Tsohon shugaban kamfanin mai na kasa Andrew Yakubu ya ce dalolin da aka kama boye a gidan kaninsa da ke unguwan Sabon Tasha Kaduna bashi Kyauta ne akayi - Hukumar EFCC ta kama Andrew Yakubu domin gudanar da bincike akansa ko akwai wasu kudaden da ya boye. jami’an hukumar EFCC sun kama daloli da ya kai naira biliyan uku boye a gidan kanin Andrew Yakubu da ke unguwan Sabon Tasha a Kaduna. EFCC ta ce Andrew Yakubu na ba jami’anta hadin kai yadda ya kamata.
A wani labarin kuma
, Majalissar dattijan Najeriya za ta saurare ra’ayi jama’a yau litinni kan kasafin kudin shekarar 2017, na naira Triliyan sama da 7 da shugaba Buhari ya gabatar gabanta.Batun da ake bayanawa a matsayin irinsa na farko da majalisar ke shirin gudanarwa, a cewar kakkakin Majalisar, Aliyu Abdullahi, an dau wannan mataki ne domin bai wa masu ruwa da tsaki da sauran al’umma daman tofa albarkacin bakinsu kan kasafin kudin. Jin bahasin kan kasafin kudin shekarar 2017, shine zai bai wa Majalisar daman amincewa da ita’’, a cewar Aliyu Abdullahi. Tun a shekarar da ta gabata shugaba Buhari ya gabatarwa Majalisa Kasafin da ya haura kasafin 2016.
©facebook/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments