Thursday

Home GUDUNMAWAR SHEIK ZAKIR NAIK GA MUSULUNCI DA KUMA KALUBALEN DA YAKE FUSKANTA.

  • TARIHIN RAYUWARSA A 
  • TAKAICECikakken sunansa shine Zakir Abdulkareem Naik.

An haife shi a ranar 18 Oct. 1965 a birnin India na Mumbai a Maharashtra.
Zakir ya hallaci makarantu da dama inda ya samu shaidar zama likitan tiyata wato
"Bachelorof Medicine and Surgery".


   zakir naik,zikr,naik,zikr naikSheik Dr. Zakir Naik


Zakir Naik na tare da mai dakinsa Farhat
Naik, dakuma 'yaya biyu Fariq Naik da Rushdaa Naik. .

Zakir Naik ya tsinci kansa cikin sahun masuDa'awah a shekarar 1991, lokacin da Muslunci ya tsinci kansa cikin tsangwama da muwiyacin hali a kasar India saboda gallazawar da masu addinin Hindu kewa Muslunci da Musulmi.

Zakir ya tasirantu ne da salon da'awar
sannanen malam nan wato Sheikh Ahmad Deedat wanda
Zakir ya hadu dashi a shekarar 1987, kamar yadda Naik na sheda a 2006, saboda tarin baiwa ta ilimi da Allah yayiwa Zakir yasa Deedat da kansa yake masa lakabi da "Deedat-Plus" wato kamar kace, "Malam da rabin Malam".

  • RUGUZA MASALLACIN BABRI
A shekarar 1992 wani muhimmin al'amari ya faru. A ranar 6, ga watan Disamba, na shekarar 1992, masu bin addinin Hindu kimanin 150,000 da taimakon jam'iyun siyasa na India; Bharatya Janata Party (BJP) da Vishva Hindu Parishad (VHP) suka afkawa gami da rugurguza Masjid
(masallacin) Babri mai dadden tarihi a cikin garin Ayodhya bayan haka suka ruguje masallatai masu yawa a yankin, masallacin Babri an gina shine tun qarni na 16 kimanin shekaru 500 da suka
wuce. Rushe masallacin ya jawo gagarumar riga wadda tayi sanadiyar asarar dukiyoyi masu tarin yawa da kuma mutuwar mutane fiye 2,000 wadanda yawancinsu Musulmi ne.

Hakika wannan rigima ta kara jefa Musulman India cikin halin ha'ula'i, zullumi da kaskanci, suka zamo basu da wata ta cewa, Muslunci ya zama abin zolaya gami da tsokana. Ana cikin wannan hali ne, Allah yayi nufin dawo
da martabar Muslunci da Musulmi ta hannun Sheikh Dr. Zakir Naik, kamar yadda Muhammad Reyaz ya sheda.


  • DEBATES DINSA
Dr. Zakir ya fara mahawararsa (debate) ta farko a 1994 kan wani littafi mai suna "Lajja" wanda wata mashahuriyar mai aibata muslunci Taslima Nasreen 'yar kasar Bangladesh ta wallafa. Haka a shekarar 2000, Zakir yayi mahawara
da sanannen masanin kimiyar nan Dr. William Campbell a birnin Chicago ta Amurika.

Campbell ya kwashe shekaru yana nazari kafin daga bisani ya wallafa wani littafi da yace Qur'an yaci karo da kimiyar zamani (modern science).
Muhawarar mai taken "The Qur'an and the Bible in the Light of Science" ta daukaka Naik saboda yadda yayi kaca-kaca da littafin da aka dau shekaru ana wallafa shi da hujja cikin kankanin lokaci,
hakan yasa Zakir ya zama abin tsoro tsakanin masu yiwa Muslunci zambo, kamar su Ali Sina wani dan asalin Iran mai tsananin adawa da Muslunci.
.
Zakir Naik wanda zaka iya kwatanta
kwakwalwarsa data "computer" saboda
kaifin rike abu, ya gudanar da lakcoci kusan 4000 a fadin duniya baki daya wanda ya hada da zuwansa Nigeria har sau biyu.


  • NASARORINSA
A bisa kokari irin nasa Zakir ya samar da:

i :- tashoshin satellite na Peace TV English, Peace TV Bangla, Peace TV Urdu da kuma Peace TV Chinese. Tashoshin wadanda babu kamar su wajen yada addini, kimanin mutane miliyan 150
ne suke iya kama Peace TV a kasashe fiye da 200.
Zakir Naik ya samar gami da jagorantar

ii :- "Islamic Research Foundation" (IRF) wato cibiyar bincike ta addinin Muslunci, a karkashin IRF aka samar da (IIS) wato "Islamic International School".

iii :- Sai kuma (UIA) "United Islamic Aid" wadda aikinta shine bada tallafin karatu ga nakasassuda masu rauni.

Irin wannan nasarori da Zakir Naik ya samu, gami da dawo da martabar Musulmai a India dama duniya baki daya, sune suka tsone idanun
munafukai musamman masu son gani bayan Muslunci, tako wace fuska.

Gazawar masu son ganin bayan Muslunci a sakamakon Zakir, yasa suke kokarin ganin bayansa, ta hanyar tsomashi cikin ayyukan ta'addanci, zargin da ako yaushe yake musawa.
Karku manta jam'iyar Bharatya Janata Party (BJP) wacce ta taka rawa wajen gallazawa Musulman India itace ke mulki yanzu. Kuma Prime Minister na yanzu Narendra Modi babban
yaron Lal Krishna Advani ne, wanda ya
jagoranci ruguza masallatan Ayodhya a 1992. Saboda haka babu mamaki cikin sabon salon rufe bakin Musulmai ta hanyar gamawa da Zakir Naik a farko.
.
  • MUSULMAI MASU ADAWA DASHI.
Yawancin masu adawa Zakir Musulmai 'yan Shi'a ne, suna zarginsa da rashin yin biyayya ga dokokin zamantakewa na India daga cikinsu akwai: Kalbe Jawad Naqvi da kuma Yasoob Abbas dss.

Amma yawancin qungiyoyin musulmai na mara masa baya kamar su: Sheikh Abdulkadir Jilani Foundation, Darul Uloom da kuma All-India Sunni Board.


  • BARAZANA GA RAYUWARSA
. A ranar 13 ga watan Juli 2016 shugabar
Vishva Hindu Parishad (VHP) wato Sadhvi ya bada sanarwar bada tukyici na dalar Amurika $78,000 ga duk wanda ya fillo kan Zakir Naik. Hakan yazo kwana daya bayan wata kungiyar Shi'a maiwa
kanta laqbi da Hussaini Tigers. ta sanya ladan $23,000 ga wanda ya kashe Zakir Naik.


  • DAUKAKARSA
Zakir ya sami zama mutum na 89 cikin
mutane 100 dake da karfin fada aji a India kasar dake da mutane fiye da biliyan daya da miliyan dari uku.
(1.3 bn) ya sake zama na 82 a shekarar 2010 kamar yadda The Indian Express ta sanar.

No comments:
Write Comments