
Ana taron addu'oi ga shugaba Muhammad Buhari a jihar Osun wanda al'ummar muslmin jihar suka shirya -Taron ya samu halartar manyan mutane daga ciki da kuma wajen jihar ciki har da Sarkin Musulmi da gwamna da kuma sauran manyan baki a yayin taron

Mai alfarma Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar da gwamnan jihar Osun na cikin manyan mutanen da suka halarci wani taron addu'oi ga Shugaba Buhari a jihar Osun Taron wanda aka yi a ranar Lahadi 12 ga watan Fabarairu, Kungiyar al'ummar musulmin jihar Osun ce ta shirya, ya kuma samu halartar jama'a daga cikin da kuma wajen jihar.

Jaridar The Punch ta rawaito cewa, cikin wadanda suka halaraci taron sun hada da Mai alfarma sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli mai kula da al'amuran addinin musulunci Sa'ad Abubakar, da gwamnan jihar Rauf Aregebsola. Sauran su ne Sarkin Ilori Alhaji Sulu Gambari, da tsohon babban sifeton 'yan sanda Alhaji Musliu Smith, da kuma sauran wasu shugabannin al'ummar musulmi na kasar.
A jawabinsa lokacin gabatar da addu'oin, mai alfarama sarkin musulmi ya jinjinawa gwamna jihar Rauf Aregbesola a kokarinsa na wanzar da zaman lafiya, da kuma hakurin zama da juna a tsakanin mabiya addinai daban- daban a jihar. A bayaninsa kan makasudin shirya taron, Mista Oyodele shugaban hukuma shirya jarrabawar shiga jami'oin ta Najeria JAMB ya ce, wannan shi ya kamaci duk wani mai hankali a kasar nan sannan ya kuma ce, Muna masu yin wadannan addu'oi ne domin neman Allah Ya ba shugaba Muhammadu Buhari lafiya, Ya dawo mana da shi gida lafiya, Allah Ya kuma ba kasar mu zama lafiya".
Al'ummar Najeriya dai sun tashi tsaye da yin addu'ar samun lafiyar shugaban kasar a dai-dai kun su da kuma a taro. A jihar Borno kadai a makon jiya, malamai ku san 350 ne su ka gabatar da addu'ar samun lafiya ga shugaban wanda ke Ingila inda likitoci ke duba lafiyarsa.
©facebook/HAUSAPOST28
No comments:
Write Comments