marigayiya Sadiya, ya bayyana cewa Sadiya ta kashe kanta ne saboda 'yar karamar malsata da ta shiga tsakaninsa da mahaifiyarta, inda kuma daga baya suka gano bakin zaren a tsakaninsu.
"Na samu matsala da mahaifiyarta, inda hakan ya batawa Sadiya rai, saboda ta yi ta faman kuka akan wannan matsala dake tsakani na da mahaifiyarta, daga baya naje na rarrasheta akan cewa komai ya wuce munyi sulhu.
Duba wannan; Yadda Ake Connecting Na Android Xender Da Computer. : Android Tutorial 2020  
"Safiya nayi na fita wurin aiki na bar Sadiya tare da 'yan uwanta a gida. Ina wurin aiki sai aka kirani a waya ake fada mini cewa an wuce da ita asibiti. Likitoci sun yi iya bakin kokarinsu, amma da yake Allah ya kaddara cewa babu sauran kwana ta rigamugidan gaskiya."


Da jaridar Aminiya ta tambayi Malam Shehu ko an tsayarwa da Sadiya miji, sai ya ce tana da wanda yake nemanta, domin kuwa har yazo sunyi magana kuma yayi alkawarin cewa zai turo magabatansa da zarar mahaifinsa ya dawo daga kasar Saudiyya.

SOURCE LEGIT.NG 

Wednesday

Kotu ta yankewa malamin Shi'a hukuncin dauri na shekaru 2 a gidan yari.

Wani malamin akidar Shi'a kuma haifaffen kasar Iran ya yankar wa kansa tikitin zama a gidan Dan Kande yayin da wata kotun kasar Faransa ta yanke masa hukuncin dauri na shekaru biyu bayan sabawa hukumar shige da fice.

Kotun kasar Faransa ta yanke wa malam Muhammad Baraeikechi Ghaleshi hukuncin zaman gidan sarka na tsawon shekaru biyu bayan ta same shi da laifin taimakawaa 'yan ci-rani ketarewa zuwa kasar Ingila ta hanyar kananan jiragen ruwa.

Kazalika kotun ta yankewa wani abokin tarayyar malamin da su ke aikata wannan mummunan harka hukuncin dauri na zama a gidan kaso duk da cewar wa'adin bai kai wanda malamin zai shafe ba wajen bai wa duga-dugan sa hutu.

Bayan gudanar da bincike da sanya idanun lura kan malam Ghaleshi na tsawon watanni kimanin hudu, hukumomin tsaro sun damke shi tare da abokin huldar sa ta aikata wannan babban laifi mai yiwa kowace kasa zagon kasa.

KARANTA KUMA: Duk mai cin kifin ruwan teku ba zai shiga Aljannah ba - In ji wata Malama 

Malam Ghaleshi mai shekaru 39 a duniyar kuma malamin akidar Shi'a a birnin Rouen na kasar Faransa ya shiga hannu tare da abokin huldar sa a watan Afrilun da ya gabata bayan kama su da laifin taimakawa 'yan ci-rani masu fafutikar ketarewa zuwa kasar Ingila daga Faransa.

SOURCE LEGIT.NG

Duk mai cin kifin ruwan teku ba zai shiga Aljannah ba - In ji wata Malamar Coci

Ta ce kifayen dake cikin teku suna da alaka da aljannun ruwa.
Wata shahararriyar Fasto ta fito ta bayyana cewa duk mutanen da suke cin kifi sadin baza su taba shiga aljanna ba idan suka mutu.

Shahararriya Faston ta bayyana hakan ne a lokacin da da take gabatar da wa'azi ga mabiyanta, Limamiyar ta kuma bayyana mabiyan nata cewa duk mutanen da suke cin abubuwan da suka fito daga ruwan teku, irinsu kifi da sauransu to baza su taba shiga aljanna ba idan suka mutu.e

A yadda wani bidiyo da yake ta yawo a shafukan sada zumunta ya nuna.

Limamiyar ta bayyana cewa kifi sadin ya fito daga cikin ruwan teku ne saboda haka yana da dangantaka da aljannun cikin teku.
A karshe Faston ta bayyana cewa duk masu cin irin wannan kifi suna bukatar taimako sosai kafin su shiga aljanna.


Malaman addini dai suna cin karen su babbaka a yankin nahiyar Afirka, inda kowanne yake kokarin nunawa mabiyansa cewa shima yana da wata baiwa ta musamman da Allah ya bashi.


Akwai rahotanni da dama da majiyarmu Legit.ng ta kawo akan malaman addini musamman na addinin Kirista wanda ke nuna yadda malaman ke gabatar da mulki son ransu akan mabiyan nasu.

SOURCE LEGIT.NG