Showing posts with label magada annabawa. Show all posts
Showing posts with label magada annabawa. Show all posts

Sunday

YADDA AKE YIN ISTIKHARA : Neman zabin Allah.

YADDA AKE YIN ISTIKHARA : Neman zabin Allah.



* Neman zabin Allah, wata sallah ce mai raka'o'ibiyu, wacce yinta sunnah ce mu'akkada (sunnahce mai karfi), wacce manzon Allah ya koyar dasahabbansa ita har tazo garemu kamar yadda al-qur'ani ya iso gare mu, sallace da akeyi yayinneman zabin Allah akan wani al-amari kamar;aure, sayan gida/mota aikin gwabnati da daisauransu, sai dai ita wannan sallar ba'ayintaakan abunda yake wajibi ko mustahabbi akan ka;kamar neman zabin Allah akanyin azuminramadan, ko salloli biyar na yini, ko fitarda zakka,azumin alhamis da litimin da dai sauransu.

* Sai dai wurin Mustahabbi ana iyayi idan suncikaro, misali: mutum ne yake son yaje umra karona biyu a lokaci guda kuma yana so yaje watakasa neman ilimi, to yana iya neman zabin Allahakan ya zaba masa wanda yafi Alkhairi a cikin su.

* Hakika Duk wanda ya nemi zabin Mahalicci,kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma yayi azama a cikinlamarin sa, to ba zai yi nadama ba Insha Allah.Domin Allah Madaukakin Sarki ya ce: "Kuma kashawarce su cikin lamarin ka, idan kuma kaquduri aniya, to ka dogara ga Allah" [Ali-Imran :159].

* Hadisi ya gangaro Jabir ibn Abdullah, Allah yakara yarda dashi da Maihaifin saya ce : Manzon Allah (SAW) ya kasance yanakoya mana yin Istikhara (neman zabin Allah) acikin dukkanin al'amura kamar yadda yake koyamana sura daga cikin surorin Alqur'ani. Ya kance: ''Idan dayanku yayi niyyar yin wani al'amarito yayi sallah raka'a biyu ba farillah ba sannanya ce:
"Allaahumma innii astakhiiruka bi ilmika,wa'astaqdiruka bi kudiratika, wa'as'aluka minfadlikal azeem, fa innaka takadiru wala akadiru,wa ta'alamu wala a'alamu, wa anta allamulguyube, Allahumma inkunta ta'alamu anna hazalamri kharal lii fii deenii wama'ashii wa'akibati amrii, aajilihi wa'aajilihi faqadirhu lii wayassirhulii thumma baariklii fiihi, wa'inkunta ta'alamuanna hazar amra sharrullii fii deenii wama'ashiiwa'akibati amrii aajilihi wa aajilihi fasrifhu'anniiwasrifnii anhu wakadur liyal khaira haithu kaana thumma raddini bihi."
Da Harshen Larabci

MA'ANA

"Ya Ubangijina! ina neman zabin ka da ilimin Ka,kuma ina neman tabbatuwar ikon Ka, ina rokanfalalar Ka Mai gaima, Kai ke da iko ni banda shi,Kai ne Masani ni ban san (komai ba) Kai nemasanin abin da yake boye. Ya Ubangiji na! Inkana ganin wannan abu ('sai ya fadi abin da yakeistiharan a kai') shi yafi min a addinina da rayuwata da qarshen lamarina, to ka tabbatar min dashi, ka sauqaqe min sannan ka yi min albarka acikinsa, in kuwa kana ganin wannan abu sharri negare ni a addinina da rayuwata da qarshenlamarina, ka juyar da shi daga gare ni, ni ma kajuyar da ni dagagare shi, ka kudurtarmin da alkhairi sannan kaamintar min da shi" [Bukhari]

* Na tabbata banbanci ya bayyana a fili gama'abota hankulla da tunani tsakanin wannankarantarwar ta shugaban talikai SAW, da Tsirfe-tsirfe da shafi fadin, wasu marubuta littattafankarya don neman kudi, da masu tsibbace tsibbace

* Ita dai wannan Sallah Mustahhabbi ce anso kayita (domin sunnah ce mai karfi, sannan zakasamu lada idan kayi), amma idan bakayi babalaifi.

* Wannan Addu'a ta istarawa ana yin tane bayanka sallame, sallar nan da kayi mai raka'a biyu,duk da wasu malaman na ganin ana karanta tane,bayan tahiya da salatin manzon Allah SAW kafinSallama, domin mafi Al-khairin bijiro da addu'aacikin sallah shine sujuda da bayan tahiya, saidai magana mafi rinjaye shine bayan Sallama.Allah shine Mafi Sani..* Babu Laifi ga mutum ya maimaita istakharasama da daya, hakam ya tabbata daga cikinmagabata, kamar Abdullahi dan zubair Allah yakara yarda dashi yayi istakhara sau ukku.[Muslum - 970].

* Babu wani hadisi daya inganta da yazo dasurorin da ake karantawa, a cikin sallar nemanzabin Allah.

* Haka kuma babu wani hadisi da yazo dagaAnnabi cewa idan mutum yayi istakhara zaiyimafarki ko zaiga wani mutum yana yi masabayani al-amarinsa.

* Babu shakka duk wanda yayi zai samu natsawucikin abunda Allah madaukakin sarki ya zabamasa.

* Ba mafarki ake yi ba kamar yadda mutanedayawa suka dauka, ana ganewa ne da yanayinnutsuwar zuciya, idan aure ne sai kajizuciyar kata qara nutsuwa da yarinyar, idan sana'a ne kakeso ka farasai kaji zuciyar ka tanutsu da sana'ar.

* Za'a iya yin wannan sallah raka'a biyu da rana,ba dole sai da daddare ba, sannan zaka yita nedaga lokaci zuwalokaci har sai ka sami biyan buqata, sannan Anayin tane koda lokacinda aka hana yin sallah ne,idan bukatar hakan ta taso, domin ita tana dagacikin "Nawafilul Asbab" - "Nafiloli masu dalili".

* Wannan kenan don gane da abunda ya shafiSallar neman zabin Allah madau kakin Sarki,Muna fatan Allah ya bamu damar Ayki Abundamuke rubutawa da karantawa Ameen.

ALLAH YA TAIMAKE MU Ameen

Monday

ALLAH YAYIWA MAWALLAFIN LITTAFIN HISNIL'MUSLIM RASUWA

INNA LILLAHI WAINNA ILAIHI RAJIUN.

JAMA'AR MUSULMI MUNYI BANBAN RASHI.

Allah yayiwa Ash'sheik Sa'id bin Ali bin wahaf Alqhtani Rasuwa A yau litinin, Ash' sheik sa'id Shine wanda ya rubuta wannan shahararren littafi da duk wani musulmi ya sani. Wato HUSNIL'MUSLIM , Littafin da yake dauke da ingantattun addu'oi.



Za'a yiwa Gawar Ash'sheik Sa'id sallah yau litinin a masallacin arrajihy dake garin riyadh Babban birnin kasar saudiyya bayan sallar la'asar, .

Ash' Sheik Allah ya Kyauta makwanci , ya baka ladan wannan hidima ta rubuta wannan shahararren littafi a duniyar musulunci.

®Share®

Thursday

GUDUNMAWAR SHEIK ZAKIR NAIK GA MUSULUNCI DA KUMA KALUBALEN DA YAKE FUSKANTA.


  • TARIHIN RAYUWARSA A 
  • TAKAICECikakken sunansa shine Zakir Abdulkareem Naik.

An haife shi a ranar 18 Oct. 1965 a birnin India na Mumbai a Maharashtra.
Zakir ya hallaci makarantu da dama inda ya samu shaidar zama likitan tiyata wato
"Bachelorof Medicine and Surgery".


   zakir naik,zikr,naik,zikr naikSheik Dr. Zakir Naik


Zakir Naik na tare da mai dakinsa Farhat
Naik, dakuma 'yaya biyu Fariq Naik da Rushdaa Naik. .

Zakir Naik ya tsinci kansa cikin sahun masuDa'awah a shekarar 1991, lokacin da Muslunci ya tsinci kansa cikin tsangwama da muwiyacin hali a kasar India saboda gallazawar da masu addinin Hindu kewa Muslunci da Musulmi.

Zakir ya tasirantu ne da salon da'awar
sannanen malam nan wato Sheikh Ahmad Deedat wanda
Zakir ya hadu dashi a shekarar 1987, kamar yadda Naik na sheda a 2006, saboda tarin baiwa ta ilimi da Allah yayiwa Zakir yasa Deedat da kansa yake masa lakabi da "Deedat-Plus" wato kamar kace, "Malam da rabin Malam".

  • RUGUZA MASALLACIN BABRI
A shekarar 1992 wani muhimmin al'amari ya faru. A ranar 6, ga watan Disamba, na shekarar 1992, masu bin addinin Hindu kimanin 150,000 da taimakon jam'iyun siyasa na India; Bharatya Janata Party (BJP) da Vishva Hindu Parishad (VHP) suka afkawa gami da rugurguza Masjid
(masallacin) Babri mai dadden tarihi a cikin garin Ayodhya bayan haka suka ruguje masallatai masu yawa a yankin, masallacin Babri an gina shine tun qarni na 16 kimanin shekaru 500 da suka
wuce. Rushe masallacin ya jawo gagarumar riga wadda tayi sanadiyar asarar dukiyoyi masu tarin yawa da kuma mutuwar mutane fiye 2,000 wadanda yawancinsu Musulmi ne.

Hakika wannan rigima ta kara jefa Musulman India cikin halin ha'ula'i, zullumi da kaskanci, suka zamo basu da wata ta cewa, Muslunci ya zama abin zolaya gami da tsokana. Ana cikin wannan hali ne, Allah yayi nufin dawo
da martabar Muslunci da Musulmi ta hannun Sheikh Dr. Zakir Naik, kamar yadda Muhammad Reyaz ya sheda.


  • DEBATES DINSA
Dr. Zakir ya fara mahawararsa (debate) ta farko a 1994 kan wani littafi mai suna "Lajja" wanda wata mashahuriyar mai aibata muslunci Taslima Nasreen 'yar kasar Bangladesh ta wallafa. Haka a shekarar 2000, Zakir yayi mahawara
da sanannen masanin kimiyar nan Dr. William Campbell a birnin Chicago ta Amurika.

Campbell ya kwashe shekaru yana nazari kafin daga bisani ya wallafa wani littafi da yace Qur'an yaci karo da kimiyar zamani (modern science).
Muhawarar mai taken "The Qur'an and the Bible in the Light of Science" ta daukaka Naik saboda yadda yayi kaca-kaca da littafin da aka dau shekaru ana wallafa shi da hujja cikin kankanin lokaci,
hakan yasa Zakir ya zama abin tsoro tsakanin masu yiwa Muslunci zambo, kamar su Ali Sina wani dan asalin Iran mai tsananin adawa da Muslunci.
.
Zakir Naik wanda zaka iya kwatanta
kwakwalwarsa data "computer" saboda
kaifin rike abu, ya gudanar da lakcoci kusan 4000 a fadin duniya baki daya wanda ya hada da zuwansa Nigeria har sau biyu.


  • NASARORINSA
A bisa kokari irin nasa Zakir ya samar da:

i :- tashoshin satellite na Peace TV English, Peace TV Bangla, Peace TV Urdu da kuma Peace TV Chinese. Tashoshin wadanda babu kamar su wajen yada addini, kimanin mutane miliyan 150
ne suke iya kama Peace TV a kasashe fiye da 200.
Zakir Naik ya samar gami da jagorantar

ii :- "Islamic Research Foundation" (IRF) wato cibiyar bincike ta addinin Muslunci, a karkashin IRF aka samar da (IIS) wato "Islamic International School".

iii :- Sai kuma (UIA) "United Islamic Aid" wadda aikinta shine bada tallafin karatu ga nakasassuda masu rauni.

Irin wannan nasarori da Zakir Naik ya samu, gami da dawo da martabar Musulmai a India dama duniya baki daya, sune suka tsone idanun
munafukai musamman masu son gani bayan Muslunci, tako wace fuska.

Gazawar masu son ganin bayan Muslunci a sakamakon Zakir, yasa suke kokarin ganin bayansa, ta hanyar tsomashi cikin ayyukan ta'addanci, zargin da ako yaushe yake musawa.
Karku manta jam'iyar Bharatya Janata Party (BJP) wacce ta taka rawa wajen gallazawa Musulman India itace ke mulki yanzu. Kuma Prime Minister na yanzu Narendra Modi babban
yaron Lal Krishna Advani ne, wanda ya
jagoranci ruguza masallatan Ayodhya a 1992. Saboda haka babu mamaki cikin sabon salon rufe bakin Musulmai ta hanyar gamawa da Zakir Naik a farko.
.
  • MUSULMAI MASU ADAWA DASHI.
Yawancin masu adawa Zakir Musulmai 'yan Shi'a ne, suna zarginsa da rashin yin biyayya ga dokokin zamantakewa na India daga cikinsu akwai: Kalbe Jawad Naqvi da kuma Yasoob Abbas dss.

Amma yawancin qungiyoyin musulmai na mara masa baya kamar su: Sheikh Abdulkadir Jilani Foundation, Darul Uloom da kuma All-India Sunni Board.


  • BARAZANA GA RAYUWARSA
. A ranar 13 ga watan Juli 2016 shugabar
Vishva Hindu Parishad (VHP) wato Sadhvi ya bada sanarwar bada tukyici na dalar Amurika $78,000 ga duk wanda ya fillo kan Zakir Naik. Hakan yazo kwana daya bayan wata kungiyar Shi'a maiwa
kanta laqbi da Hussaini Tigers. ta sanya ladan $23,000 ga wanda ya kashe Zakir Naik.


  • DAUKAKARSA
Zakir ya sami zama mutum na 89 cikin
mutane 100 dake da karfin fada aji a India kasar dake da mutane fiye da biliyan daya da miliyan dari uku.
(1.3 bn) ya sake zama na 82 a shekarar 2010 kamar yadda The Indian Express ta sanar.