Friday

Home › › Yahya Jammeh ya amince ya sauka daga kan karagar mulki, sannan kuma ya fice daga kasar : GAMBIA
Zababben shugaban kasar Gambia ya ce Yahya Jammeh ya amince ya sauka daga kan karagar mulki, sannan kuma ya fice daga kasar.

Adama Barrow ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter bayan shafe sa'o'i ana tattaunawa domin shawo kan Mista Jammeh ya amince da sakamakon zaben.

Kasashen Yammacin Afirka sun turo dakaru zuwa Gambia domin barazanar kawar da shi da karfin tuwo.

Mista Barrow ya shafe kwanaki a kasar Senegal mai makwaftaka da Gambia.
Kuma a ofishin jakadancin kasar da ke birnin Dakar aka rantsar da shi a ranar Alhamis.

Kasashen duniya sun amince da shi a matsayin shugaban kasar bayan nasarar da ya samu a zaben watan da ya gabata.


  • Ta yaya Jammeh zai bar fadar gwamnatin Gambia?


  • Wane ne sabon shugaban Gambia



  • Tun da farko Shugaban kasar Guinea Alpha Conde da na Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz sun isa Banjul don ganawa da Yahya Jammeh.

    Shugaban hukumar ECOWAS, Marcel Alain de Souza ya ce idan tattaunawar ta gaza samun nasara, sojoji za su ɗauki mataki.

    Jawabin kama-aiki
    A jawabinsa na farko don kama mulki Shugaba Adama Barrow ya ce: "Daga ranar (Alhamis) DA ta gabata, Ni ne shugaban kasar Gambia ko ka/kin zaɓe ni ko ba ka/ki zaɓe ni ba."
    Ya ce "Wannan nasara ce ga kasar Gambia.. mulki a hannun jama'a yake a Gambia"
    A cewarsa "Wannan rana ce wadda babu wani ɗan Gambia da zai taɓa mantawa da ita... karon farko tun bayan samun 'yancin kai, Gambia ta sauya gwamnati ta hanyar kuri'a".
    Shugaban kasa biyu
    A ranar Laraba ne wa'adin Yahya Jammeh a kan mulki ya kare, ko da yake majalisar dokokin kasar ta tsawaita zamansa a kan mulki da kwana 90.
    'Yan Gambia da ma 'yan kasashen waje da ke zuwa yawon bude ido a kasar da yawa ne suka fice zuwa wasu kasashe makwabta saboda tsoron ɓarkewar rikici.

    Barrow ya kayar da Mista Jammeh a zaben da aka yi cikin watan Disamba.
    Da farko dai Jammeh ya amince da shan kaye sannan ya taya Mista Barrow murna, amma daga bisani sai ya ce ba zai sauka daga mulki ba saboda zargin da ya yi cewa an tafka kura-kurai a zaben.

    Ya kuma garzaya kotu inda yake kalubalantar sakamakon zaben.
    No comments:
    Write Comments