Wani matashi dan shekara 15 kuma
mazaunin Karamar Hukumar Kura da ke
jihar Kano mai suna Danliti Ciliti yace yana
gab da kammala kera wata na’auran tara
wutan lantarki mai amfani da hasken wata
Ba kamar yadda kowa ya sani cewa
na’urori masu amfani da hasken rana ce
kawai ake gani kuma ake mu’amula da su,
Danliti yace shi nasa na’uran da yake
kirkirowa da hasken wata ce za ta yi
amfani.
“Banga sana’ar da zata gagareni ba da
yardar Allah. Allah shiyasan yawan
sana’oin da na iya.”
Danliti yace ya kirkiro abubuwa da
dama kamar su rediyon kwali, ya iya
gyarankwan fitillan da ta mutu, ya iya
zana gida kowanne iri da ginawa, shi
kafinta ne kuma yana gyaran karaya ko
targade.
“Ina gyaran Keke Napep wato adaidaita
sahu, ni kafinta ne, ni makaniken mota
ne sannan ina gyaran keken dinki.''
Danlami yace wannan baiwa ce Allah
ya bashi a garin kura kuma kowa ya
sanshi da sana’o’insa.
Yace a yanzu yana ci gaba da nazarin
kera na’urar tara wutan lantarki
amfani da hasken farin wata wacce sam
baza tayi aiki da hasken rana ba da
izinin Allah.
Yanzu hakan Danliti ya gano yadda za’a
gyara memori na waya.
Kamar yadda ya fadi, Danliti yace ya
gano hakanne saboda hasarar da
mutane sukeyi idan memori din
wayarsu ta lalace. Yanzu yana gyara
memori kuma ta dawo aiki kamar
yadda take ada.
No comments:
Write Comments