Sunday

Home Jamusawa sun kubuta daga masu garkuwa a Najeriya.






Gwamna Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna ya bayyana haka a ranar Lahadin nan cikin wani jawabi da ya fito daga gwamnan inda a cikinsa ya ke yaba wa jami'an tsaro.


Jami'an tsaro a Najeriya sun yi nasara ta kubutar da wasu masanan kimiyar gano halittu da suka dade da mutuwa a cikin kasa wato (archaeologists) a Turance, wadannan kwararru dai sun kasance Jamusawa guda biyu da aka yi garkuwa da su a Arewacin Najeriya.

Gwamna Nasir El-Rufa'i na Jihar Kaduna ya bayyana haka a ranar Lahadin nan cikin wani jawabi da ya fito daga gwamnan inda a cikinsa yake yaba wa jami'an tsaro kan yadda suka yi nasara wajen kubutar da wadannan Jamusawa. Sai dai babu karin bayani ko an kama wadanda suka yi garkuwar da su.

Tun farko dai 'yan bindiga sun nemi a biyasu kudin fansa na Naira miliyan 60 kimanin (Dala $200,000) kafin su saki Farfesa Peter da mai taimaka masa Johannes. An kama su bayan tisa keyarsu da bindiga a ranar Laraba a lokacin da suke aiki a kauyen Jenjela da ke Jihar Kaduna. Masu garkuwar dai sun kashe wasu mutane biyu 'yan garin bayan da suka yi kokari na kubutar da Jamusawan.
No comments:
Write Comments