Masallaci a ciki, Coci a waje a birnin Durban ta
Afrika ta kudu.
Wani ginin coci matsohon tarihi a Afirka
ta Kudu ya zama masallaci kuma kuros din
da aka yi ado da ita a hasumayar gaban
cocin har yanzu tana nan.
Ginin an yi shi ne tun shekarar 1903,
shekaru 114 wanda daga bisani aka sayar
wa da wani dan kasuwa a shekarun 1990s.
An kirawo wasu masu zane-zane da ado
irin na musulunci daga kasar Maroko su
mayar da cikin cocin zama masallaci.
Masallaci a ciki, Coci a waje a birnin Durban ta
Afrika ta kudu
Musulmai a Durban ta Afirka ta Kudu
su ka karbi wani tsohon coci sun kuma
mayar da ita masallacin Juma'a.
An mayar da wani Coci mai tsohon
tarihi a Africa ta Kudu masallaci, sai
dai hukuma ta hana sauyawa wajen
ginin kamanninsa na asali zuwa
masallaci.
Haka kuma masallacin mai kama da
majami'a har yanzu ya na tare kuros a
can saman hasumayar sa wacce aka
gina kimanin shekaru 114 da suka
wuce.
Tsohuwar majami'ar da aka kira da
Aliwal Congregational Church, an fara
gina ta ne a 1903 inda daga bisani aka
sayar wa da wani dankasuwa a
shekarun 1990s.
Duk da cewa a yanzu an mayar da cocin
masallaci, ginin zai ci gaba da karbar
baki wadanda ba musulmai ba da su ke
sha'awar ganin yadda ake yin sallah.
Ba kuma zai zama wajen sallah ba
kawai, a sabon masallacin ma'aikata na
kokarin samar da wajen bajen bajekolin
hotuna da lakcoci da za a rika
gabatarwa lokaci-lokaci a cikin ginin.
Musulman Durban sun dauko masu
taswira kwaliyar gine-gine daga Maroko
domin su mayar da ginin yanayin ginin
musulmai daga ciki.
Yanzu dai masu taswirar sun shafe
kimanin wata biyu su na kawata
masallacin da alamomin musulunci.
Masallacin ya ci gaba da zama da kuros
saboda duk abin da ke wajen Cocin na
karkashin kariyar doka.
A karshe ya zama gurin bauta da ya
hada manyan addinan guda biyu.
Kirisatanci da kuma muslunci.
Don ganin wasu misalan majami'u da su
ka rikide zuwa masallatai, kalli hoton
bidiyon da ke kasa.
Afrika ta kudu.
Wani ginin coci matsohon tarihi a Afirka
ta Kudu ya zama masallaci kuma kuros din
da aka yi ado da ita a hasumayar gaban
cocin har yanzu tana nan.
Ginin an yi shi ne tun shekarar 1903,
shekaru 114 wanda daga bisani aka sayar
wa da wani dan kasuwa a shekarun 1990s.
An kirawo wasu masu zane-zane da ado
irin na musulunci daga kasar Maroko su
mayar da cikin cocin zama masallaci.
Masallaci a ciki, Coci a waje a birnin Durban ta
Afrika ta kudu
Musulmai a Durban ta Afirka ta Kudu
su ka karbi wani tsohon coci sun kuma
mayar da ita masallacin Juma'a.
An mayar da wani Coci mai tsohon
tarihi a Africa ta Kudu masallaci, sai
dai hukuma ta hana sauyawa wajen
ginin kamanninsa na asali zuwa
masallaci.
Haka kuma masallacin mai kama da
majami'a har yanzu ya na tare kuros a
can saman hasumayar sa wacce aka
gina kimanin shekaru 114 da suka
wuce.
Tsohuwar majami'ar da aka kira da
Aliwal Congregational Church, an fara
gina ta ne a 1903 inda daga bisani aka
sayar wa da wani dankasuwa a
shekarun 1990s.
Duk da cewa a yanzu an mayar da cocin
masallaci, ginin zai ci gaba da karbar
baki wadanda ba musulmai ba da su ke
sha'awar ganin yadda ake yin sallah.
Ba kuma zai zama wajen sallah ba
kawai, a sabon masallacin ma'aikata na
kokarin samar da wajen bajen bajekolin
hotuna da lakcoci da za a rika
gabatarwa lokaci-lokaci a cikin ginin.
Musulman Durban sun dauko masu
taswira kwaliyar gine-gine daga Maroko
domin su mayar da ginin yanayin ginin
musulmai daga ciki.
Yanzu dai masu taswirar sun shafe
kimanin wata biyu su na kawata
masallacin da alamomin musulunci.
Masallacin ya ci gaba da zama da kuros
saboda duk abin da ke wajen Cocin na
karkashin kariyar doka.
A karshe ya zama gurin bauta da ya
hada manyan addinan guda biyu.
Kirisatanci da kuma muslunci.
Don ganin wasu misalan majami'u da su
ka rikide zuwa masallatai, kalli hoton
bidiyon da ke kasa.
No comments:
Write Comments