Saturday

Home › › Ko Donald Trump zai goyi bayan kafa kasar Biafra? : NIGERIA
Tun dai bayan zaben shugaba Muhammadu Buhari a bara, dangantakar Najeriya da Amurka ta dan inganta.

Dangantakar dai ta yi tsami ne bayan zargin cin zarafin bila'dama da ake yiwa sojojin Najeriyar, musamman ma a yakin da suke yi da mayakan Boko Haram.

Sojojin Najeriyar suna samun horo da kuma kayan aiki daga gwamnatin Barack Obama, don haka za su so Mista Trump ya ci gaba da karfafa wannan dangantakar.

Najeriya za ta kuma so ta samu kyautatuwar dangantakar kasuwanci da Amurkar.

Wasu daga cikin manyan kamfanonin Amurka na cikin gaggan masu zuba jari a bangaren makamashi a Najeriya, amma kuma gano danyan man da Amurkar ta yi ya sa yawan man da ta ke saya daga kasar ya ragu.

  • Me ya sa shugabannin Afirka ke tsoron mulkin Trump?


  • 'Katobarar da Donald Trump ya yi'


  • Su waye na hannun-daman Trump
    'Yan aware na Biafra


  • Me yiwuwa kasashen biyu su samu kan su cikin yanayin nan da Hausawa ke kira ta ciki-na-ciki, ko kuma akai ruwa-rana, muddin Mista Trump ya yanke shawarar amincewa da 'yan awaren Biafra.

    Masu fafitikar ballewa daga Najeriyar sun nuna goyon bayansu ga dan takarar jam'iyyar Republican din a lokacin yakin neman zabe, suna masu fatan cewa zai goyi bayan fafitikar da suke yi ta samun wannan 'yancin.

    Sun ce ya goyi bayan ''Brexit''- matakin Birtaniya na ficewa daga kungiyar Tarayyar Turai - don haka suke ganin zai goyi bayan "Biafrexit", koda yake bai nuna alamun zai yi hakan ba a bainar jama'a.

    An samu hargitsi tsakanin masu fafitikar kafa kasar Biafra da jami'an tsaro a lokacin da suke zanga-zangar nuna goyon baya a ranar da aka rantsar da Shugaba Trump.
    Wasu rahotanni sun ce an samu asarar rayuka amma jami'an 'yan sanda sun ce babu wanda ya mutu.

    Akwai 'yan Najeriya fiye da miliyan daya da ke zaune a Amurka, kuma wasu na fargabar cewa manufofin Mista Trump kan harkokin shige-da-fice ka iya kai wa ga korar dubban su zuwa gida.
    No comments:
    Write Comments